Sakonnin Masu Karatu (2016) (12)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

81

Assalamu alaikum. Ina mai maka jinjina da fatan alkhairi saboda wannan namijin kokari da kake wajen ilimantarwa, da fadakarwa, da tunatarwa da kake mana; Allah ya sa hannu cikin lamuranka. Tambayata ita ce, ina amfani da wayar “Nokia Lumia 820,” idan ina amfani da manhajar Whatsapp takan cinye min ma’adanar kan wayata (Phone Storage), kuma hakan kan sa sako bazai shigo min ba sai na goge wani abu. Shin, yaya zan yi in kaucewa wannan matsalar?  Domin wataran nakan rasa abin da zan goge.  Idriss Isa Lamido: lamidopkm01@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Abin da nake fahimta shi ne, ma’adanar wayarka na cikewa, sanadiyyar hakan sai wayar ta kasa gaba ko baya, saboda karancin ma’adanar wucin-gadi dake baiwa manhajoji damar sakewa da aiwatar da umarnin mai waya.  Da farko dai, wayoyin kamfanin Microsoft masu suna: “Windows Phone” nau’in “Lumia” ba su da wajen makala ma’adanar mai waya (User Memory).  Wannan shi ne babban dalilin da yasa wayarka ke yawan sumewa ko zama lakakai-lakakai.

Abu na biyu, dalilin hakan shi ne, da gangar kamfanin yaki sanya wannan kafa, domin a galibin lokuta kwayoyin cuta (Virus) kan fara isa ga babbar manhajar wayar ne ta hanyar bayanan da ke cikin ma’adanar “SD Card,” ko “Memory Card.” Ko dai sanadiyyar jona wayar da kwamfutar dake dauke da kwayar cuta (Virus), ko kuma ta amfani da fasahar “Bluetooth” wajen karban hotuna ko bayanai ko bidiyo daga wata waya mai dauke da kwayar cutar.  Ta duk inda aka bi dai, wannan shi ne dalili dake sawwake wa kwayoyin cuta isa ga babbar manhajar waya.  Daga nan kuma sai ta harbu.

- Adv -

Wannan shi ne dalilin da yasa kamfanin Micsoroft, a wayoyin nau’in “Lumia,” yaki sanya ramin kara ma’adanar waya.  Kuma ga dukkan alamu, ya bi tafarkin kamfanin Apple ne, kamar yadda yake a wayoyinsa da na’urorin sarrafa bayanansa, irin su: “iPhone”, da “iPad”, da su “iPod.”  Ba wannan kadai ba, hatta sauran kamfanonin waya irin su LG, da Sony, da Samsung, wadanda suke sanya kafar kara ma’adanar mai waya kai tsaye, akwai ‘yar dabara da suke yi, amma ba dukkan mai amfani da waya ya san hakan ba.  Hanyar gane haka na samuwa ne idan ka kasa matsar da wata manhaja dake ci maka ma’adanar waya, daga waya zuwa ma’adanar “SD Card.”  Abin da za ka iya yi kai tsaye da ma’adanar da ka kara wa wayarka kawai shi ne loda mata bayanai na sauti ko bidiyo.  Amma idan manhaja ce kake son saukarwa ka dora a ma’adanar waya, sai abin yaki.

Ba dukkan wayoyin ke da wannan matsala ba.  Galibi ma sababbin wayoyin da ake kerawa a yanzu ne aka fara sa musu wannan kariyar kai tsaye.  Musamman irin su Samsung Galaxy J5, ita ma haka take.  Galibi ma wayoyin Samsung nau’in “J” (kamar su J5 misali) da “A” (irin su A5, da A7, da A8), duk an jona musu wannan kariya a boye.  Don haka, duk wata manhaja da za loda wa wayarka, ida kayi kokarin gusar da ita zuwa ma’adanar Memery Card, sai ta ki.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik. Barka da marece. Don Allah ina so ka turo min Kasidar Tsibirin Bamuda zuwa ga wannan adireshin: hafizuharunahadejia@gmail.com.  Ka huta lafiya. Daga Hafizu Haruna Hadejia.

Wa alaikumus salam, barka da warhaka.  Ka duba akwatin Imel dinka, na aika maka kasidar kamar yadda ka bukata.  Allah amfanar damu baki daya, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.