Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet (3)

A wannan karo ma mun ci gaba da bayani ne kan ka’idojin mu’amala a Intanet. A sha karatu lafiya.

235

Makon Jiya

Idan mai karatu na biye da mu makonni biyu da suka gabata, ya samu bayanai kan asali da wasu daga cikin dunkulallun ka’idojin mu’amala da za su taimaka masa wajen gabatar da dukkan abin da yake son yi a Intanet.  Hakan muka ce yana da matukar muhimmanci wajen samun ingantacciyar yanayin da mai lilo da tsallake-tsallake ke bukata.  A makon da ya wuce mun kawo ka’idoji guda goma dunkulallu.  A yau cikin yardan Ubangiji za mu kawo sauran ka’idoji sha daya da suka rage.  Har wa yau, mun sanar da cewa wadannan ka’idoji dukulallu ba su kenan ba, kowa na iya kirkira, daidai fahimta da mahangar da yake dashi kan wannan fasaha.  A yanzu za mu ci gaba:

Durkusa ma Wada, Ba Gajiyawa Bane

 Sosai kuwa!  Wannan ka’ida tana da muhimmanci wajen mu’amala da mutane a Majalisun Tattaunawa, wato Mailing Lists ko Discussion Group.  Domin waje ne da kowa ke iya kawo fahimtarsa kan abin da ake tattaunawa ko ya faru.  Kuma yadda dabi’ar dan Adam take, zai yi wahala a ce ga wani ra’ayi da dole ne kowa da kowa ya yarda dashi, sai in doka ce.  Don haka za ka ji ana ta tafka muhawara, wanda hakan ke taimakawa wajen fitar da wasu nau’uka na ilimi da wani bai sani ba.  Wannan tasa a galibin Majalisun Tattaunawa, musamman na Hausawa da ke Intanet, ba a cika hana muhawara ba, sai in akwai cin fuska da zage-zage a ciki.  Banbance-banbancen ra’ayoyi ne ke kawo haka,  kuma haka Allah Ya halicci mutane.  Wannan tasa dole wasu lokuta ka saurara ma wasu ra’ayoyin ko da kuwa kana ganin ra’ayinka (in ma ka bayyana kenan) bai samu karbuwa ba.  Domin yin hakan, baya nufin kana kan ra’ayin da yayi rinjaye kenan.  A wasu lokuta ma shawarwari ne za a kawo, ana son wanda ya fi dacewa, sai kake ganin naka ne yafi, amma kuma aka dauki wanda kake ganin bai kai naka muhimmanci ba, sai ka hakura.  Don me?  Durkusa ma wada, har abada, ba gajiyawa bane.

 In Ka Ki Ji, Ba Ka Ki Gani Ba

 Wannan haka yake, kuma misalai kan haka na nan ko ina a Intanet, galibi a gidajen yanar sadarwa na wasu al’ummomi da al’adu ko akidu ko kuma tsarin rayuwarsu ta sha banban da naka.  Gidajen yanar sadarwa masu tallata hajojin da suka sha banban da yanayin tunani da tsarin al’umma hatta wadanda suke ciki, za ka samu suna gargadin duk wanda ya shigo, ”a wannan gidan yanar sadarwa, kaza da kaza muke tallatawa, idan yayi maka, ka shigo, in kuwa ba ka bukata, ga hanyar ficewa nan”.  Ka ga a nan, sun fita hakkinka.  Wannan yafi shahara a gidajen yanar sadarwa na masu akidun “Ba Allah” (wato Atheists), da na masu tallata hajojin batsa da shashanci.  Har wa yau, wasu lokuta kwamfutar ka za ta sanar da kai cewa a wannan gidan yanar da ka shiga, akwai wasu abubuwa da za su iya bata maka kwamfutar;  ka amince in shigar da kai, ko ko za ka fice?  Za ta baka zabi; duk wanda ka dauka, shi za ta zartar maka.  Sauran bayanai kuma, kai ka jiyo, sautun mahaukaciya. Dole su sa wannan sanarwa a dokokin kasashen su, don ba kowa bane ke da mahanga da tunani irin nasu.  A nan an sanar da kai cewa ga abin da za ka gani idan har ka shiga; kenan in baka so, sai kawai ka fice.  Amma idan ka ki ji, to fa ka sani, ba ka ki gani ba.

 Gaskiya Kujera Ce…

 Wannan a fili yake.  Idan gidan yanar sadarwa kake dashi, kayi mu’amala da mutane da gaskiya, musamman a wannan duniyar da karya da zamba ne ke da tasiri, jama za su kaunace ka, su ci gaba da mu’amala da kai.  Amma da zarar sun nemi gaskiyarka sun rasa, sai ka ga wayam, sunan wani mawaki.  Haka ko Majalisun Tattaunawa, idan ka fadi gaskiya aka ki sauraranka, share.  Muddin ana raye, in dai gaskiyar ake nema, to sai an dawo mata.  Don me?  Kujera ce, duk inda aka je aka dawo, za a same ta.  Ba ta bin kowa, sai dai a bi ta.

Zama Lafiya, Ya Fi Zama Dan Sarki

 Wa ke Magana kuwa!  Ai ka zauna lafiya shi yafi a tara maka dukkan arzikin da ke duniyan nan, ba ma kudin da ke ciki kadai ba.  Idan kana Majalisar Tattunawa, ka lazimci bakinka, muddin abin da za ka fada bai da muhimmanci.  Amma in har yana da muhimmanci, ko da wasu basu so, ka iya fada.  Illa dai hakan ya danganta da yanayin da ka fadi maganar ne.  Amma idan mutum zai ta aiko da dukkan abin da kawai yaji zuciyar sa ta raya masa ne, to fa zai ga ko ji abin da baya son gani ko ji.  Son zuciya, in ji Malam Bahaushe, bacin zuciya.  Wannan tasa wasu ke yin shiru a Majalisun Tattaunawa, kai kace basu nan.  A a, kawai abin fadi ne bai zo ba.  Ko kuma munasabar Magana ne bai zo musu ba.  Sai kawai su lake a bakin garka suna karanta sakonnin da ake aikowa.  Wannan shi ake kira Lurking, a turancin Intanet.  Don me?  Zama lafiya, yafi zama dan Sarki.

Idan An Ciza, A Rika Hurawa

 Sosai kuwa, sai al’amura su tafi daidai.  Wannan ka’ida na da muhimmanci wajen tarbiyya a Majlisun Tattaunawa.  Galibin lokuta, yin sassauci shi ke sa a dade ana amfana da juna, ko kuma amfanuwa da wata hanya ta ci gaba.  Idan jayayya tai yawa ko ta tsawaita, galibi takan haddasa gaba a tsakanin masu yi.  Haka idan tsanantawa tai yawa wajen lura da dokoki, sai a samu kosawa wajen mabiya.  Wannan tasa a wasu Majalisun Tattaunawa za ka samu ana rangwame wajen shigar da gaishe-gaishe da aiko da sakonnin neman aiki, da na zanen suna da daurin aure, wadanda watakil sun sha banban da manufar Majalisar.  Ana haka ne, don jawo mutane a jika.  Idan an ciza, to fa a rika hurawa.

 Taka-tsantsan, Ya Fi Bundun-bundun

- Adv -

 Ai ko a rayuwar yau da kullum haka abin yake.  Ko da kana da manufa wajen abin da kake son yi, kuma ka samu abin da kake so, to fa taka tsantsan na da muhimmanci, don daukan abin da kake son daukawa.  Kada ka dauki abin da ba shi kake bukata ba, saboda gaugawa.  Intanet wata duniya ce mai kama da kantin alawa;  idan ka zama yaro wajen daukan irin alawar da kake so don ruwan ido, sai ka rude, ka dauki mara zaki, don yawan kyale-kyalen bawonta.  Taka-tsantsan, ya fi bundun-bundun.

 Kowa da Abokin Burminsa

 A Intanet kowa da abokin burminsa; Jamila na tare ne da Jamilu; Danjuma na tare ne da Danjummai; Salihu na tare da Salaha; Doma na tare da Awai.  Don me?  Abokin biri, idan ka bi duddugi, za ka samu kare ne.  Wannan na nufin kowa ya san inda zai samu mutanensa; wadanda dabi’arsa ko tunaninsa suka yi daidai.  Wannan shi ne galibin abin da yafi shahara a Intanet, musamman ga wadanda suka saba shiga yau da kullum.  Hatta a Majalisun Tattaunawa, inda ake da jama’a daya, Hausawa kuma Musulmai, a misali, za ka samu a tsakaninsu ma kowa da abokinsa, ko abokiyarsa.  Wani baya karanta sakon kowa sai na wane.  Wani baya goyon bayan rubutun kowa sai na wane ko wance.  Wani kuma baya Magana, sai an taba wane ko wance.  Kowa dai da mutanensa.  Idan ka fahimci wannan, to ba abin da zai bata maka rai. Don daman a rayuwa Allah bai yi mutane su zama daya ba; kowa da abin da yake so ko sha’awa.  Sai hali yai daidai ake abota.

 Gyara Kayanka, Ba Ya Zama Sauke Mu Raba

 Idan aka maka gyara kan abin da ka fada a Majlisun Tattaunawa misali, ka karba, kada ka bi son zuciyarka wajen ki, ko kuma ka daga hanci.  Ko wani ne ya cutar da kai, aka taru wajen baka hakuri, to ka hakura.  Kada ka dauka an yi haka ne don raunata muhimmancin ka ko na tunani ko ra’ayinka.  A a, gyara kayanka ne, wanda kuma ba ya taba zama sauke mu raba.

 In Baka Gayyaci Kowa Ba, Baka Ganin Kowa

 Wannan yafi shahara a Wasikar Hanyar Sadarwa, wato Imel.  Idan ka bude akwatin wasikar Imel, dole ka sanar da abokanai da ‘yan uwa da kake son ku rika karban wasiku a tsakaninku.  Idan ba haka ba, ba za ka samu wasikar kowa a jakar Imel dinka ba, sam.  In kuwa ka samu, to dayan biyu; ko dai wanda masu manhajar Imel din da ka bude ne suka aiko maka don yi maka “barka da shigowa”, ko kuma sakonnin bogi ne, wato Spam.  Haka idan gidan yanar sadarwa kake dashi, kana bukatar ka rika tallata gidan, ta hanyar sanar da abokan hulda, ko ka aika ma gidajen yanar sadarwa masu manhajar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine), irinsu Google, Yahoo, Altavista, Websearch da sauransuSu za su sa “dan aikensu” wato Robot, ya shiga gidan yanar don taskance irin kalmomin da ke ciki, yana zubawa a Uwayen Garken su.  Da zarar masu neman bayanai sun yi amfani da kalmomi masu munasaba da wannan, sai su samo ki.  In kuwa ba haka ba, to ba ka ganin kowa.

 Mai Hakuri Yakan Dafa Dutse

 Idan kana da hakuri wajen neman abin da kake nema, ko ba dade ko ba jima, za ka samu abin da kake so.  Abin da ake bukata shi ne ka rike ka’idojinka a matsayin fitila.  Wannan zai kai ka ga nasara.  Idan ilimi kake nema, duk wahalarsa, muddin ka lazimci ka’idojin da ke da munasaba da wannan ilimi, ba abin da zai hana ka samun sa.  Duk abin da kake koyo, za ka iya kwarewa a kai.  Duk abin da kake nema, indai yana nan, ka ci gaba da nema.  Za ka samu wataran.  Idan littafi kake son rubutawa, duk za ka samu bayanai.  Idan wani fasaha kake son koyo, duk za ka samu mabudai da hanyoyin cin nasara.  Abin da kake bukata shi ne ka san abin da kake nema, da ka’idojin da ke tattare da shi, kada ka damu da tsawon lokacin da zai dauke ka.  Domin idan za ka yi mu’amala da duk abin da ya shafi kwamfuta da Intanet, to fa kana bukatar hakuri da jajircewa.  Su ne manyan fitilu masu haskaka maka hanya.  Da su, sai ka dafa dutsenka, har ka shanye romonsa.

 Kowace Ka’ida Da Kaidinta

 Wannan ita ce ka’ida ta karshe, kuma ita ke nuna mana cewa duk wata ka’ida da dan Adam ya kawo maka ko ya sanya ma kansa, to fa tana da kaidinta.  Wannan kaidi shi ke tsawaita amfaninta, da kuma nuna cewa idan al’amura suka cakude, kana ganin cewa amfanin ka’idar da kake kai ya zo karshe, sai a ce maka ga mafita karkashin wannan ka’ida.  Dukkan ka’idojin da muka kawo a sama suna da kaidin da ke kayyadesu da wani yanayi ko lokaci ko muhalli.  Idan ba haka ba, sai hikimar da ke tattare da ka’idar ta bace.  Da aka ce kada mu ci mushe a musulunci, sai aka kayyade wannan hani da lokacin tsanani ko rashin abinci.  Domin tsare ran dan Adam da lafiyar sa, shi yafi.  Don sai kana da rai sannan za a yi tunanin dora maka wata doka.  Haka sauran ka’idoji suke.  Misali, muka ce Ko da me kazo an fi ka;  sai kuma muka kayyade wannan ka’ida da cewa kogi ba ya kin dadi.  Don kada ka dauka, tunda an ce duk abin da kaje dashi na ilii da fasaha, ai wani ya riga ni, don haka na fasa.  A a, kogi ba ya kin dadi.  Da dai sauran kaidin da aka sa ma sauran ka’idoji da mai karatu zai ci karo dasu.

Kammalawa

 A nan za mu dakata sai wani mako.  Ina fatan masu karatu sun samu hanya guda wajen kiyasta manufa ko dalilan da za su taimaka musu wajen mu’amala da wannan fasaha.  Duk abin da ba a fahimta ba a rubuto.  Zuwa mako mai zuwa kuma za mu juya akala zuwa wani bangaren don dada fahimtar wannan fasaha mai tasiri.  Ina kuma mika sakon gaisuwa ta musamman da shigowar mu wannan wata mai alfarma na Ramadana, Allah Ya karbi dukkan ayyukan mu gaba daya, amin.  Sai mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.