
Asalin ‘Yan Dandatsa (Hackers) da Alakarsu da Kwayar Cutar Kwamfuta (1)
A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai ne kan kwayoyin cutar kwamfuta da tsarin su da yadda suke yaduwa, da kuma tasirin su. A karshe kuma sai muka kawo nau’ukan wadannan cututtuka da ke damun kwamfuta da hana ta sakewa. A yau idan Allah Ya yarda za mu ci gaba da kwararo bayanai ne ; za mu san su waye ke da alhakin yada ire-iren wadannan kwayoyin cututtuka da kuma irin mummunan abin da suke haifarwa a duniya gaba daya. Za mu san shahararren suna ko lakabin da aka san su dashi a duniyar fasahar sadarwa a yau, da kuma tarihin wannan sana’a tasu mai mummunan sakamako. Idan Allah Ya bamu dama, za mu kawo bayani kan manufar wadannan mutane ; me yasa suke wannan aiki?