Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (5)

Wannan shi ne kashi na karshe, ko ince inda za mu dakata a halin yanzu. Ina sa ran nan gaba zan ci gaba da bincike a wannan fanni, don samar da gamewa. Da fatan masu karatu sun amfana.

403

Matashiya

Na tabbata kamar sauran makonnin baya, masu karatu na tare damu cikin wannan silsila da muka faro kan abin da ya shafi alakar da ke tsakanin tabbatattun nau’ukan ilmin kimiyya da ke cikin Kur’ani mai girma da kuma sakamakon binciken da malaman kimiyyar zamani ke fitarwa lokaci-lokaci, masu kuma alaka ta dacewa da abin da Allah Ya fada a Kur’ani.  A makon da ya gabata mun kawo bayanai kan abin da ya shafi kimiyyar halittu da yadda rayuwa ke samuwa a cikin mahaifa a tsarin karantarwar Kur’ani, da kuma tabbacin hakan daga sanannu kuma shahararrun malaman kimiyyar wannan fanni, irinsu Farfesa More da sauransu.  A yau za mu ci gaba, inda za mu kawo tabbaci na karshe kan abin da ya shafi kimiyyar karkashin teku da Allah Ya halitta, ya kuma sanar damu kadan cikin sirrin da ke karkashin kasan tekun; ba wai na halittu ba, a a, na duhun da ke karkashin teku kadai.  Sirrin da ke cikin teku na da dimbin yawa, don haka daya kawai za mu tabo, shi ne zurfin da ke karkashinsa, da kuma cewa akwai duhu mai tsakanin gaske, wanda ke karuwa, iya karuwar zurfin tekun.

Kamar kullum, kada mai karatu ya gafala da cewa Al-Kur’anin nan asalinsa (bai gushe ba kuma bazai gushe ba kan cewa) littafi ne  na shiriya, ba wai zuwa yayi don karantar da ilmin kimiyya da fasaha ba.  Duk abin da ke ciki na nau’ukan ilmin, ya samu ne sanadiyyar karantar da mu ikonsa da kuma cancantarsa da bauta, ba wai mu barshi mu je muna bautar  wani abu daban, halitacce ba.  A takaice dai, dukkan wani ilmi da ke Kur’ani, indai ba don shiriya aka dauke shi ba, to riban-kafa ne kawai.  Mu tsayu a kan haka; domin hakan ne zai kaimu ga gaci, mu samu shiriya, sannan mu amfana da abin da ke tattare da wa’azin shiriyar na amfanin rayuwar duniya.  Abdullahi dan Abbass na cewa: “Duk wanda ke son duniya, to na umarce shi da ya rike Kur’ani.  Haka duk wanda ke son lahira, shi ma na ina umartansa da ya rike Kur’ani.  Wanda kuma ke son duniyar da lahirar baki dayansu, to shi ma ina umartansa da ya rike Kur’ani.” Don haka za mu ci gaba.


KIMIYYAR KARKASHIN TEKU

———————————————————————-

Akwai Duhu a Karkashin Teku

Farfesa Durga Rao, wani shahararren masani ne, kwararre kan ilmin halittu da tsarin rayuwa a karkashin teku, wato Marine Geologist, kuma Farfesa ne a Jami’ar Sarki Abdul-Aziz da ke Jidda, a kasar Saudiyya. Ba musulmi bane.  Wata rana an dunfare shi da wannan aya da ke cikin Suratun Noor, inda Allah ke cewa:

“Ko kuwa kamar duffai ne a cikin teku mai zurfi, taguwar ruwa tana rufe da shi, daga saman sa akwai wata taguwa, daga saman sa akwai wani girgije; duffai, sashensu a bisa sashe, idan ya fitar da tafin (hannun) sa ba ya kusa da ya ganshi.  Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to ba ya da wani haske.” (Noor: 40)

Kafin mu kawo ra’ayi ko jawabin da Farfesa Rao ya bayar kan alakar wannan aya da abin da ya sani na ilmin karkashin teku, yana da kyau mu fahimci cewa wannan aya an kawo ta ne ciko ga wani misali da Allah ya fara kawowa a ayar da ta gabace ta, inda yake siffata halin da kafirai suke ciki na bata, sanadiyyar kauce wa shiriya da suka yi.  Ga ayar farko nan, don mu fahimci tsarin abin da kyau:

“Kuma wadanda suka kafirta, aiyukan su kawalwalniya ne a fako, (wanda) mai kishirwa yana zatonsa ruwa ne, har sai da ya je inda (kawalwalniyan) yake, bai iske komai ba; kuma ya sami Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisabinsa.  Kuma Allah Mai gaggawar sakamako ne.” (Noor: 39)

Kenan Allah na mana misali ne tsakanin duhun da ke karkashin teku, da wanda kafirai ke ciki. Da aka samu Farfesa Rao kan alakar da ke tsakanin wannan aya da abin da ya karanta kuma yake karantarwa, sai yace tun tsawon zamani malaman kimiyya basu taba sanin cewa akwai duhu a karkashin teku ba, sai bayan samuwar na’urorin bincike na kimiyyar zamani.  Yace ba mamaki idan aka yi la’akari da cewa masu yin ninkaya ko nutso cikin teku basu iya tafiya kasa iya zurfin mita ashirin zuwa talatin sai da taimakon kayan ninkaya irin na zamani.  Amma da za a barsu a haka, duk kwarewarsu wajen ninkaya basu iya wuce wannan tazara.  Yace kuma hatta da taimakon kayan ninkar ma, ba wanda zai iya rayuwa a iya tazaran zurfin da ya kai mita dari biyu (200 metres).  Wannan kuwa ya faru ne sanadiyyar tsananin duhun da ke karkashin tekun.  Iya zurfin tafiya, iya kaurin duhun da mai ninkaya zai rika cin karo dashi.  Hakan na samuwa ne a manyan tekuna masu tsananin zurfi da ke duniya, amma ba ‘yan gijari-gijari ba.  Domin ko a Kur’ani ma “teku mai zurfi” aka ce.  To me yasa?

A cikin littafinsu mai suna Oceans, shafi na 27, marubuta Elder da Pernetta sun nuna cewa wannan duhu da ke karkashin teku na samuwa ne sanadiyyar manyan dalilai guda biyu.  Dalili na farko shi ne samuwar haske da ke darsuwa a saman teku.  Wannan haske, a cewarsu, yana dauke ne da launuka ko kaloli guda bakwai.  Wadannan launuka ne a turance ake kira ROYGVIB: wato launin bakan-gizo, sune: launin ja (red), da launin ruwan lemo (orange), da launin rawaya (yellow), da launin kore (green), da launin shudi (blue), sai kuma sauran launuka biyu da ke samuwa sanadiyyar hada wasu cikn wadanda suka gabata, wato launin Indigo, da kuma Violet.  Wadannan su ne launukan da ke cikin kowane irin haske da ke samuwa a sararin wannan duniya tamu.  Duk sanda haske ya haska saman teku, ya kan zarce ne zuwa can karkashi.  A hanyarsa ta tafiya, ruwan tekun na hadiye wadannan launuka a mataki daban-daban na zurfi, har a kai ga inda babu wani abin da ya rage na launin da ke hasken balle ya haskaka; ba abin da zai rage sai tsananin duhu mai firgitarwa.  Ga yadda abin yake nan.

Mawallafan wannan littafi suka ce idan hasken ya shige cikin teku da zurfin mita goma zuwa goma shabiyar, tekun na hadiye launin ja da ke tattare da hasken ne. Launin ja bazai wuce wannan tazarar ba.  Don haka idan mai ninkaya cikin teku ya kai zurfin mita ashirin da biyar (25 metres), kuma aka samu matsala yayi rauni, ko kadan bazai ga jinin da ke fita daga jikinsa ba.  Domin sinadaran da ke samar da launin a cikin hasken da ke haska masa hanyar tafiyarsa basa nan, zurfin teku ya hadiye su.  Duk wani teku da zurfinsa ya wuce mita ashirin ya kai ashirin da biyar, launin ja bazai kai labari ba a wannan tazarar.  Haka sauran launukan zasu ci gaba da bacewa a yayin da mai ninkaya ke dada yin kasa.  Misali, idan ya kai zurfin mita hamsin, launin ruwan lemo zai bace; duk wani abu mai wannan launin da ke tare dashi za a daina ganinsa a wannan tazarar.  Haka idan ya kai tsakanin mita hamsin zuwa dari, duk wani abu mai launin rayawa zai bace; a daina ganinsa a wannan tazarar.  Idan kuwa ya kai tazarar mita dari biyu zuwa sama, to duk sauran launukan zasu bace, tasirin zurfin teku zai hadiye su, a daina ganin duk wani abu mai launinsu.  Haka abin yake; a duk tazarar zurfi, akwai launin da ke bacewa ko teku ke hadiye shi, har idan aka wuce zurfin mita dari biyu, to babu abin da za a iya gani sai duhu.  Don me?

- Adv -

Saboda daman hasken da zai haska wa mai ninkaya yana tinkaho ne da wadancan launuka guda bakwai masu tabbatar masa da tasirinsa.  Da zarar zurfi da tasirin teku ya hadiye su, sai haske ya bace.  In banda duhu babu abin da za a gani.  Wadannan mawallafa suka ce, a tazarar zurfin mita dubu daya babu komai sai tabbataccen duhu mai firgitarwa.  Wannan, a cewar wadannan malamai, shi ne dalilin farko na samuwar duhu a karkashin teku.

Dalili na biyu kuma suka ce yana samuwa ne sanadiyyar girgije da ke tare hasken rana a saman teku, ya warwatsa hasken a karkashinsa.  Wannan warwatsawa da yake yi, yana tasiri sosai wajen haddasa matakin farko na duhu ga teku.  Domin galibin launukan da ke cikin hasken ranar zasu bace ne.  Don haka da zarar hasken ya iso saman teku, sai ya haska taguwar ruwa da ke shawagi a saman tekun, ta hanyar samar da haske mai kyalli na wucin-gadi.  Bangaren hasken da bai samu sauka a saman taguwar ruwa da ke saman tekun ba kuma, sai ya zarce karkashin teku, inda a hankali tasirinsa ke bacewa, kamar yadda bayani ya gabata a dalilin farko.  Wannan haske mai kyalli da taguwar ruwa ke cafkewa a saman teku, shi ke haddasa dumi ko zafi a saman ruwan.  Shi yasa Malaman kimiyyar karkashin teku suka ce ruwan da ke cikin kowane teku ya kasu kashi biyu ne; akwai wanda ke sama, mai tattare da taguwar ruwa (ko igiyar ruwa, wato Ocean Waves, a turance), wanda kuma ke tattare da haske mai kyalli sanadiyyar hasken rana da ke haska shi, ya sa yayi dumi.  Da kuma bangare na biyu, wanda ke can karkashin tekun, mai tattare da tsananin duhu mara misaltuwa.

Wannan tsananin duhu ke haddasa nauyin mizanin ruwan da ke can karkashi, idan aka kwatanta shi da wanda ke saman tekun, mai shawagi cikin kadawar taguwar ruwa da ke kai-komo dashi daga gaba zuwa gaba.  Domin hatta kifayen da ke karkashin teku basu gani da idanunsu, saboda tsananin duhu.  Abin da ke sa su ga juna kawai shi ne kyallin da ke jikinsa na halitta.  Don haka abin da ke rarrabe ruwan saman teku da wanda ke karkashi kuma ita ce wannan taguwa mai kadawa.

A karshe idan muka duba sai mu ga cewa wannan duhu da ke karkashin teku yana rayuwa ne a kasan shamaki guda biyu.  Na farko shi ne wannan girgije da ke sama mai tare hasken rana ta hanyar hadiye masa launukansa, da kuma warwatsa shi.  Na biyu kuma wadannan taguwar ruwa masu kame dan hasken da ya karaso saman tekun.  Wanda kuma ya ci nasarar shigewa, sai tasirin zurfi yayi ajalinsa.  Allah Buwayi gagara-misali!  Wannan yayi daidai da fadin Allah kuwa, inda yake cewa:

“Ko kuwa kamar duffai ne a cikin teku mai zurfi, taguwar ruwa tana rufe da shi, daga saman sa akwai wata taguwa, daga saman sa akwai wani girgije; duffai, sashensu a bisa sashe, idan ya fitar da tafin (hannun) sa ba ya kusa da ya ganshi.  ..” (Noor: 40)

Bayan gama bayaninsa kan wadannan ayoyi, sai Farfesa Rao ya kammala da cewa:

“Shekaru 1400 da suka shige babu wani mahaluki da zai iya yin cikakken bayanin wannan tsari kamar yadda ake yi yanzu.  Wannan ke nuna cewa lallai wadannan bayanai (ko ayoyi) sun zo ne daga wata makwafa da ta sha karfin tunanin dan Adam.”

Kammalawa

A tabbace yake cewa lallai binciken Malama kimiyyar zamani kan wannan duniya tamu gaba daya da ma sauran wadanda ke makwabtaka damu, sau tari sakamakonsu kan dace da abin da Allah ya fada a cikin Kur’ani mai girma.  Idan kuwa kaga an samu bambanci, to ko dai bincikensu ne yake da nakasa ko kuma basu bi ka’idojin da suka kamata ba.  Domin kuwa muddin za a bincika, to sai an samu dacewa.  A nan za mu dakata da wannan silsila kuma, sai wani makon mu kutsa wani fannin daban.  A ci gaba da kasancewa damu.


SABUWAR MUDAWWANA

Ta la’akari da yadda kasidu ke kara yawa kan sauran fannonin Kimiyya da Fasaha, irinsu ilmin kimiyyar teku da sararin samaniya da sauransu, na ga dacewar samar da wata Mudawwana (Blog) ta musamman don ci gaba da adana kasidun da suka shafi wannan fanni na musamman.  Wancan Mudawwanar kuma, mai taken “Makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa” da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com, mun ajiye ta don zuba kasidun da suka shafi Fasahar Intanet da Kwamfuta da kuma Wayar Salula.  Wannan sabuwar Mudawwana wacce na sanya wa taken “Zauren Kimiyya da Fasaha”, za a same ta a wannan adireshin: http://kimiyya.blogspot.com, daga ranar asabar mai zuwa in Allah Ya yarda.

Dalili na biyu da yasa nayi hakan kuwa shi ne don ganin yadda masu karatu suka kasu kashi biyu, dangane da yanayin sakonnin da nake samu a duk mako; wasu hankalinsu na kan Fasahar Intanet da Wayar Salula da Kwamfuta, wasu kuma hankalinsu na kan Ilmin Sararin Samaniya, da Kimiyyar Halittu da dai sauransu.  Don haka wannan zai ba kowane janibi damar mallakar kasidu cikin sauki, ba sai ya sha wahalar nema ba a Mudawwana daya.

Da fatan za a yi hakuri da wannan sauyi da aka samu kwatsam. Kada kuma a mance, duk wanda ke son kasida kan abin da ya shafi Wayar Salula da tsarin hada ta da Intanet, adireshin Imel zai aiko ba sakon text ba.  Ko kuma a je Mudawwana don samun kasidar cikin sauki. In kuwa ba haka ba, to sai dai ayi hakuri.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.