Hanyoyin Kwarewa a Fannin Fasahar Sadarwa (2)

Wannan kashi na biyu kenan cikin fadakarwar da muka faro a makon jiya kan hanyoyin da mai karatu zai iya kwarewa a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani. A yau mun dubi abubuwan da za su iya taimaka wa mutum ne wajen cin ma nasara a wannan hanya.

455

Sindaran Kwarewa

A tabbace yake cewa duk wanda ka ga yayi fice a wani fanni na rayuwa, to alal hakika ba haka kawai ya samu wannan martaba ba, sai da ya rasa wasu abubuwa da yake tsananin so, sannan ya samu.  Don haka, duk wanda ke son kwarewa a fanni musamman na ilimin fasahar sadarwa na zamani, yana bukatar wasu sinadarai na rayuwa, wadanda za su taimaka masa wajen yin hakan. Yana kuma da kyau ya san cewa, iya gwargwadon himmar sa wajen bin wadannan dokoki na rayuwa, iya gwargwadon kwarewarsa.  Ga wasu daga cikin halayen da muke bukatar dabi’antuwa da su, don cin nasara a kowane fanni ne muka dauka:

Sha’awa

Wannan shi ne babban garkuwa da mai karatu yake bukata.  Sha’awar da nake nufi a nan ita ce abin da ake kira “Interest”, a turance.  Ya zama kana son yin abin, kuma kana kulawa da irin ci gaban da kake samu lokaci lokaci.  Domin idan baka da sha’awa, to babu yadda za a yi ka rinka kulawa.  Kada ka damu cewa “ai ban taba mu’amala da kwamfuta ba”, duk wannan ba hujja bane.  Idan kana da cikakkiyar sha’awa, nan da nan za ka koya.  Shekaru shida da suka gabata ko kusa da kwamfuta bana yi, saboda tsaban tsoro.  A kullum gani nake kamar idan na taba jikin kwamfutar, lalata ta zan yi.  Na fara gina sha’awa na ne lokacin da nake ta mu’amala da gidajen rediyon BBC da Deuschewelle dake Jamus, da irin su Voice of America.  Nakan ji suna ambaton adireshin Imel dinsu, ni kuma ba a abin da na fi bukata a rayuwa illa in aika da sako, ya isa cikin gaggawa.

Don haka wata rana sai na rubuta sako zuwa ga BBC Sashen Turanci (The Learning Zone), na samu wata baiwar Allah da ke sashin kwamfuta a ofishinmu ta aika musu.  Sai ta dinga min yanga.  Har sai da na harzuka.  Daga lokacin na yanke shawaran koyan kwamfuta da shiga Intanet.  Ba a dauki lokaci mai tsawo ba Allah Yai mani muwafaka.  A yanzu ba na iya kwana ba tare da nayi shaukin taba kwamfuta ko shiga Intanet ba.  Ya zama kamar jinin jiki na.  duk wannan ba komai ya kawo haka ba, sai tsaban sha’awa da nake dashi kan hakan.  Ban taba zuwa makaranta don koyon ilimi da aiki da kwamfuta ba, balle yadda ake mu’amala da Intanet.  Don haka, idan mai karatu ya gina sha’awarsa kan fannin da yake sha’awa, ina tabbatar masa cewa nan ba da jimawa ba zai samu bakin zaren.

Karatu da Aiki Da Shi

Abin da ilimin kwamfuta da Fasahar Intanet ke bukata bayan sha’awa, shi ne aiki da abin da ka karanta.  Domin idan baka aikata abubuwan da kake karantawa, to zai yi wahala ka iya komai a harkan.  Domin shi wani fanni ne wanda karantunsa ke rataye da aiki.  A wasu lokuta ma za ka samu aikin ya fi karatun yawa.  Babu abin da za ka koya a harkan Kwamfuta da Intanet ba tare da kayi karatu ba; kuma baka iya komai, idan baka kwatanta abin da ka karanta ba.  Don dole ne mai karatu ya rinka kwatanta ilmummukan da yake koyo.  Wannan ne zai bashi daman auna ilminsa kan abin da yake karantawa.  Duk inda ya cije, sai yayi tambaya.  Wannan tasa nake zaburar damu kan abin da ya shafi neman bayani cikin dukkan abin da mai karatu ya karanta amma bai fahimta ba.  Ko ya koya, amma da yaje aikatawa sai bai samu natija ba.   Yin tambaya ne kadai zai wayar maka da kai cikin abin da kake nema.

Galibin abubuwan da na tara na ilimi da aiki kan wannan fasaha, sun ta’allaka da tambayoyin da nake yi ne kusan a kullum.  Idan abubuwa suka cakude mini, na kan aika wa Farfesa Abdallah Uba Adamu dake Jami’ar Bayero sakon Imel, don neman Karin bayani.  Wasu lokuta kuma sai in nemi bayani (Search) ta hanyar Matambayi Ba Ya Bata, wato Search Engine. Don haka, mai karatu yasa a ransa cewa dole ne ya aikata abin da ya koya, kuma duk inda ya samu matsala, to yayi tambaya.  Domin matambayi, inji Hausawa, baya bata – sai dai in bai yi tambayar daidai ba, ko kuma yadda ta dace.

- Adv -

Manufa

Wannan ya kawo mu kan mataki na gaba, wato manufa.  Kafin nan, yana da kyau mai karatu ya san cewa, yadda zuwansa duniya ke da manufa mai karfi,  to haka abin yake a bangaren koyo da kwarewa na ilimin fasahar sadarwa, sai ya riki manufa kwakkwara, idan kuwa ba haka ba, sai ya bace.  Wannan ya faru ne saboda duniyar Intanet wata irin duniya ce mara badala; babu kyaure, muddin a ciki kake.  Kuma yadda kasashen duniya suka kasu kashi-kashi, to haka manufofi da ra’ayoyin mutane suke birjik.  A fage irin wannan, idan baka da manufa, sai ka narke cikin rubibi.  Samun manufa ya kasu kashi-kashi;  manufa wajen lilo da tsallake-tsallake.  Wani irin gidan yanan sadarwa za ka ziyarta?  Me kake bukata a ciki wajen kwarewa?  Duk sai ka tantance.

Kafin in karkare wannan bangare, yana da kyau mai karatu ya san cewa yadda dabi’un mutane suka karkasu a rayuwar yau da kullum, to haka ire-iren wadannan dabi’u suke a duniyar Intanet.  Idan addini kake so akwai.  Idan holewa kake so, akwai mazauninta.  Idan neman kudi kake son yi, ta hanyar da ta dace da wacce bata dace ba, duk akwai su.  Duk irin abin da kake bukata na dabi’u, baza ka rasa mazauni ba.   Don haka nake karfafa Magana kan manufa.  Me kaje yi?

Hakuri da Juriya

Komai dan hakuri ne, musamman idan aka ce ya shafi neman ilmi da aiki da shi.    Hakuri ya kasu kashi biyu a Intanet; juriya wajen kamewa daga aikata alfasha.  Da kuma juriya wajen dagewa da ganin ka koyi abin da zai amfaneka.  Ba za ka san dimbin ilimin da ke makare a giza-gizan sadarwa ta Intanet ba sai ka fara shawagi a wannan fage.  Kowane irin ilimi kake son koyo, za ka iya samunsa in Allah Ya yarda.  Abin da kake bukata kawai shi ne sanin abin da kake nema, da kuma inda za ka je ka sameshi.  Hakurin da ya fi kowanne shi ne wanda za ka yi wajen koyon ilimi; ilimin kwamfuta da Fasahar Intanet nake nufi.  Domin wani fanni ne dake tsarinsa ke sauyawa kusan a dukkan dakika ko bugun agogo.  Yana bukatar a kullum ka rinka mu’amala da shi don sanin irin sauye-sauyen da ke samuwa a kullum. Idan ba haka ba sai ka zama bakauye cikin kankanin lokaci.  Domin ana kirkiro sabbin hanyoyin mu’amala da wannan fasaha ne kusan a kullum.

Wannan yasa dole mai karatu ya zama mai juriya da hakuri wajen lazimta da mu’amala da kowane irin bangare ne ya kallafa ma kansa koyo.  Idan hakan ya zama maka jiki, ba zai rinka damunka ba, in Allah Ya yarda.

Kammalawa

Dangane da bayanan da suka gabata, na tabbata mai karatu ya dauki mataki kan tsarin da zai bi wajen daukan fannin da yake son kwarewa a kai.  Idan haka ya samu, to an yi mai wuyan, duk saura masu sauki ne.  A mako mai zuwa, za mu fara kwararo bayanai kan wadannan fannoni, filla-filla, daya na bin daya, insha’Allah.  Za mu fara ne da gamammen ilimin kwamfuta, wato Computer Science and Education, har mu kai karshe.  Don haka sai a zage damtse wajen sauraro irin na fahimta, don samun karuwa.  Duk abin da ba a fahimta ba kuma a rubuto, don neman Karin bayani.  Ina kuma mika gaisuwata ga dukkan masu karatu.  Sai wani makon.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.