Shawarwari Ga Gwamnatin Tarayya Kan Hanyoyin Ciyar Da Najeriya Gaba A Fannin Kimiyya Da Ƙere-Ƙere (7)

Fatanmu shi ne Mai Girma Shugaban Ƙasa ya wakilta wani sashe na jami’a da hukumomin gwamnati dake ƙarƙashin kulawarsa, don samar da wani tsari gamamme da zai motsa hanyoyin ci gaba a wannan fanni baki ɗaya.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 28 ga watan Yuli, 2023.

62

Samar da Makamashi Wadatacce

Daga cikin dalilan dake haddasa tsadan kayayya a Najeriya akwai ƙaranci da tsadan kuɗin wutar lantarki da kamfanoni da masana’antu ke biya wajen tafiyar da ayyukansu.  Duk da cefanar da ɓangaren samar da wutar lantarki da Gwamnati tayi, har yanzu ba mu da ingantacciya kuma wadataccen wutar lantarki.  Akwai kamfanoni da yawa masu son zuwa Najeriya don zuba jari, amma babbar matsalar da suke dubawa bayan cin hanci da rashawa, ita ce matsalar wutar lantarki.  Idan muka yi la’akari da ƙasashen da suka ci gaba a fannin kimiyya da ƙere-ƙere, za  mu ga basu samu wannan matsayi ba sai da suka yaƙi zuciyarsu wajen tabbatar da samuwar ingantacciyar wutar lantarki a ƙasarsu.  Wannan zai sa makarantu su samu ilmi mai inganci sanadiyyar ingantacciyar karantarwa daga malamai.  Shi zai sa kamfanonin ƙere-ƙere su samu kwanciyar hankali, ya zama damuwarsu kan bincike ne kawai da abin da za a ƙera, amma ba akan makamashi ba.  Wannan zai sa har wa yau a samu ƙarkon kayayyakin ƙere-ƙere da ake amfani da su.  Idan kuwa gwamnati bata yi haka ba, to da sauran rina a kaba.

Lura da Buƙatun Ƙasa/Al’umma

Abu na kusa da ƙarshe da hukuma za ta yi shi ne ta lura da buƙatar ‘yan Najeriya.  Meye muke da tsananin bukatuwa zuwa gare shi?  Kuma yaya za a tabbatar da samuwarsa?  Wannan shi ne abin da ya kamata  mu lura dashi, ba wai mu zama “’yan abi Yarima a sha kiɗi” ba – don ƙasar Amurka ta je duniyar wata, wannan ba shi zai sa mu ma dole mu je ba.  Don ƙasar Sin ta harba kumbo, ba shi zai sa mu ma dole mu harba ba.  Don ƙasar Indiya ta ƙera makamin Nukiliya, har wa yau, ba wannan bane zai zama mana dalili dole mu ma sai mun ƙera ba.  Don me?  Bukatunmu kaɗai ya kamata mu duba.  Idan muka  dubi ƙasa irin Malesiya misali, za mu ga cewa duk da ci gabanta, bata damu da ƙera makamin Nukiliya ba, balle har ta kama cuku-cukun zuwa duniyar wata.  Abin da ƙasar ta sadaukar da kanta wajen samarwa shi ne ingantaccen ilmi, da bunƙasa fannin ƙere-ƙere da fasahar sadarwa, da kuma samarwa tare da tabbatar da doka da oda a ƙasarta.  Duk wanda ya ziyarci wannan ƙasa zai fahimci haka.  To amma ta yaya muka yanke shawarar harba tauraron ɗan adam, alhali ba mu da cikakken tsarin doka da oda, bamu kawar da ci hanci da rashawa ba iya gwargwado, bamu samar da ingantaccen ilmi ba, balle har mu tabbatar da samuwar ingantacciyar wutar lantarki?  Idan mun ce ai ba a Najeriya bane tauraron ke da asali, amma ai muna da cibiyar dake lura da shawagi ko bayanan da yake tarkatowa daga sararin samaniya a nan ƙasar, wadda kuma dole ne sai da janareto take dogaro.  Anya, wannan ba tufka bane da warwara?

- Adv -

Shugabanci na Gari

Dukkan shawarwarin da muka kawo a sama, samuwarsu ta dogara ne kacokan kan shugabanci na gari; wani abu mai tsada da ƙasar nan ta rasa tun shekaru kusan hamsin da suka gabata.  Da shugabanci na gari ne kaɗai gwamnatin tarayya da na jihohi za su iya sadaukar da kansu wajen ganin wannan ƙasa ta gyaru, ta kintsu, ta zama ‘yantacciya daga ƙangin talauci, da ƙaskanci, da cin hanci, da rashawa, da dukkan abin da yake mata tarnaƙi wajen ci gaba.  Don haka, dole ne shugabanni su tabbatar da cewa sun yi abin da zai samar da maslaha ga al’umma, amma ba ga kansu ba.

Kammalawa

Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, a fili yake cewa lallai ƙasarmu na buƙatar kulawa ta ɓangaren kimiyya da ƙere-ƙere.  Tabbas a ɓangaren kimiyyar sadarwa akwai ci gaba, akwai kamfanonin sadarwar wayar salula da yawa kuma ana samun gasa mai tasiri a tsakaninsu.  Farashin kira da aika saƙonni sun ragu matuƙa idan aka kwatanta da lokuta ko shekarun baya.  A ɗaya ɓangaren kuma, an samu ci gaba a fannin fasahar Intanet da yaɗuwarta a wayoyin salula da sauran kayayyakin sadarwa na zamani.  Wanna ya haddasa ci gaba sosai a tsakanin al’umma, kuma ya samar da ayyukan yi ga matasa.

Fatanmu shi ne Mai Girma Shugaban Ƙasa ya wakilta wani sashe na jami’a da hukumomin gwamnati dake ƙarƙashin kulawarsa, don samar da wani tsari gamamme da zai motsa hanyoyin ci gaba a wannan fanni baki ɗaya.  Allah albarkaci wannan ƙasa tamu, ya kuma bamu juriya wajen yin abin da zai inganta rayuwar mazauna cikinta, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.