Matsalolin Wayar Salula (2)

Kashi na 23 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

703

Matsalolin Ruhi

Ruhin wayar salula yana da matukar muhimmanci wajen sadarwa, domin aiki biyu yake gudanarwa; yakan bayar da damar aiwatar da wasu ayyukan wayar salula ko da babu Katin SIM a jikin wayar, sannan yana hada alaka tsakanin wayar da yanayin sadarwar kamfanin waya, wato Network Service kenan.  Wannan tasa duk abin da ya shiga tsakanin ruhin wayar da wayar, to za a samu matsala mai girma.  Wannan ke sa wayar ta yi gajeren suma (wato ta sandare, a kasa sarrafa ta na wani dan lokaci), ko dogon suma (wato Hanging kenan, a turancin sadarwar zamani). Idan waya ta fada cikin ruwa, har ta jima a ciki, tana iya sumewa.  Amma idan aka shanya ta a rana za ta farfado – musamman idan Nokia ce.  Bayan haka, daga cikin dalilan da ke haddasa dogon suma ko gajeren suma akwai shigan kwayoyin cuta a cikin ruhin wayar.

Wadannan kwayoyin cuta da a baya muka kira su da suna Virus, suna samun kafar shiga ruhin wayar ne sanadiyyar aiwatar da sadarwa.  Ko dai wajen shigar da bayanai ta amfani da fasahar Bluetooth, ko fasahar Infra-red, ko kuma wayar shigar da bayanai na USB, ko kuma sanadiyyar gidan yanar sadarwa da mutum ya shiga ta Intanet mai dauke da wadannan kwayoyin cuta, ko kuma wasu bayanai da ka debo daga Intanet masu wadannan matsaloli.  Idan waya ta kamu da matsala irin wannan, ya zama ba ta iya tabbata kan hali daya; ma’ana, ta kan kashe kanta, ko ta rika sumewa na tsawon lokaci, ko taki yarda a shigar mata da bayanai kowane iri ne, to dole ne a kai ta wajen mai gyara.

Akwai yanayin da zai sa a mata wankin kwakwalwa ta hanyar goge wadannan kwayoyin cuta.  Amma idan sun ci karfinta fiye da kima, to sai dai a goge ruhin gaba daya ta amfani da tsarin da ake kira Phone Flashing.  Idan haka ta faru, to, duk wasu bayanai da ke cikin wayar za su goge, za ta koma kamar yadda aka siyo ta ne a asali.

Wasu matsalolin ruhin kuma kan faru ne sanadiyyar dangwale-dangwale da matse-matsenmu mara ma’ana.  Ko kuma mu bar wa yara kana suna ta wasa da ita.  Sadda za su latsa wani maballi mai hadari, ba za mu sani ba balle mu san yadda za mu gyara.  Idan ka sayi sabuwar waya yana da kyau ka karanci kundin da ta zo da shi.  Idan ba ka iya karatun turanci ba, ka nemi wanda ya san waya ya nuna maka amfanin dukkan bangarorinta.  Don kada kaje ka matsa abin da zai jawo maka jidali da kashe kudi wajen mai gyara.

Matsalolin Yanayin Sadarwa

- Adv -

Daga cikin dalilan da ke haddasa matsaloli ga wayoyin salula akwai yanayin sadarwar kamfanin waya, wato Network Service.  Wasu daga cikinsu matsalolin wucin-gadi ne; bayan wasu ‘yan lokuta za su gyaru.  Kamar matsalolin da ke da alaka da rashin yanayin kira mai inganci, ko rashin iya aikawa da sakonnin tes, ko daukewan yanayin sadarwar ma gaba daya (wato Network Outage ko Network Fluctuation).  Dukkan wadannan sukan daidaitu bayan wasu awanni ko mintuna.  Bayan haka, sun danganci inda kake ne.  Yanayin sadarwa galibi sun fi inganci a cikin manyan birane. Sannan idan akwai hargitsi a tsakanin jama’a sanadiyyar fadace-fadace da ake yi, kamfanonin waya sukan yanke yanayin sadarwa a bangaren da ake wannan tashin hankali.

A daya bangaren kuma, wayarka na iya shiga yanayin Call Divert, ko Call Barring, ko kuma Voice Mail, sanadiyyar tsokale-tsokalenka ko danne-danne mara ma’ana.  Idan wayarka ta shiga irin wannan yanayi ba za ka iya karban kira ba, ko yin kira, ko kuma aiwatar da wasu nau’ukan ayyukan waya, dole sai ka fitar da ita daga yanayin da ta shiga. Abin zai fi muni idan baka san yadda aka yi ka matsa abin da ya shigar da ita cikin wannan yanayi ba.  Wadannan matsaloli duk suna da alaka ne da tsarin sadarwar kamfanin waya.  Sai mu kiyaye.  Domin idan matsala ta faru ba kowa zai iya magance maka irin wannan matsala ba.

Haka wasu lokuta idan ka zo shigar da lambobin katin caji na MTN, ya ki shiga, idan ka maimaita har sau uku, to suna iya kulle katin wayar daga inda suke.  Wannan zai sa wayar ta kasa sarrafuwa har sai ka shigar da lambobin PUK, wadanda ke rubuce a jikin katin wayar da ka saya.  Galibi da zarar mun sayi sabon layi sai mu jefar da kwalin da kwarangwal dinsa.  Wannan kuskure ne, domin akwai bayanai masu fa’ida a jikin kwalin katin da ka siyo.  Dole ne mu rika karantawa.  Idan ba mu iya karatu ba, mu adana kwalin, akwai ranarsa. To amma matsalarmu ita ce, Bahaushe bai cika son karatu ba. Kamar yadda Marigayi Mudi Sipikin ke cewa: “Bahaushe dan saurare ne.”  Shi dai ka bashi labari kawai.  Wannan tasa yawan masu sauraron rediyo suka fi yawa a cikinmu.  Dole ne mu rika caza kwakwalwa da karatu. Babu abin da ke raya zuciya da kwakwalwa, ya kimtsa mutum, ya kuma kara masa fahimta da hangen nesa irin karatu.

Shawarwari

Wadannan kadan ne daga cikin nau’ukan matsalolin da wayar salula ke fuskanta.  Sai dai shawara a nan ita ce, duk sadda ka fuskanci akwai matsala da wayarka, kuma ka kasa gano inda matsalar take ko musabbabinta, abin da ya fi muhimmanci shi ne ka kai wa mai gyara ya duba maka ita.  Sannan yana da kyau mu san cewa masu gyaran wayar salula suna suka tara; akwai kwararru na tsakani da Allah, sannan akwai na bogi, wadanda ba wai koyon gyaran suka je suka yi, tsaban tsokane-tsokane da bige-bige ne kawai suka mayar da su masu gyaran. Maimakon su gyara maka, sai su bata maka.

Bayan haka, akwai wayoyin salulan da ba a samun bangarorinsu a kasuwa balle a saya a gyara su.  Ire-iren wadannan wayoyi sun hada da nau’ukan wayoyin da ake kawo su daga kasar Sin, wato China.  Galibinsu ba kowane mai gyara bane ya iya gyara su.  Don haka, idan kana da waya irin wannan ta samu matsala, wasu lokuta sayan sabuwa shi yafi alheri, in kuwa ba haka ba sai ka narkar da kudadenka wajen gyara amma bata gyaru ba.  Sai a kiyaye.  Wadannan su ne kadan cikin shawarwarin da zan iya bayarwa.

A karshe dai, Baban Sadiq ba ya gyaran waya. Don haka idan wayarka ta samu matsala, a yi kokarin garzayawa wajen masu gyara, kamar yadda bayanai suka gabata.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.