Tsarin Amfani da Wayar Salula (1)

Kashi na 26 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

609

Matashiya

A baya bayanai sun gabata kan tasirin mu’amala da wayar salula, ga al’umma baki daya, da kuma tasirin hakan ga kebantattun mutane.  Wannan na da muhimmanci wajen taimawa wa mai amfani da wayar salula ya san yadda zai yi, don kada ya afka cikin wadannan munanan tasiri su shafe shi.  Duk wani abu na mu’amala yana da bangare biyu ne; da bangaren amfani, da kuma bangaren cutarwa. Ya danganci yadda mai amfani da abin yayi.  A yau kuma ga bayanai kan tsarin amfani da wayar salula a warware.  Domin sanin tsarin amfani da wayar salula ne zai taimaka wa mai mu’amala fahimtar hanyoyin da zai bi wajen magance dukkan matsalolin da ke jawo munanan tasiri wajen mu’amala da wayar salula. Ga bayanan nan tafe:


Sayan Wayar Salula

A al’adance, kafin aiwatar da duk wani abu da wayar salula, mai mu’amala yana da bukatar mallakar wayar salular tukun.  Duk da cewa ba duk mai amfani da wayar salula bane yake mallakarta. Akwai wadanda suke kira da karbar kira daga ‘yan uwansu ba tare da sun mallaki waya ba. Sai dai ba su da yawa, musamman ma da ya zama wayoyin salula sun kara araha yanzu, sanadiyyar yawaitarsu a kasuwa, da samun nau’uka daban-daban, daga kamfanonin kera waya musamman na kasar Sin (China). Mallakar wayar salula shi ne abu na farko, ga duk mai son sanin tsarin amfani da wayar.  Kowace wayar salula kan zo ne da kundin sarrafa ta, wato “Manual” kenan a harshen Turanci.  Sai dai kuma a galibin lokuta, irin yadda muke amfani da waya ta kowane yanayi kan sa idan ta samu matsala mu kasa samun bayanai kan yadda za mu gyara. A wasu lokuta ma bamu cika damuwa da wannan kundi da waya kan zo da shi ba, duk da muhimmancinsa.

Akwai wayoyin salula nau’uka daban-daban. Sau tari jama’a kan aiko sakon tes ko su kira suna neman bayani kan wace irin waya ya kamata su saya? Sai in rasa amsar da zan basu.  Wasu lokuta sai na musu tambaya: “wace irin bukata kake da ita a waya?” Irin amsar da na samu, shi ke bani hasken basu shawarar da ta danganci bukatunsu.  Babu wata wayar salula daya tinkwal da za ace ta fi kowacce. Illa dai kowacce da yanayinta, da irin tsarinta, da kuma wasu siffofi da ta kebanta dasu.  Haka kamfanonin waya ke kera su. Akwai wacce musamman don sawwake mu’amala da Intanet aka kera ta. Akwai wacce don iya aika sakon tes aka kera ta. Akwai wacce musamman don sauraron sauti aka kera ta.  Ga su nan dai. Wannan ke nuna mana cewa lallai babu wata wayar salula wacce za a ce ta fi kowanne.

Idan muka fahimci haka, sai mu san cewa abin da muke bukata kadai ya kamata mu rika la’akari da shi a jikin waya.  Kada ka ga jama’a na ta yayin waya, kawai kaima ka je ka saya, don kana da kudi. In har kana da manufar da ta sa kake son waya, a karshe za ka ga cewa wannan wayar da ake yayi bata dace da kai ba. Na sha samun mutane da yawa da ke cewa, sun sayi waya sabuwa don sun ji ana ta kuranta ta, amma daga baya sai suka ga ashe wacce suke amfani da ita a baya ma ta fi ta.  Me yasa? Saboda abubuwan da suke bukata babu su a cikin sabuwar wayar.

Don haka mu kiyaye; abin da muke bukata a waya kadai ya kamata mu yi la’akari da shi idan muka tashi sayan waya. Ba wayar salula kadai ba, hatta mota, ko mashin/babur, ko talabijin, ko kwamfuta, duk wannan ka’ida ta kamata mu rika amfani da ita wajen sayansu. Idan bukatarka yawaita rubutun tes ne, wato SMS, ka bincika, akwai wayoyin da ke da wannan dama mai kayatarwa, daga allon shigar da bayanansu (Keypad), zuwa masarrafar rubuta sakon (SMS Application), duk za su kayatar da kai.  Idan kuma kana son waya ce mai bayyana sauti sosai kamar zai fasa dodon kunne, duk akwai.  Idan kana son mai sawwake mu’amala ne da fasahar Intanet, duk akwai.  Sai ka duba bukatarka, sannan ka dubi yanayin waya kafin ka saya.  Dole ne ka san cewa, biyan bukata ya fi dogon buri.

Idan ka zo sayan wayar salula har wa yau, ka lura da abubuwa guda biyu.  Abu na farko shi ne aljihunka.  Zai iya yiwuwa akwai wayar da kake so, amma kuma karfinka bai kai ba. Ka hakura da wacce karfinka zai iya mallaka. Kada wata sabuwar waya ta burge ka.  Idan za ka iya sayar da wacce kake amfani da ita ka cika kudi ka sayi wata, ka yi.  Idan ka san ba za ka iya ba, ka nisanci cin bashi don sayan wayar salula idan ba tsananin lalura bane ya haddasa haka.  Idan kuwa ba haka ba sai ka mutu da bashi.  Domin sababbin wayoyi sun dinga bayyana kenan, ba za su kare ba.  Dole ne mutum ya zama mai tattali.  Duk abin da ka san ya fi karfin aljihunka, kuma ba za ka iya mallakarsa ta dadi da kwanciyar hankali ba, to, ka hakura da shi.  Allah bai yi yatsun hannayenmu daidai ba wajen tsawo, balle samunmu.

Abu na biyu da ya kamata kayi la’akari da shi kuma shi ne mahallin da kake.  Idan kana rayuwa ne a inda barayin waya sun yawaita, ko inda sa-ido ya zama ruwan dare, to, ka zama mai kaffa-kaffa wajen sayan waya mai tsada.  Idan kuma har ka saya, to ka zama mai alkinta ta.  Idan kuwa ba haka ba, to sai a sha ka musilla, in ji wani mawaki dan kasar Jega.

- Adv -

Yin Kira da Amsa Kira

Wannan shi ne babban wazifar wayar salula na farko, tun fil azal.  Kafin duk wasu kyale-kyale su samu a jikin wayar salula, abu na farko da aka fara samarwa a waya shi ne tsarin amsawa da karbar kira na sauti.  Tsarin aiwatar da kira shi ne abu na farko kuma wanda ya fi maimaituwa wajen mu’amala da kowace wayar salula.  Akwai maballai da aka tanada don amsa kira idan aka kira ka. Haka akwai inda za ka matsa, ka shigar da lambar wanda kake son kira.  Da zarar ka matsa, aiki ya kare maka, sai dai sauraro. Idan ya daga kirar za ka gane, domin za ka ji wayar ta daina ruri (Ringing).

Daga nan sai ka yi masa sallama idan musulmi ne. Idan kuma da ya daga kirar ya maka sallama, saboda ya san layin, sai ka amsa.  Amma dai mu sani, kalmar “Hello” ko halo da muke cewa a yayin yin kira, bata dace ba.  Ko a turai, wanda ya daga waya shi yake cewa “Hello”.  Domin kalmar “Hello” harshen Faransanci ce, wacce aka yi amfani da ita a karni na sha tara (19TH Century), kuma Turawa na amfani da ita ne don jawo hankalin abokin magana.  Don haka, wanda ya daga waya shi ke cewa halo, shi kuma mai kira ya gabatar da kansa.

To amma duk musulmi ya kamata ya lazimci kalmar sallama, wato “Assalaamu Alaikum” a kowane lokaci, ba sai an zo shiga gida kadai ba.  Domin tsarin aiwatar da kira ta wayar salula ma ai kamar shiga gida ne.  Wanda ya kira shi ne a matsayin bako mai sallama a bakin kofa ko mai kwankwasawa.  Wanda ake kira kuma shi ne mai karban bako, mai amsa sallama kenan.  Shi yasa ma galibin malamanmu na musulunci idan ka kira wayarsu, da zarar sun dauka, sai kaji sun ce maka: “Na’am.” Kai kuma ya rage a gare ka kayi sallama sannan ka gabatar da kanka.  Tunda kai ne ka shigo “gidansa.”

A wasu lokuta muna kuskure. Idan muka kira mutum ya daga, sai kawai mu kama gaisuwa ko gabatar da abin da muke bukata.  Wannan bai dace ba.  Duk sadda ka kira waya aka daga, abu na farko da za ka yi bayan sallama, shi ne gabatar da kanka.  Ka kaddara gidansa ne ka zo shiga.  Idan ka gabatar da kanka, daga nan zai samu natsuwa.  Amma idan wanda ka kira ya sanka, to a nan babu maganar gabatar da kai.  Da zarar ka gama magana, sai kayi bankwana, tunda kai ne ka kira.  Bai dace da zarar ka kira mutum, ka gama biyan bukatarka sai kawai ka kashe waya ba.  Wannan alama ce ta rashin natsuwa, ko da kuwa wanda ka kira kasa yake da kai wajen shekaru.  Yana da kyau ka yi masa bankwana. Misali, kace masa “Sai an jima,” ko “Wassalaamu alaikum.”  A nan ya san cewa lallai an gama sadarwa.  Idan yana da bukata nan take zai jawo hankalinka.

Haka mai amsa kira, bai dace da zarar ya gama bayani ya kashe wayar ba.  Domin ba shi ya kira ba.  Sai ya jira sai ya ji bankwanan mai kira, ko kuma mai kira ya kashe wayar da kansa, sannan ya ajiye.  Bayan haka, wasu kanyi wani abin da bai dace ba.  Idan suka kira ka, ka daga, har kuka gama magana, sai su maka bankwana, amma su ki kashe wayar, suna sauraron abin da za ki ci gaba da shi na zance tare da abokan hirarka a inda kake.  Wasu kanyi haka idan suna tuhumar abokin zancensu da algushi wajen magana.  To ka ga idan kaine mai amsa kira, da aka maka bankwana, sai baka kashe wayar ba kawai ka ajiyeta, to ana jin duk abin da kake fada.  Don haka da zarar ka ji an maka bankwana, to, alamar sadarwa tsakaninka da abokin magana ta zo karshe kenan, sai ka kashe wayar.

Bayan haka, kasancewar kira ta hanyar wayar salula yana jan kudin kati, wajibi ne da zarar ka kira, ka kuma gabatar da kanka, to nan take kayi abin da ya kawo ka. Mukan shantake a kan layi muyi ta fadin banza da wofi marasa fa’ida, wannan almubazzaranci ne.  Mu kuma gode Allah, domin a wasu kasashe da wanda yayi kira da wanda aka kira, duk sai an caje su kudin waya.  To mu a nan ba mu da wannan tsarin.  Duk da haka bai kamata mu bata lokacinmu a banza ba cikin abin da ba shi da fa’ida. Idan kuma aka kira ka a waya, sai ya zama kana da wata bukata da kake so ka tattauna da wanda ya kira ka, sai ka nemi izninsa, ba wai kawai ka ci gaba da wasu bayanai ba. Ta yiwu babu kudi sosai a wayarsa, kuma ba zai iya tsayar da kai ba, nan take kuna cikin magana sai kaji wayar ta yanke.  Kai ka ja.

Sannan kuskure ne mutum ya kira ka ko ka kira shi, kuna cikin magana sai ranka ya baci, ka yanke waya ba tare da ka sanar da shi ba.  Na san duk muna yin haka idan rai ya baci, amma kuskure ne; musamman idan kai ne aka kira.  Kuskure ne ka kashe wayar. Sai ka sanar da shi, misali, sai ka ce masa: “…wane/wance, me zai hana mu bar tattaunawa wannan al’amari, domin raina ya baci….don Allah mu bar zancen haka…in kuwa bamu bari ba, a mini hakuri, zan ajiye wayar.”  Ka ga idan ka gaya wa abokin zancenka haka, ya san ka masa adalci.

A wasu lokuta idan aka kira mu, sai mu daga wayar, amma saboda ba mu son magana da mai kira, sai mu yi karya; mu ce muna mitin, ko muna cikin aji, ko kuma mu ki daukar wayar da gangan, ayi ta kira ba iyaka.  Duk wannan ba shi daga cikin tsarin amfani da wayar salula.  Domin karar kiran zai ta damunka, ko wadanda suke wurin, idan ka ki dauka.  Ko kuma karyar da kayi za a rubuta shi a littafinka.  Akwai kuma masu daukar wayar, amma sai su ba wasu da ke wurin, su gaya musu abin da za su fada, wanda ba gaskiya bane.  Wannan kuskure ne shi ma.  An taba kiran wani mai gidana a waya, muna zaune tare muna aiki, sai yace in amsa wayar in ce ba ya nan ya fita, alhali ga shi muna tare.  Sai na roke shi, nace: “…to Oga mai zai hana ka fita kawai daga ofishin, sai ince masa ka fita.”  Sai nan take ya fice daga ofishin, sai na amsa wayar, nace ya fita.

Wannan hila ce, ma’ana dabara ce wacce shari’a bata so ba.  To amma dai ya fi da zan yanka karya ince ba ya nan alhali ga shi a zaune ina ganinsa.  Ya kamata mu rika shirya gaskiya cikin al’amuranmu.  Wannan zai sa mu samu nutsuwa a zukatanmu kan duk wanda ya kira mu. Idan abin da yake bukata mai yiwuwa ne, mu amsa mu bashi ko mu masa alkawari, idan ba mai yiwuwa bane, kai tsaye mu gaya masa gaskiya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.