Fasahar 5G: Asali da Tarihin Samuwar 5G (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 17 ga watan Yuli, 2020.

125

Asali da Tarihin Samuwar Fasahar “5G” (2)

Shekarar 2013

A cikin watan Fabrairu na shekarar 2013 sai hukumar ITU ta samar da kwamitin bincike na musamman (Working Group), wanda ta dora masa alhakin gudanar da bincike kan mahimman abubuwa guda biyu; na farko shi ne yin nazari kan manufar ci gaban habaka kimiyya da fasahar sadarwar wayar salula zuwa shekara ta 2020. Manufa ta biyu kuma ita ce: kokarin gano makomar fasahar sadarwa ta bangaren ci gaba musamman a fannin gina hanyoyin karban sakonnin wayar salula ta karkashin kasa. Wannan kwamitin bincike, wanda ta kira: “ITU-R Working Party 5D”, an kafa shi ne don yunkurin tabbatar da ka’idojin sadarwa na zamani da fasahar “5G” za ta dogara a kansu wajen gudanuwa, ta bangaren wayar salula.

Ranar 12 ga watan Mayu na wannan shekara ne kuma kamfanin kera wayar salula mai suna Samsung ya fitar da sanarwar cewa ya samar da tsarin sadarwar wayar salula mai dauke da fasahar “5G”, mai karfin sadarwa da isar da sako mai yawo cikin kankanin lokaci a tazara mai nisa, wanda ke iya aika bayanan da mizaninsu ya kai gomannin gigabyte a cikin dakika guda. Nan take ya gudanar da gwaji na musamman, inda aka aika da sako mai dauke da bayanin da mizaninsa ya kai tiriliyon daya da miliyan dari biyar da sittin (1.56GB), zuwa tazaran kilomita biyu, cikin dakika guda. Wannan gwaji da kamfanin yayi dai an yi shi ne ta amfani da tsarin sadarwa mai amfani da titin aika sako masu yawa a lokaci guda, mai suna: “Multi-input and Multi-output”, ko kuma “MIMO” a gajarce. Karkashin tsarin, anyi amfani da hanyoyin aika sako guda takwas ne wajen tafiya, da tituna takwas wajen karba. Wato: “8×8 MIMO” kenan. Wannan gwaji da kamfanin Samsung yayi dai na cikin alamomin da suka fara nuna tasiri da ingancin wannan tsarin sadarwa na fasahar “5G”.

Cikin watan Yuli sai kasar Indiya da kasar Isra’ila suka rattafa hannu kan wata yarjejeniya da za ta basu daman gudanar da bincike na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, kan tsarin sadarwa ta marhala na biyu, wadda a yanzu ake kira da: fasahar “5G”. Sun yi wannan ittafaki ne a watan Yuli na shekarar 2013.

Watanni uku bayan wannan, cikin watan Oktoba kenan na shekarar 2013, sai wani kamfani dan kasar Japan mai suna NTT, wato: “Nippon Telegraph Telephone”, wanda kamfanin sadarwa na tarho ne, ya zama kamfani na farko a kasar Japan da ya fara amfani da wannan tsari na fasahar “5G” kai tsaye, a na’urorin sadarwarsa, don baiwa masu bukata cikin al’ummar kasar da kamfanoni, daman amfani da wannan tsari. Sanadiyyar hakan ne Hukumar Harkokin Cikin Gida da Sadarwa na kasar ta bashi kyauta ta musamman don wannan kokari.

- Adv -

A cikin watan Nuwamba na shekarar 2013 dai har wa yau, kamfanin Huawei (ana furuta shi da: “Wawe”, ba “Hawi” ba) na kasar Sin, wanda shi ne kamfanin sadarwar wayar salula da kayayyakin sadarwa mafi girma a kasar Sin, kuma kamfani na uku ko hudu a duniya a yau, ya fitar da sanarwa ta musamman cewa ya ware zunzurutun kudade da yawansu ya kai dalar amurka miliyan dari shida ($600 million) – kusan naira biliyan dari da biyar da miliyan dari shida kenan, a nairan Najeriya na wancan lokaci – don gudanar da bincike da bunkasa tsarin fasahar “5G”. A cewar kamfanin, wannan tsari a ya kaddamar zai bashi daman gina tsarin sadarwa na fasahar “5G” dake da karfin isar da sako karba, ninki 100 sama da ingancin tsarin 4G da ake amfani dashi a lokaci.

Shekarar 2019

Cikin watan Afrailu na shekarar 2019 da ta gabata ne kasar Koriya ta Kudu (South Korea) ta kaddamar da wannan sabon tsari na sadarwa a hukumance, inda ta zama kasa ta farko a duniya wajen yin hakan. Amma ba da wannan sanarwa nata ke da wuya, bayan wasu sa’o’i, sai kamfanin VERIZON na kasar Amurka shi ma ya kaddamar da tsarin a na’urorin sadarwarsa na wayar salula. Nan take kuma ya ayyana cewa shi ne kamfani na farko da ya fara hakan, ba kasar Koriya ta Kudu ba. Domin kasar Koriya ta Kudu ta fara gwajin tsarin ne, inda ta baiwa wasu shahararrun taurarin fina-finai guda 6 damar gwajin tsarin, amma ta fake da hakan don nuna ita ce ta farko. Yace ba a samu rajistan jama’a a tsarin ba sai ranar da ake kaddamar da tsarin a kasar, inda manyan kamfanoni uku na kasar – SK Telecom, da KT, da kuma LG Uplus – suka yi rajistan kwastomomi sama da 40,000 a yini guda.
Ana shiga watan Yuni na shekarar kuma, sai kasar Filifin (Philippines) ta sanar da cewa ita ma ta kaddamar da wannan tsari na sadarwa ta hanyar kamfanin wayar salular dake kasarta mai suna Globe Telecom. Wannan yasa kasar ta zama ta farko a nahiyar Asiya maso Gabas, wajen kaddamarwa da kuma fara amfani da wannan tsari na fasahar “5G”.

A nan Najeriya kuma, ranar 18 ga watan Nuwamba, kamfanin sadarwar wayar salula mai suna MTN ya gudanar da gwajin wannan fasaha a babban birnin tarayya, Abuja. Wannan shi ne gwajin fasahar “5G” na farko da aka fara yinsa a nahiyar Afirka. Bayani kan hakan ya gabata a makalar makon jiya. Sai dai wannan gwaji ne, amma a hukumance gwamnatin Najeriya bata tabbatar da wannan tsari na sadarwa ba. Don haka, ko kana da wayar salula mai dabi’un fasahar “5G”, baza ka iya amfana da fa’idojin tsarin ba.

Ana shiga watan Disamba kuma kamfanin sadarwar wayar salula na kasar Amurka mai suna: “AT&T” ya sanar da cewa shi ma tuni ya fara amfani da wannan tsari na fasahar “5G”, kuma ma har ya fara baiwa wani adadi cikin masu amfani da layukansa damar amfani da sabon tsarin. Ya kuma yi alkawarin zuwa karshen watan Yuni na shekarar 2020 tsarin zai game dukkan masu amfani da layukansa a kasar Amurka.

Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin mahimman abubuwan da suka faru cikin shekaru 10 da suka wuce, wadanda kuma su ne ke tabbatar da asali da yadda aka yi wannan sabuwar fasahar sadarwa ta kasance a aikace a halin yanzu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.