Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (3)

Ma'adanar Wayar Salula

Ma’adanar ROM na iya ɗaukan zallar bayani a sigar rubutu.  Tana iya ɗaukan bayanan sauti (Audio).  Tana iya ɗaukan hotuna (Images/Pictures).  Tana iya ɗaukan hotuna masu motsi, wato bidiyo kenan.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 18 ga watan Agusta, 2023.

102

A ɗaya ɓangaren kuma, sikirin nau’in LED suna amfani da hasken dake bayyana daga jikinsu ne kai tsaye, ba daga baya ba, kamar na LCD.  Sikirin ɗin LED na ɗauke ne da ƙananan ramuka masu gidan dara da ake kira “Pixels”, masu haɗuwa don ba da launin hoto da harafi ko dukkan abin da sikirin ɗin wayar ke bayyanawa.  Wannan nau’in sikirin na bayyana launi raɗau-raɗau, musamman manyan launukan asali – launin ja, da shuɗi, da kuma kore.  Bayan haka, sikirin nau’in LED na amfani ne da fasahar AMOLED, wanda ke iya kunnawa da kashe hasken dake wasu daga cikin waɗancan ƙananan ramuka (Pixels), lokaci zuwa lokaci.  Abin da wannan ke nufi shi ne, ba a kowane lokaci bane hasken ke tabbata akan sikirin ɗin ba, saɓanin yadda lamarin yake a ɓangaren sikirin nau’in IPS/PLS.  Hakan ke sa a samu ƙarancin cin batir ko caji a ɓangaren AMOLED.

Sai bayani kan dalilan tsada ko araha sanadiyyar bambancin sikirin.  A taƙaice dai, wayoyin salula masu ɗauke da sikirin nau’in AMOLED, wato: “LED” kenan, sun fi tsada idan aka kwatanta su da wayoyi masu ɗauke da sikirin nau’in IPS/PLS.  Domin sun fi ƙarancin cin caji, sannan launuka sun fi bayyana raɗau-raɗau.  Bayan haka, ko wajen canja sikirin ma, sikirin ɗinsu ya fi tsada.  Gaibin wayoyin Tecno, da Infinix (irin su Infinix Hot 12i, da Hot 30i, da Samart 7 HD, da Samart 7 Plus) da iTEL, da ƙanan wayoyin kamfanin Samsung irin su Samsung Galaxy A14 (4G),  da Samsung Galaxy A03, da A02, da A04s, duk suna ɗauke ne da sikirin nau’in PLS/IPS.  A yayin da wayoyi masu tsada na can sama kuma suke ɗauke da sikirin nau’in AMOLED, irin su iPhone daga kan iPhone 12 zuwa sama, duk suna ɗauke ne da sikirin nau’in AMOLED.  Haka ma wayoyi irin su Samsung Galaxy A24, da A34, da A53,  da sauran wayoyin dake jerin Samsung S Series, duk suna amfani ne da nau’in Super-AMOLED.

Girman Fuska ko Sikirin

Daga cikin dalilai har wa yau akwai girma – faɗi da tsayi – na fuska ko sikirin ɗin wayar salula.  Duk da cewa akwai wayoyin dake da manyan fuska amma masu araha ne, kamar yadda ake da masu matsakaicin fuska amma masu tsada, sai dai galibin wayoyin salula masu manyan sikirin suna da tsada.  Girma kuwa ya kama daga inci 6 zuwa inci 6.7, har masu inci 7 akwai.

Ma’adanar Wayar Salula (Memory/Storage)

- Adv -

Dalilan tsada ko arahar wayar salula na iya samo asali daga nau’i da girma ko ƙarancin mizanin ma’adanar wayar salula.  Waɗannan su ake kira “Memory” da “Storage” a harshen turanci.  Babu wayar salular da za ta iya aiki ba tare dasu ba.

Waɗannan ma’adanai dai nau’i biyu ne; akwai ma’adanar wucin gadi, wannan ita ake kira: “Random Access Memory” ko “RAM” a gajarce.  Haka kuma ana kiranta da suna: “Memory”, wato wajen adana bayanai.  Kamar yadda ɗan adam yake amfani da ƙwaƙwalwarsa wajen adana bayanai dai a taƙaice.  Sai kuma ma’adanar bayanai da ake kira: “Read Only Memory” ko “ROM”.  Ana kuma kiran wannan nau’in ma’adana da suna: “Storage”, ko “Internal Storage”.   Kasancewar dukkansu ma’adanai ne, sai dai zai dace mu san meye bambancin dake tsakaninsu, kuma ta yaya suke zama dalilan tsada ko arahar wayar salula?

Ita dai ma’adanar ROM ko “Internal Storage”, ita ce ma’adanar dake ɗauke da dukkan bayanan dake kan wayar salula.  Bayan an gama ƙera ɓangarorin wayar salula, aka haɗe su wuri guda a matsayin waya, ana loda mata dukkan bayanan da za ta yi amfani dasu ne wajen ma’amala da mai sarrafa ta. Waɗannan bayanai duka ana zuba su ne a wannan ma’adana ta dindindin.  Ko da wayar na kunne ko tana kashe, duk waɗannan bayanai suna nan daram a cikinta.

Ma’adanar ROM na iya ɗaukan zallar bayani a sigar rubutu.  Tana iya ɗaukan bayanan sauti (Audio).  Tana iya ɗaukan hotuna (Images/Pictures).  Tana iya ɗaukan hotuna masu motsi, wato bidiyo kenan.  Shi yasa a fannin kimiyyar sadarwa na zamani ake kiranta da suna: “Dynamic Memory”.  Domin kana iya ɗora mata dukkan waɗannan nau’ukan bayanai kai tsaye, ba tare da sai ka kintsa ma kowane irin bayanai ɓangarensa ba.

Wannan ma’adana ta ROM dai mataki mataki ne wajen mizani, wato girma kenan.  Ta la’akari da wayoyin salula na wannan zamani, mafi ƙarancin mizanin irin wannan ma’adana dai shi ne 16GB.  A sama kuma ana samun mai 32GB, sai 64GB, sai 128GB, sai 256GB, sai 512GB.  Nan gaba kaɗan kuma muna sa ran samun wayar salula mai girman mizanin ma’adanar da ta kai 1TB; wato Gigabyte 1,000 kenan.

Yanayin girman mizanin ma’adanar wayar salula na daga cikin dalilan dake sa wayar tayi tsada ko araha, idan an kwatanta ta da akasinta.  Misali, a galibin lokuta, wayar salula mai ɗauke da mizanin ma’adanar da ta kai 64GB, tafi wacce ke ɗauke da 32GB tsada, har ka hauda zuwa mafi girman mizani.  Haka abin yake idan ka gangara ƙasa shi ma.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.