Sakonnin Masu Karatu (2013) (6)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

59

Assalaamu alaikum Baban Sadik, ko akwai wani bambanci a tsakanin waya nau’in Blackberry Z10 da kuma Samsung Galaxy S4, ta wajen abubuwan da suke dauke da su ko wajen amfani da su ko aikewa da sakonni?  –  Salisu Samaila, Zariya: 08056619781

Wa alaikumus salaam, Malam Salisu barka ka dai. Lallai akwai bambanci kuwa. Domin kamfanonin da suka kera su sun sha bamban, kamar yadda masarrafansu suka sha bamban. Wayar salula nau’in BlackBerry Z10 tana da hanyoyin sadarwa da suka sha bamban da wadanda Samsung Galaxy take dauke dasu. Wayar BlackBerry Z10 na da hanyar sadarwa ta BB Chat, ko BBM, wanda kamar tsarin Intanet yake; wayoyin BlackBerry kadai ke dauke da shi. Ga kuma tsarin gajeren sakonni wato SMS, da dai sauransu. A nata bangaren, Samsung Galaxy na dauke ne da masarrafai masu fahimtar tsarin fuska da idanun mai mu’amala da ita.

Wadannan masarrafai na taimaka wa mai karatu a shafin wayar ne wajen budo shafin da ke tafe, da takaita hasken shafin idan mai karatu ya kawar da fuskarsa, don tanajin makamashin batir. Wadannan kadan ne daga cikin abubuwan da wadannan wayoyi suke dauke da su. Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalaamu alaikum, yaya ibada?  Na ga ka rubuta wayoyin da suka fi shahara ka amfani Z10 da Samsung Galaxy S4, amma ban ji ka ambaci iPod ba, duk da cewa ta fi wadannan tsada.  – Usman Muazu Funtua

Wa alaikumus salaam, Malam Mu’azu barka dai. Ai wadannan da na ambata wayoyin salula ne, amma ita “iPod” ba wayar salula bace, na’urar sauraron sauti ne da taskance hotuna daskararru da masu mtosi. Sai dai in “iPad” kake nufi. Ita ma ba wayar salula bace, na’urar taskance bayanai ne da mu’amala da fasahar Intanet. Wannan shi ne dalilin da yasa ban ambace ta ba. Da fatan ka gamsu.


Salaamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya.  Don Allah wane tsawon lokaci ne batirin wayar salula zai iya dauka yana ajiye bai lalace ba?  Sannan kana iya ajiye shi a cikin na’urar caji na tsawon lokaci don ya cika sosai?  –  Husseini M. Binanchi da Isa Kwafsi Ba Ka Soyayya, Unguwar magajin garin Sakkwato: 08087436699

Wa alaikumus salaam, da fatan kuna cikin koshin lafiya. A gaskiya babu wani lokaci na musamman da aka haddade cewa idan batirin wayar salula ya kai a ajiye ba a amfani da shi zai lalace. Abin da na sani dai shi ne, idan aka yi cajin batiri ya cika, ba a yi amfani da shi ba, to a hankali zai sance, saboda sinadaran da ke cikinsa za su yi rauni, har su zagwanye. Bayan haka, abin da aka fi so shi ne, da zarar batir ya cika a caji, a yi maza a cire shi, domin idan har aka dauke wuta yana like da cajin, muddin a kashe wayar salular take, to cajin na iya zukewa. Sai a kiyaye. Da fatan kun gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.