Fasahar 5G: Fa’idojin Fasahar 5G

An buga wannan makala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 3 ga watan YuLi, 2020.

259

Fa’idojin Fasahar “5G”

Mai karatu na iya hasashen dimbin fa’idar da za a iya samu karkashin wannan tsarin sadarwa na biyar mai suna: “5G”, musamman a fannonin rayuwa masu mahimmanci wajen inganta rayuwa da kuma ci gaban al’umma ta bangarori daban-daban. Sai dai kamar yadda na sanar ne a makon jiya, cewa, kasancewar wannan tsari bai kankama ba a wannan kasa da nahiya tamu, kuma ga wanda bai san cin gaban da ake kan samu ba wannan fanni na sadarwa a duniya, bayanan da za su zo kan fa’idar wannan fasaha na iya sa muga kamar almara ne abin, ko kuma wani buri da a tunani ne kawai dan adam ke iya hararo shi, amma babu tabbas a tare dashi. Tunani irin wannan ba abin mamaki bane idan mutumin dake Afirka kuma yake da karancin fahimta kan ci gaban tsarin sadarwar zamani ya ayyana shi a zuciyarsa ko ma ya furta shi. Domin ire-iren wadannan ci gaba da ake dasu a sauran kasashen, ko rabinsu ba mu dashi a nan kasar ko nahiyar tamu. Amma tabbacin da zan iya baiwa mai karatu shi ne, abubuwa ne da suke da hakika, kuma muddin aka samar da mahallin da za su iya gudanuwa a al’adance, to, za mu gansu a aikace. Kadan daga cikin wadannan fa’doji dai sun hada da:

Ingantaccen Tsarin Sadarwa

Fasahar “5G” na dauke ne da ingantaccen tsarin sadarwa na zamani, wanda ke dauke da siffofin da bayaninsu ya gabata a makon jiya. Fa’idar hakan kuwa a fili yake. Harkokin sadarwa ta fannin yada labaru da kasuwanci da tattalin arzikin kasa da zamantakewa zasu kankama. Za a samu karancin matsaloli wajen tasarrafin rayuwa, iya gwargwadon yadda hukuma da kafafen sadarwar wayar tarho da Intanet suka karbi wannan tsari da kuma habbaka shi yadda ya kamata. Na farko wajen amfanuwa da wannan tsari su ne kafafen yada labaru na talabijin da rediyo. Karkashin tsarin “5G”, a yanzu kamfanonin sadarwar talabijin na tauraron dan adam (Satellite TV Channels) na tunanin amfani da tsarin “5G” ne wajen isar da hotunan bidiyo zuwa akwatin talabijin mutane a ko ina suke, domin wannan tsarin ya fi isar da sako mai inganci, cikin lokaci ba tare da tsaiko ba, kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya. Kafafen sadarwa na rediyo su ma suna iya amfani da tsarin wajen yada shirye-shirye babu tangarda. Haka kafafen jaridu su ma, suna iya shiryawa da tattaro bayanai daga masu farauto musu labarai zuwa dakin tace labarai cikin sauki da inganci.

Habakan Tattalin Arzikin Kasa

- Adv -

Duk da cewa ingancin tattalin arzikin kasa da tabbatuwarsa abu ne da ya ta’allaka da dalilai masu dimbin yawa, sai dai tsarin sadarwar zamani na daga cikin manyan dalilai. Misali, kafin bayyanar sabon tsarin GSM a Najeriya a shekarar 2000, layuka tarho a Najeriya duk basu shige dubu dari biyar ba. Sannan hukuma daya ce kadai ke samar da wannan dama ta sanarwa, ita ce Hukumar Sadarwa ta Kasa (National Communication Commission – NCC). Amma daga sadda aka bai wa kamfanonin sadarwa lasisi zuwa yanzu, ana da layukan wayar salula yanzu a Najeriya sama da miliyan 160. Kamfanin MTN kadai na da layuka sun kai miliyan 60, tsakanin masu rai da marasa rai! Harkokin kasuwanci sun karu, sannan sun inganta. Hanyoyin kasuwanci sun sawwaka. Kana cikin gidanka sai ka sayar da hajarka. Sannan fasahar Intanet, wanda kafin wancan lokaci sai wane da wane, a yanzu ta zama kamar kyauta – ta la’akari da yadda take a lokutan baya. Jama’a da dama sun samu ayyukan yi – daga masu sayar da wayar salul, zuwa masu sayar da katin waya, da masu dillacin na’urorin sadarwa, da kudaden shiga da hukuma ke samu a duk shekara idan kamfanonin wayar salula sun sabunta lasisin da aka basu, zuwa ma’akatan da suke dauka – injiniyoyi, leburori, masu gida, masu talla da dai sauransu. Abin da zai biyo bayan dabbaka tsarin fasahar “5G” kuma nan gaba, Allah ne kadai ya san Karin fa’idar da za a samu. Sai dai muyi hasashe.

Inganta Fannin Kiwon Lafiya

Duk da cewa muna da kalubale a fannin kiwon lafiya a kusan dukkan kasashe masu tasowa, musamman nan nahiyar Afirka, sai dai kuma, daga cikin dalilan da za su taimaka wajen inganta wannan fanni akwai samuwar sabuwar fasahar “5G”. Kamar yadda nasha fada a wannan shafi mai albarka, fannin sadarwa na zamani yana da alaka da kowane fannin rayuwa – daga addini har zuwa sharan bola. Duk wani abin da kake yinsa shekaru 50 da suka wuce a kalla, muddin har yanzu yana nan, to, sai ka samu sabon hanyar inganta shi a fannin sadarwa ta zamani. Shi yasa, fannin kiwon lafiya a yanzu yana dogaro ne da tsarin sadarwa na zamani. Na’urorin da ake amfani dasu a asibitoci yanzu duk ana iya jona su da kwamfuta, da wayar salula, sannan su aiwatar da sadarwa da fasahar Intanet. Misali, asibitin da nake zuwa a nan Abuja, daga sadda ka isa wajen karban kati, aka maka rajista aka baka sabon kati, to, ka daina ta’ammali da wata takarda ta Zahiri. Komai ya koma kwamfuta. Ta hanyar kwamfuta za a aika sunanka wajen masu duba dumin jikinka kafin ganin likita. Suna gamawa za su aika sunka zuwa kwamfutar likitan da zai duba ka, su sanar dakai dakin da yake. Kana zaune zai kira sunanka. Da zarar ka shiga, kwamfuta zai budo ya tambayeka lambar katinka. Da zarar ya budo shafinka zai fara dubawa yaga ko a baya ka taba ganin likita a nan. Idan a a, sai ya tambayeka me ke tafe da kai? Duk bayanin da zaka masa, yana rubutawa a kwamfuta. Da zarar ya gama maka tambayoyi, ya fahimci damuwar dake tafe dakai, sai ya aika sunanka, da sunayen magungunan da za a baka, idan ba bukatar yi maka gwaji. In da bukata sai ya aika ka dakin gwaji. Kana zuwa can ma lambarka kawai za ka basu. Suna dubawa, sai su dauki jikinka, su maka gwajin da likita yace a maka. A takaice dai, komai ta hanyar kwamfuta ake yi. Sannan kwamfutocin nan a jone suke da tsarin Gajeren Zangon Sadarwa na asibitin. Wannan a yanzu kenan, nan gaba, dukkan na’urorin da ake tiyata dasu, da wadanda ake jona wa mara lafiya don taimaka masa numfashi, da wadanda ke sarrafa bayanan asibiti, duk za su koma amfani da tsarin sadarwa na fasahar “5G”. Wannan zai taimaka wajen aiwatar da ayyukan asibiti cikin sauki. Daga ganin mara lafiya zuwa sallamarsa.

Inganta Fannin Ilimi

Amfani da na’’urori da hanyoyin sadarwa na zamani a makarantu wajen daukan dalibai a Najeriya abu ne sananne, shahararre. Hatta biyan kudin makaranta duk ta hanyar kwamfuta da Intanet ake yanzu. Abin da ya rage shi ne shirya tsarin karantar da dalibai ta hanya da na’urorin sadarwa na zamani. Na tabbata mai karatu zai shede ni yanzu cewa hakan bazai zama matsala ba – ma’ana, abu ne mai yiwuwa. Musamman ganin yadda muka koma amfani da wadannan hanyoyi na sadarwa tsawon lokacin da hukuma ta kulle jama’a sanadiyyar cutar Korona dake kan gasa mana aya a hannu a duniya. Cikin watan Ramada, kusan dukkan tafsirai an gabatar dasu ne ta hanyoyi da kafafen sadarwa na zamani. Daga Facebook Live, zuwa manhajar Zoom da sauransu. Nan gaba idan tsarin sadarwa na “5G” ya habbaka, dalibai zasu koma daukan karatu ta dukkan hanyoyin sadarwa na zamani. A kasashe irin su Malesiya, idan malami bazai samu zuwa aji ba saboda dalili karbabbe, sai ya shirya muku lacca ta kafar sadarwa na zamani. Yana gidansa ko duk inda yake, ku kuma kuna naku dakuna ko aji, kuna kallonsa ta hanyar bidiyo, yana harbo muku darasi kai tsaye (live). Duk mai tambaya cikinku na iya masa tambaya, kuma ya baku amsa kai tsaye. Karkashin wannan tsari yanzu akwai cikas na rashin ingancin siginar sadarwa a wasu lokuta, kamar yadda na san da yawa mun gani yayin da muke saurare ko kallon tafsiran malamai a baya, amma zuwan tsarin fasahar “5G” duk zai kawar da wannan saibi in Allah Yaso.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.