Tasirin Killace Jama’a Sanadiyyar Cutar COVID-19 Ga Kamfanoni da Kafofin Sadarwa na Zamani a Duniya (3)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 12 ga watan Yuni, 2020.

238

Apple Inc.

Bayan riba da kamfanonin sadarwa na Intanet ke ta samu sanadiyyar zaman gida da jama’a ke yi don kauce wa kamuwa da cutar COVID-19, kamfanin Apple Inc dai nakasa ya samu, musamman ganin cewa babbar hajar da yake kerawa sannan ya sayar, ita ce wayar salula da sauran kayayyakin sadarwa, wanda kuma sanadiyyar shiga wannan annoba, ya rufe shagunansa dake duniya gaba daya, in ka kebance na kasar Sin da kuma shago daya dake kasar Koriya ta Kudu (South Korea).  Kamfanin Apple dai shi ne mai kera wayar salula nau’in iPhone, da iPad da iPod da sauran makamantansu.

A marhalar kasuwanci na farkon wannan shekara dai, yayi cinikin dala biliyan hamsin da takwas ne da miliyan dari uku da sittin ($58.36bn).  Wannan adadi, duk da cewa makodan kudi ne mai yawa, sai dai faduwa ne gare shi.  Domin ya ragu da kashi 0.05% in aka kwatanta da abin da ya samu a marhalar shekarar da ta gabata.  A bangaren iPhone yayi cinikin dala biliyan ashirin da takwas da miliyan dari tara da sittin ($28.96bn), shi ma ragi ne da kashi 7% kan cinikin da yayi a baya.  Sai dai kuma a bangaren sauran hajojinsa irin su: Apple iCloud, da Apple Music, an samu karin kudaden shida da kashi 16% da 38.4% a dukkan bangarorin biyu.  A bangaren kwamfutocinsa nau’in Mac kuma, anyi cinikin dala biliyan biyar da miliyan dari uku da hamsin ($5.35bn).  Bangaren iPad ya kawo dala biliyan hudu da doriya ($4.8bn), sai na’urorin daurawa (Wearables – Apple Watch dsr) an samu cinikin dala biliyan goma da miliyan goma ($10.01bn) ne kacal.

Ganin yadda kasuwa ta fara tutsu tun cikin watan Janairu, yasa kamfanin Apple ya fitar da wata wayar salula mai saukin farashi da ya kira: “iPhone SE”.  Farashinta duk bai shige naira dubu dari ba, in tayi tsada kenan.  Kamfanin yayi haka ne ganin yadda komai ya tsaya, kuma shaguna duk an rufe.  Galibin jama’a zasu rage kashe kudade, sai abin da yake na lalura kawai.  Ganin cewa wayoyin iPhone suna da tsada, sai yayi masu saukin farashi ga masu bukata.  Amma duk da haka wannan azanci nashi bai biya ba.  A taronsa da ya gudanar ta hanyar bidiyon sadarwa a Intanet ga masu hannun jarin kamfanin, Tim Cook, shugaban kamfanin Apple, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda abubuwa suka zama haka.  A karshe yake cewa: “Wannan wani irin yanayi ne da bamu taba tunaninsa ba.  Kuma ina fatan kada in kara samun kaina a cikin wannan yanayi (a matsayina na shugaban kamfanin).”

Samsung Electronics

Duk da cewa kamfanin Samsung kamfani ne da yake kera wayoyin salula kamar kamfanin Apple, sai dai ya sha bamban da kamfanin Apple ta hanyoyi da dama.  Domin kamfanin Samsung, bayan wayoyin salula da ya kware wajen kerawa da tallatawa, yana kera kwamfutoci, da ma’adanan kwamfuta, da talabijin, da agogon sadarwa da dai abubuwa da dama da suka danganci fannin sadarwa.  Kamfani ne babba.  Kamfanin ya samu kudaden shiga da suka kai tiriliyon hamsin da biyar da biliyan dari uku da talatin, na Won din kasar Korea ta Kudu (KRW 55.33trn).  Ya kuma ci ribar Won tiriliyan shida da biliyan dari hudu da hamsin (KRW 6.45trn).  Tirkashi.

- Adv -

Amma duk da haka, kamfanin ya sanar da cewa ya samu ragowan kudaden shiga da kashi 7% kasa da abinda ya samu a marhalar kasuwanci na shekarar 2019.  Haka ma bangaren ribar da yaci.  Yace an ribar ta ragu da Won biliyan dari bakwai (KRW 0.7trn).  A fagen wayoyin salula kamfanin yace an samu nakasu, kamar dai abin da ya shafi kamfanin Apple kenan.  Domin ba don fitar da sabuwar wayar salula nau’in Samsung Galaxy S20 da yayi ba, to, da abin yayi muni.

MTN Nigeria

Kamfanin MTN, wanda ke da reshe a nan gida Najeriya, shi ma mun duba tagazawarsa don kokarin tantance lamarin; shin, manyan kamfanoni ne kadai abin ke shafa ko har da na gida Najeriya.  Da muka duba sai muka samu kamfanin MTN Nigeria ya samu kudaden shiga da ya kai naira biliyan dari uku da ashirin da tara da miliyan dari biyu (N329.20bn).  Wannan adadi dai kari ne kan cinikinsa na marhalar shekarar 2019 da kashi 16%.  A bangaren riba kuma, kamfanin MTN ya samu ribar naira biliyan hamsin da daya da miliyan ashirin, cikin watanni uku kacal – tsakanin Janairu zuwa Maris, 2020.  Tirkashi.  Wannan adadi na riba dai kari ne da kashi 5.3% kan na baya.

A cikin marhalar, kamfanin ya samu karin masu rajista wajen miliyan daya da dubu dari bakwai (1.7m subscribers).  Wannan ya kawo adadin rayayyun masu rajista a kamfanin zuwa miliyan ashirin da shida da doriya.  A halin yanzu dai kamfanin MTN ne ke dauke da masu rajistar layukan wayar salula mutum miliyan hamsin da biyar da doriya.

Don tantancewa, cikin adadin cinikin da kamfanin yayi a wannan marhala, naira biliyan dari biyu da ashirin da bakwai da miliyan sittin (N227.60bn), duk kudin kiran waya ne na murya – Voice Calls.  A yayin da kamfanin ya samu naira biliyan arba’in da shida da miliyan dari shida (N46.6bn) daga kudin “data” da muke ke saya kadai.  Sai dai duk da wannan tarin kudin shiga, kamfani yace an samu ragi a bangaren kudin shiga da ya shafi kiran waya, yayin da aka samu kari kuma a kudin shiga a bangaren masu mu’amala da fasahar Intanet da kamfanin yake sayarwa da kashi 59.2%.

Kammalawa

Kamar yadda bayanai suka gabata, duk da cewa tattalin arzikin duniya ya tasan ma durkushewa sanadiyyar yaduwar wannan cuta ta COVID-19, inda hakan ke sanadiyyar mutuwa da durkushewar kasuwanci da sana’o’i a dukkan bangarori na nahiyoyin duniya, said ai galibin kamfanonin sadarwa suna samun karin kudaden shiga sosai, sanadiyyar sauyar yanayin rayuwa daga Zahiri zuwa rayuwa ta hanyar kafafen sadarwa na zamani.  Wannan ke baiwa kananan kamfanonin sadarwa dake kasashe masu dukiya damar mikewa, saboda dogaro dasu da ake yi wajen gudanar da rayuwa.  Sai dai kuma, wannan ci gaba da wadannan kamfanoni ke samu, somin tabi ne.  Babu wanda ya san me gobe za ta haifar; shin, ci gaban zai dore, ko kuwa?  Domin bayanai daga masana harkar kiwon lafiya na nuna cewa wannan cuta ta COVID-19 ta fara canza salo da hanyoyin kamuwa.  In kuwa haka ne, ashe da sauran rina a kaba kenan.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.