Shawarwari Ga Gwamnatin Tarayya Kan Hanyoyin Ciyar Da Najeriya Gaba A Fannin Kimiyya Da Ƙere-Ƙere (1)

Mai Girma Shugaban Ƙasa, daga cikin dalilan da suka sa shafin Kimiyya da Ƙere-ƙere ganin dacewar gabatar da waɗannan shawarwari na musamman kan  ci gaban wannan ƙasa ba a fannin kimiyyar sadarwar zamani kaɗai ba, har da fannin ƙere-ƙere, waɗanda su ne ginshiƙi wajen ci gaban kowace ƙasa a duniya. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 16 ga watan Yuni, 2023.

108

Mabuɗin Kunnuwa

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da sabon Shugaban Ƙasar Najeriya, Alhaji Ahmad Bola Tinubu, tare da sauran zaɓaɓɓun gwamnonin jihohin da suka yi nasara a babban zaɓen da ya gudana a watan Fabrairu.  Kamar kowace gwamnati, nan take sabon shugaban ƙasa ya fara aiwatar da ayyukan ci gaban ƙasa.  Manyan ƙalubalen da ƙasarmu ke fuskanta dai kamar yadda kowa ya sani, su ne taɓarɓarewar tsaro da na tattalin arziƙin ƙasa.  Waɗannan matsaloli dai mun daɗe dasu a ƙasar nan, kuma a kullum ƙara taɓarɓarewa suke yi.  Daga cikin manyan dalilan dake sa hakan kuwa akwai tsananin cin hanci da rashawa da ƙasarmu tayi ninƙaya a ciki, da kuma ƙarancin nagartattun kayayyakin aiki na zamani da wasu ƙasashe ke amfani dasu wajen daƙile ire-iren waɗannan matsaloli, musamman a fannin tsaro.

Masana masu sharhi kan waɗannan al’amura dai sun danganta rashin ingancin kayayyakin aiki na zamani wajen daƙile matsalar tsaro da cin hanci da rashawa ne kan raunin dake tattare da hukumomin gwamnati da aka ɗora wa alhalin samar da abubuwan ci gaba a ƙasa.  A taƙaice dai, har yanzu Najeriya na da rauni a ɓangaren ci gaban kimiyya da ƙere-ƙere.  Daga jiragen da muke amfani dasu a fagen tsawo zuwa wayoyin salular da muke amfani dasu, kama da mafi ƙarancin abin amfani a gida, na zamani, kashi 80 cikin 100 duk shigowa dasu muke yi.  Don haka, a yayin da shugaban ƙasa ke ƙoƙarin magance matsalar tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasa, za mu so mu ƙara tunatar dashi wajabcin inganta ɓangaren da shi ne kaɗai zai iya taimakawa wajen kawo ƙarshen waɗannan manyan matsaloli da Najeriya ke fama dasu a yau.

- Adv -

Daga wannan mako in Allah Ya so, za mu gabatar da wasu jerin shawarwari ga Gwamnatin Tarayya da Hukumomin da aka ɗora musu alhalin fannonin kimiyya da ƙere-ƙere, dangane da hanyoyin da za su taimaka wajen inganta wannan fanni.  Sai dai kafin nan, za mu yi bita kan yunƙurin da aka yi a baya don inganta wannan fanni da zamanantar dashi, sai taƙaitaccen bayani kan irin albarkatun da Allah yayi wa Najeriya.  Har wa yau, za mu yi ta’aliƙi kan wasu alamomi guda 6 dake nuna raunin kowace ƙasa ne a fannin ci gaba, sannan a ƙarshe mu kawo shawarwarinmu.

Fa’idar Ci Gaba a Fannin Kimiyya da Ƙere-Ƙere

Mai Girma Shugaban Ƙasa, daga cikin dalilan da suka sa shafin Kimiyya da Ƙere-ƙere ganin dacewar gabatar da waɗannan shawarwari na musamman kan  ci gaban wannan ƙasa ba a fannin kimiyyar sadarwar zamani kaɗai ba, har da fannin ƙere-ƙere, waɗanda su ne ginshiƙi wajen ci gaban kowace ƙasa a duniya.  Domin ta hanyarsu ne ƙasa ke iya ciyar da al’ummarta har ma ta fitar da ragowar abin da ta noma zuwa wasu ƙasashe, ta hanyar ci gaba a fannin kimiyya da ƙere-ƙere ne ƙasa za ta iya haɗa kan al’ummarta a siyasance, ta koya musu tarbiyya ingantacciya; ta hanyar gamammiyar tafarkin sadarwa da ingantaccen rumbun bayanai na ƙasa.  Har wa yau, ta hanyar inganta waɗannan fannoni ne hukuma za ta iya samar da kyakkyawar hanyar bayar da ilmi – daga matakin farko har zuwa kololuwa – ga dukkan al’ummarta. Ta hanyar bunƙasa waɗannan fannoni guda biyu hukuma na iya samar wa al’ummar ƙasarta dukkan ababen da suke buƙata a fannin ƙere-ƙere; daga kayayyakin amfanin gida, zuwa ababen hawa irin su jiragen sama, da na ruwa, da motoci, da babura, da kuma kekuna.  A ɗaya bangaren kuma, tana iya amfani da waɗannan fannoni wajen rage yawan sace-sace, da kashe-kashe, da dukkan wasu ayyukan assha a ƙasa.  Samuwa da yiwuwar dukkan waɗannan ababe a ƙasa irin Nijeriya ba wani abu bane mai wahala in Allah ya yarda.  Abin nufi dai, bunƙasar Nijeriya da ci gabanta abu ne mai yiwuwa; ba dole bane ya zama yanzu-yanzu, domin gyara na ɗaukan lokaci.  Barna ce ake iya yinta cikin kankanin lokaci.

A halin yanzu ya kamata mu dubi dukiyar da Allah Ya hore mana na albarkatun ƙasa, sannan mu ɗora ƙasarmu kan wasu ƙa’idoji guda shida da masana harkar kimiyya da ƙere-ƙere a duniya suka yarda cewa sai ƙasa ko al’umma ko daula ta cika su sannan za a iya cewa ta ci gaba a wannan fanni.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.