Shawarwari Ga Gwamnatin Tarayya Kan Hanyoyin Ciyar Da Najeriya Gaba A Fannin Kimiyya Da Ƙere-Ƙere (5)

Duk da taɓarɓarewan ilmi a ƙasar nan, akwai cibiyoyin bincike masu ƙoƙarin ƙirƙiro hanyoyin samar da sababbin kayayyakin ƙere-ƙere a ƙasar nan.  To amma saboda shi bincike wani abu ne da ake fara shi a takarda, kuma a ƙare shi a aikace, rashin ɗabbaƙa binciken yasa ba su da wani tasiri.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 14 ga watan Yuli, 2023.

49

Durƙushewar Kamfanonin Ƙere-ƙere

Bayan samun ‘yancin siyasa gwamnatin Najeriya ta yi ƙoƙarin ciyar da ƙasar gaba a fannin ƙere-ƙere ta hanyar samar da kamfanonin ƙera-kere (na motoci, da mashina, da sauran kayayyakin aikace-aikace) a gida, tare da shigowa da kayan aikin don ƙera abubuwan da ake buƙata ba tare da dogaro kan wasu ƙasashe ba.  Wannan tsari na ci gaban tattalin arziƙi mai suna Import Substitution Industrialization Policy, ya fara aiki, inda har gwamnati ta kafa masana’antun ƙera motoci da ɓangarorinsu – kamar Fiat, da Leyland da Stear – da kuma kamfanonin sarrafa ƙarafa – irin su Kamfanin Sarrafa Ƙarafa na Delta, da Kamfanin Sarrafa Ƙarafa na Ajaokuta – da aka samar don ƙera bangarorin mota (Automobile Spare Parts).  Ƙarƙashin wannan tsari har wa yau, gwamnati ta tanadi masana’antar ƙera manyan ɓangarorin injina da mashinan masana’antu.  To amma saboda rashin damuwa da ci gaban ƙasar, haka gwamnati ta bar waɗannan kamfanoni ko masana’antu da ta fara kafawa don wannan gagarumin aiki mai mahimmanci suka taɓarɓare.  Domin daga baya an daina shigowa da kayayyakin da waɗannan masana’antu ke buƙata don ci gaba da aiki, kuma a haka suka durƙushe, aka sallami ma’aikatan dake ciki; tsarin ya mutu.  A ɗaya bangaren, ƙasashe irin su Brazil da Malesiya sun ci gaba nesa ba kusa ba a wannan fanni, alhali kuma cikin lokaci ɗaya muka fara dasu.

Rashin Ɗabbaka Sakamakon Binciken Ilmi

Duk da taɓarɓarewan ilmi a ƙasar nan, akwai cibiyoyin bincike masu ƙoƙarin ƙirƙiro hanyoyin samar da sababbin kayayyakin ƙere-ƙere a ƙasar nan.  To amma saboda shi bincike wani abu ne da ake fara shi a takarda, kuma a ƙare shi a aikace, rashin ɗabbaƙa binciken yasa ba su da wani tasiri.  A wasu ƙasashe, da ire-iren waɗannan sakamakon bincike ake taƙama, su ake ɗabbaƙawa a aikace, har a ƙarshe a samar da sababbin hanyoyin ciyar da rayuwa gaba.  Bayan waɗannan cibiyoyin bincike har wa yau, akwai sakamakon binciken ilmin ƙere-ƙere dake fitowa daga manyan malamai masu hazaƙa a jami’o’inmu da kuma kwalejin fasaha da ƙere-ƙere, su ma ko kaɗan hukuma bata damu dasu balle tayi wani abu a kai.

Ni kaina sheda na kan haka.  Lokacin da nake sakandare, akwai malamin fannin Fiziya da ya ƙera jirgin sama mai saukar ungulu babba.  Duk sadda muka shiga dakin bincikensa don ɗaukan darasi, wannan abu da ya ƙera yakan bamu sha’awa tare da ƙayatar da mu sosai.  Sau tari mukan yi kwaɗayin ina ma ace gwamnati ko wani kamfanin ƙera jiragen sama ya ɗauke shi aiki, don ƙarasa ƙera wannan jirgi.

- Adv -

Rashin Damuwa a Ɓangaren Gwamnati

Ɗabi’un gwamnatin tarayya da na jihohi wajen rashin damuwa da haɓɓaka fannin kimiyya da ƙere-ƙere a Najeriya ya daɗa taimakawa wajen durƙeshewar wannan fanni.  Ba abin mamaki bane a yanzu ka samu kowace irin mota ce a ƙasar nan.  Duk irin wanda kake so akwai an shigo da ita.  A wasu lokuta ma, mako biyu ko uku da ƙera wata sabuwar mota, ka sa idonka a kan titunan ƙasar nan, za ka ganta tana tafiya.  Wasu masu alfarmar ma aka ce kamfanin ƙera motocin suke zuwa don zaɓan irin wacce suke so a ƙera musu.  Amma har yanzu babu wanda ya damu – daga gwamnatin tarayya har zuwa jihohi – don ganin an farfaɗo da tsarin samar da kamfanoni da masana’antun ƙere-ƙere a ƙasar nan.  An wayi gari galibin tsare-tsaren gwamnati waɗanda suka shafi fannin kimiyya da ƙere-ƙere da ka ake shirya su, ba a cika neman shawarar ƙwararru a wannan fanni ba.  A inda aka shawarce su wajen shirya tsare-tsaren kuwa, za ka samu ba a nemansu idan aka tashi aiwatar da shirin.  Wannan ke sa kaga an kashe kuɗaɗe maƙudai a fannin, amma sai ka nemi aikin da aka yi ka rasa.  Siyasa, da tumasanci, da ‘yangaranci, da cin hanci, da rashawa sun ɓata tsare-tsarenmu baki ɗaya.  Wannan ba zai haifar mana ɗa mai ido ba ko kaɗan.

Rashin Ilimi Ingantacce

Galibin makarantunmu suna fama da matsalar wutar lantarki, da hanyoyi marasa inganci, da rashin kayayyakin aiki masu taimakawa wajen samar da ilmi mai inganci.  Yin karatu a yanayi irin wannan, zai yi wahala a samar da dalibai masu inganci da za su yi wani abin kirki!  Wani malamin jami’a a kudancin ƙasar nan ya taɓa cewa, ba abin mamaki bane ka samu ɗalibi mai karatun fannin fasahar ƙere-ƙere (Mechanical Engineering) a jami’armu ya kasa bambance maka tsakanin sandar noti, wato bolt, da kuma noti, wato nut.  

A shekarun baya alƙaluman bayanai sun tabbatar ce, a duniya karankaf,  ƙasar Indiya ce ta uku a fannin ci gaban ƙere-ƙere da kimiyyar lantarki, inda take biye da ƙasar Amurka da Rasha.  A ƙididdigar shekarar 2003, ƙasar Indiya ta mallaki ƙwararru kan harkar kimiyyar ƙere-ƙere da lantarki sama da miliyan hudu.  A shekarar 1985 kaɗai ta yi rajistan Injiniyoyi 750,000.  Tana da manyan cibiyoyin koyar da ilmin kimiyya da fasahar ƙere-ƙere guda biyar da take kira India Institutes of Technology, waɗanda take basu tallafi mai tsoka don karantar da ingantaccen ilmi ga ‘yan ƙasarta da masu shigowa daga wasu ƙasashe.  Ƙasar Indiya na fitar da galibin hajojinta ne zuwa ƙasar Amurka da sauran ƙasashen Turai.  A shekarar 2008 ƙasar Indiya ta samu sama da biliyan goma sha ɗaya ($11bn) wajen sayar da manhajojin kwamfuta da ‘yan asalin ƙasarta suka gina kaɗai.

Mai Girma Shugaban Ƙasa, duk wannan ƙoƙari na ƙasar Indiya fa bai samu ba sai don sadaukar da kanta da tayi wajen ganin ta inganta ilmin kimiyya da ƙere-ƙere. Wannan ne kuma yasa jami’o’in ƙasarta da na ƙasashe irin su Malesiya da Singafo ke samun ɗalibai daga dukkan sasannin duniya, ciki har da ‘yan Najeriya!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.