Fasahar 5G: Nau’ukan Titunan Sadarwar 5G

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 24 ga watan Yuli, 2020.

118

Cikin dacewar Ubangiji yau muke biki da shagulgulan babbar sallah. Muna rokon Allah ya karbi kyawawan ayyukan da muka gabatar, ya kuma gafarta mana kura-kuranmu. Da fatan za a shagulgulan sallah cikin nishadi da annushuwa. Barkanmu da sallah.
———–
Nau’ukan Titin Sadarwar Fasahar “5G”

Sabanin sauran tsarukan sadarwar wayar salula da suka gabata, daga na zangon farko (1G) zuwa zango na hudu (4G) da ke cin zamaninta har zuwa yau musamman a kasashe masu tasowa, duk titin sadarwa guda daya ne suke amfani dashi, duk da cewa titin na dauke ne kananan hanyoyin sadarwa. Wannan titi, wanda a harshen sadarwar zamani ake kira: “Radio Band”, ko kuma “Band” a takaice, shi ne titin dake kayyake yawan bayanai – na sauti, bidiyo, ko rubutu – dake bin titin daga mai aikawa zuwa mai karba. Yawan bayanan dake bin titin kuma, shi ake kira: “Bandwith”, a tsarin sadarwa ta Intanet.

A galibin kasashen da suka ci gaba a fannin sadarwa da tattalin arziki a duniya, tuni sun dade suna amfani da mafi ingancin tsarin aikawa da sakonni ta siginar rediyo, mai daukan bayanai masu yawa a lokaci guda. Wannan tsari shi ake kira: “Broadband”, wanda har yanzu mu a nan Najeriya, wannan tsari bai gama inganta ba, musamman a karkara. Ingancin wannan tsari na da mahimmanci wajen taimaka mana amfana da dukkan fa’idojin da wannan tsari na Fasahar “5G” ke dauke dashi. In ba haka ba, zai yi wahala mu iya gane bambancin dake tsakarin wadannan marhaloli na sadarwa da ake ta maganarsu tsawon wannan lokaci.

Tsarin fasahar “5G” na dauke ne da tituna guda uku masu mizanin tsarin sadarwa daban-daban, a mataki-mataki. Kuma kowane yana mai cin gashin kansa ne. Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, kowace kasa na iya zaban tsarin da take son aiwatarwa, ba dole sai ta aiwatar da duka ba. Wannan na daga cikin abubuwa muhimmai da suka bambanta tsarin da na sauran marhalolin sadarwar da suka gabata. Ga bayanin kowanne a takaice, don saukake fahimtar masu karatu:

Karamin Titin Sadarwa (Low-Band 5G)

- Adv -

Titin farko da fasahar “5G” ke amfani dashi wajen aiwatar da sadarwa shi ne “Karamin Titi”. Wannan titi shi ake kira: “Low-band 5G” a tsarin sadarwa na zamani. Wannan tsari, ko titi, duk da cewa yana daga cikin sababbin ka’idojin sadarwa na fasahar “5G”, amma da kadan ya dara tsarin sadarwar marhala ta hudu, wato: “4G”, wajen saurin isar da sakonni da kuma yawan bayanan da titin ke aikawa a lokaci guda – cikin kowane dakika, misali. Wannan titi dai yana aika sakonni ko bayanai ne a zangon sadarwa dake mataki na 600 zuwa 700 a zangon sadarwa ta Mega Hetz.

Dangane da abin da ya shafi kadadar sadarwa ko fadin mahallin sadarwa, Karamin Titi na amfani da irin titin marhalar sadarwa na “4G” ne, kamar yadda bayani ya gabata a baya. Kuma ta bangaren yawan bayanan da titin ke iya aikawa ko karban sakonni, shi ma dai iri daya ne ko da kadan ya dara yawan bayanan da tsarin “4G” ke karba ko aikawa, a lokaci guda. Karkashin wannan tsari na fasahar “5G”, masu mu’amala da tsarin na iya aikawa ko karban sakonnin da mizaninsa ya kama daga biliyan 30 zuwa biliyan dari biyu da hamsin (wato: 30MB – 250MB), a cikin kowane dakika guda.

Kenan, idan kana bukatar saukar da bidiyo da mizaninsa ya kai 500MB, a tsarin fasahar “5G” karkashin Karamin titin sadarwa, cikin kasa da dakiku 20 ka gama saukar dashi. Duk da cewa hakan zai dogara ne ga karfin yanayin sadarwar kamfanin wayar da kake amfani da layinsu.

Matsakaicin Titin Sadarwa (Mid-Band 5G)

Wannan shi ne nau’in titin sadarwa na biyu da fasahar “5G” ke gudanuwa a kansu. A fasahar sadarwa na zamani ana kiran wannan titi da suna: “Mid-band 5G”, wato tsarin fasahar “5G” dake gudanuwa a matsakaicin titin sadarwa. Wannan titi na aikawa tare da karban sakonnin bayanai ne a zangon sadarwa dake matakin Giga Hertz 2.5 zuwa 3.7; ya dara matakin Karamin titi da bayaninsa ya gabata a sama. Dangane da abin da ya shafi yawan bayanan da titin ke aikawa ko karba a dukkan dakika guda, Matsakaicin titin a karban sakonnin da mizaninsu ya fara daga biliyan dari daya zuwa biliyan dari tara (wato: 100MB – 900MB).
Matsakaicin titi na gudanuwa ne a kadadar sadarwa mafi fadi da nisa wajen sadarwa. Kuma shi ne tsarin da mafi yawan kasashen duniya ke aiwatarwa daga cikin nau’ukan tsarin fasahar “5G” da ake kokarin dabbakawa a duniyar yau. Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, wannan tsari ne ke matsayin mafi karancin inganci ta la’akari da karfin kudurar sadarwa da fasahar “5G” ke dashi a yadda aka tsara shi. Domin Karamin titi bai da bambanci da tsarin titin sadarwa na marhalar “4G”. Galibin gwajin da kasashe da kamfanonin sadarwar wayar salula da na masana’antu suka yi kan fasahar “5G” duk kan wannan titin ne, wato: “Matsakaicin titin sadarwa” ko “Mid-band 5G”.

Kenan, idan kana bukatar saukar da bidiyo da mizaninsa ya kai 2GB, a tsarin fasahar “5G” karkashin Matsakaicin titin sadarwa, cikin kasa da dakiku 20 shi ma, ka gama saukar dashi. Duk da cewa hakan zai dogara ne ga karfin yanayin sadarwar kamfanin wayar da kake amfani da layinsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.