Tsarin Neman Bayanai a Intanet (1)

A baya in masu karatu basu mance ba, munyi bayani kan manhajar dake taimakawa wajen zakulo bayanai daga shafukan Intanet. A yau za mu dubi dabaru da hanyoyin da ake amfani dasu wajen yin hakan, cikin sauki.

349

Gabatarwa

Duk wanda ya karanta tarihi  da kuma asalin fasahar Intanet, zai ga cewa asalin manufar da ta haddasa bunkasa da kwarjinin wannan fasaha ita ce manufar yada ilimi da samunsa cikin sauki.  Wannan manufa kuwa ita ce kan gaba har a yanzu.  Domin haka ne galibin masu bincike suke karade duniyar Intanet don samun abin dogaro wajen bincikensu – daga dalibai zuwa malamai; daga masu bincike zuwa masu neman karin ilimi; daga ‘yan kasuwa zuwa masu binciken sanin ingancin hajojin da suke bukatar saye.  Har wa yau, idan kana neman babban dalilin da yake haddasa karancin masu bincike a dakunan karatu, musamman a kasashe masu tasowa, za ka ga cewa fasahar Intanet ce.  Domin muddin bayanai kake nema masu nasaba da kuma alaka da abin da kake bincike, cikin lokaci da kuma yanayi mai sauki, to ka je farfajiyar Intanet.  Wannan ba ya nufin cewa fasahar Intanet kadai mai bincike zai dogara da ita wajen bincikensa.  Domin akwai abubuwa da dama da ba lallai bane ya same su.  Sai dai kuma, kamar yadda duk wani mai bincike ya sani ne, duk bayanan da za su zama madogara a gareshi wajen bincikensa suna dauke ne da wasu siffofi masu muhimmanci; kamar nasaba, da saukin samu, da alaka da kuma tsari.

A bayyane yake cewa fasahar Intanet a yau duk ta kumshi bayanai masu wadannan siffofi, komai kankantar bayanan kuwa.  In kuwa haka ne, kenan mai karatu ko binciken ilimi bai da wadatuwa da fasahar Intanet a yayin da yake bincikensa.  Ga duk wani mai binciken ilimi ta hanyar fasahar Intanet, dole ne ya kiyaye wasu ka’idoji ko matakai  da za su taimaka masa kai wa ga nasara.  Domin kuwa wani muhalli ne mai dauke da nau’ukan bayanai fiye da tunanin mai bincike.  Wannan shi ke nufin cewa dole ne duk wani mai binciken ilimi a wannan muhalli ya samu wasu ka’idoji da za su taimaka masa samun abin da yake nema.  In kuwa ba haka ba, to sai ya bace.  Ire-iren wadannan matakai ko ka’idoji sun hada da:

Ingancin Bayanai

Abin da duk wani mai bincike ke so a farkon lamari shi ne ya samu bayanai ingantattu da za su taimaka masa samun kyakkyawan natija a bincikensa.  Domin a Intanet akwai bayanai nau’uka dabam-dadan, wadanda wasu suka rubuta su da manufofo dabam-daban, har wa yau.  Idan kana bincike ne a kan amfanin wani abu ko muhimmancin wani abu, za ka samu bayanai kan haka, sannan da bayanai masu akasin hakan.  Akwai hanyoyi guda biyu da duk mai bincike zai bi don tabbatar da ingancin bayanan da yake son dauka a yayin da yake aikin bincikensa.  Hanyar farko ita ce: ka tabbatar da marubucin kasidar ko makalar da ka samu.  Wa ya rubuta?  Dole ne ka tabbatar da wanda ya rubuta kasidar ko makalar.  Domin wannan zai ba ka damar ambaton madogaranka a karashen binciken da kayi.  Bayan nan, ka tabbata ka san wani kan fannin da kake son gabatar da bincike a kai.  Hakan zai dada taimaka maka wajen fahimtar manufar marubucin.  Hanya ta biyu ita ce: ka tabbata cewa marubucin ya ambaci madogaransa a ciki ko karshen kasidar.  Wannan ma zai taimaka sosai wajen fadada bincike.  Idan cikin wasu littafai ne ya tsamo bayanan, hakan zai sa ka neme su misali, don fadadawa.

Abu na karshe kan abin da ya shafi ingancin bayanai, shi ne muhallin da ka samu bayanai ko kasidar.  Ba kowane gidan yanar sadarwa za ka je don neman bayanai ba.  Ba kuma kowanne cikin sakamakon binciken da aka turo maka ke dauke da ingantaccen bayanin da kake nema ba.  Dole ne ka nemi muhallin da ke da alaka da fannin bincikenka, don samun natija mai kyau.  Misali, kana neman bayanai ne ko kasidu akan hanyoyin da ke haddasa hauhawan farashin kayayyakin masarufi a cikin al’umma (Causes of Inflation in an economy).  Dole ne ka doshi gidajen yanar sadarwar da ke da alaka da fannin tattalin arzikin kasa ko hada-hadar kasuwanci.  Bayan nan, wasu cikin gidajen yanar sadarwar da ake samun bayanai ingantattu sun hada da: rubutattun kasidun da ake samu daga gidajen yanar sadarwar jaridu da mujallu, da makarantu ko jami’o’i da kuma hukumomin da fannin ya shafe su.

Haka kuma, ana samun kasidu masu inganci a gidajen yanar sadarwar malaman jami’a ko kwararru kan fannonin da me bincike ke neman bayanai kan su.  In da hali, mai karatu ya kiyaye kansa daga tsamo bayanai daga mudawwanai zalla, wato Blogs.  Domin galibin bayanan da ke ire-iren wadannan mudawwanai, ko dai na tallace-tallace ne, ko kuma suna dauke ne da tsantsar son zuciya; ma’ana, zallar ra’ayin marubucinsu, wanda ba lallai bane ya fadi hujjojinsa ba a ciki.  Tabbas a kan samu bayanai ingantattu a wasu mudawwanan, amma da dama duk hauragiya ne a cikinsu.  A takaice dai, kada ka takaita kanka da su; duk da cewa hakan ya danganci irin bayanan da kake nema ne a bincikenka.

Nasabar Bayanai

- Adv -

Abu na biyu da duk mai bincike ya kamata ya kiyaye shi ne, alakar da ke tsakanin bayanan da ya samu, da kuma binciken da yake yi.  Kada ka rudu da taken kasida ko makala kadai.  Ka karanta sadararorin da ke ciki, don tantance alakar da ke akwai da maudu’in da kake bincike a kai.   Idan kuwa ba haka ba, sai ka tara bayanai marasa amfani, wadanda kuma ba za su baka natijar bincike mai kyau ba.  Bayan nan, cikin abin da zai taimaka maka sanin alakar da ke tsakanin kasidar da ka samu da kuma bangaren da kake bincike akwai sanin yaushe aka rubuta kasidar?  Ta yiwu kana neman bayanai ne kan dalilan da suka haddasa rushewar tattalin arzikin kasa a duniya cikin shekarar 2008.  Da ka yi tambaya sai aka turo maka kasidu masu taken: “dalilan rushewar tattalin arzikin kasa a duniya” kadai, babu shekara a cikin taken shekararKana ganin haka kai kuma, sai ka budo kasidar, ba tare da karanta kadan cikin mukaddimar ba, ka dinga loda wa kwamfutarka don taskancewa.  Sai kaje gida sai kawai ka ga ashe kasidar na Magana ne kan dalilan rushewar tattalin azikin kasa a duniya cikin shekarar 1930, wato gamammiyar matsalar farko da tattalin arzikin kasashen duniya ya fara samu.  Ka ga dai ga shi taken kasidar daya ne, kuma kan matsala daya, amma alakar shekara ko lokacin faruwa ta raba su.  Wanann kuma ke nuna cewa wannan kasidar ba  za ta maka cikakkiyar amfani ba cikin binciken da kake yi. Abu  na karshe da ya kamata mai binciken ilimi ta hanyar Fasahar Intanet ya kiyaye shi ne yin amfani da kalmomi masu siffatawa ko kwatanta abin da yake so.

Bayan haka, dole ne mai bincike ya san cewa da wahala ya samu wata kasida rubutacciya mai take da tsari da kuma zubin rubutu irin wanda yake bincike a kai.  Domin galibin abin da kowa ya sani ne cewa amfanin bincike shi ne zuwa ko samar da wani abu sabo, wanda wani bai irinsa ko makamancinsa ba.  Don haka dole ne ka yi amfani da Kalmar da za ta siffata wa manhajar neman bayanai irin nau’in bayanan da kake so.  Sannan kuma ka sani, ba wai taken kasidar da kake rubutawa kadai za ka rubuta wajen neman bayanai ba, a a.  Dole ne ka kacalcala kasidar da kake bincike a kai zuwa mataki-mataki ko sashe-sashe.  Ka kuma ayyana irin nau’in bayanan da kake so a kowane mataki, wato Outlines kenan.  Wannan zai sawwake maka samun bayanai masu nasaba da kasidar, ya kuma sawwake maka tsarin rubutun a yayin da ka tashi rubutawa.

Misali, sai malaminka a makaranta ya baka aikin gida da ka rubuta kasida mai shafi goma, kan dalilan da ke haddasa yawan hadarurruka a kan titunan Nijeriya (Causes of Road Accidents in Nigeria).  Idan ka tashi bincike, za ka nemo bayanai ne kan tsarin kare hadarruka a Nijeria, da kuma hukumomin da ke lura da hakan a Nijeriya, sannan, a karshe, ka kawo bayanai kan dalilan da ke haddasa wadannan hadarurruka a kan titunan kasar.  Wannan ke nuna cewa ba kalma daya kawai za ka yi amfani da ita ba wajen binciken bayanan da kake nema.  Kana bukatar kalmomi a kalla uku zuwa hudu, kamar haka: (1) System of road safety in Nigeria, (2) Road safety regulators in Nigeria, (3) Causes of Road Accidents in Nigeria.  Idan ka bi wannan tsari kai kanka za ka san cewa ka samu sauki, kuma rubutun ba zai maka wahala ba.  A karshe kuma, duk wanda ya karanta ya san cewa lallai ka fahimci abin da ake son ka da rubutawa.  Bayan haka, sai abu na karshe:

Ina Zan Je?

Kamar yadda bayanai suka gabata kan tsarin gidajen yanar sadarwa, duk wani bayani na kasida ko makala da za ka ci karo dashi, yana dauke ne a wani gidan yanar sadarwa.  Sai dai kuma, zai yi wahala a ce ka san dukkan gidajen yanar sadarwar da ke dauke da bayanan da kake son mu’amala da su a lokacin bincikenka.  Wannan tasa dole ka nemi hanya mafi sauki da zai taro maka dukkan wani abin da kake bukata ko hanyar samunsa.  Daga cikin wadannan hanyoyi akwai yin amfani da manhajar Matambayi Ba Ya Bata, wato Search Engine kenan.  Wannan manhaja na samuwa ne a gidajen yanar sadarwar Google, ko Yahoo!, ko kuma MSN, a takaice.  Idan ma hotuna kake nema ko bayanan da suka shafi sauti ko hotuna masu motsi, wato bidiyo kenan, duk za ka samu.  Gidan yanar sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata da suka fi shahara su hada da na kamfanin Google, wanda ke www.google.comSai kuma gidan yanar sadarwa na kamfanin Yahoo!, da ke samuwa a www.yahoo.comIdan kana son fadadawa, sai ka kara da na kamfanin Microsoft, wato MSN, shi kuma za ka samu shafinsa ne a www.msn.comDukkan wadannan gidajen yanar sadarwa ne masu amfani da wata manhaja da ke yawo rariya-rariya a giza-gizan sadarwa ta duniya, don taskance dukkan gurabun samun bayanai na hotuna ko sauti ko kuma rubutattun kasidu da makaloli.  Idan manhajar ta tattaro su, sai ta taskance su a cikin kwamfutocin da ke dauke da gidan yanar sadarwar.  Duk sa’adda mai neman bayanai ya “tambaya”, sai a turo masa bayanan – da sunan take, da takaitaccen bayani da kuma rariyar da za ta kai shi inda kasidar ko hoton yake tsibe.

Haka idan bayanan da suka kunshi hotuna masu motsi kake nema, wato bidiyo, kana iya ziyartar gidajen yanar sadarwa irin su: Youtube da ke www.youtube.com,  ko kaje Google Video da ke http://video.google.com, ko Yahoo! Video, wanda ke samuwa a http://video.yahoo.comIdan kana son fadadawa har wa yau, akwai gidajen yanar sadarwa masu rubutattun kasidu kan fannonin ilimi da dama, irin su How Stuff Works, wanda gidan yanar sadarwa ne mai dauke da rubutattun kasidu masu kwatanta maka yadda ake gudanar da abubuwa da dama, a aikace – daga kan ilimin kwamfuta zuwa yadda ake dafa abinci kala-kala, a misali.  Idan kana son sanin yadda mota ke aiki, akwai.  Idan kana son sanin yadda kwamfuta ke aiki, akwai.  Idan kana son sanin yadda tauraron dan Adam ke shawagi, akwai.  Kai a takaice dai, idan ka shiga wannan gidan yanar sadarwa, akwai abubuwa da dama da ba za ka so a ce ka wuce su ba tare da ka duba ba. Wannan ba karamar dama bace da za ta taimaka maka wajen rubutu.

Har wa yau, akwai gidajen yanar sadarwa masu dauke da rubutattun kasidu na ilimi kan fannonin rayuwa, masu tsawo wadanda aka rubuta su don amfanin masu bincike ko karantarwa, birjik.  Shararriyar cikinsu ita ce:  EssayWorld, wacce shafinta ke samuwa a www.essayworld.comA wannan gidan yanar sadarwa, akwai kasidu sama da dubu talatin wadanda musamman aka rubuta su don taimaka wa dalibai masu karatu a dukkan matakan ilimi.  Da zarar ka shiga gidan yanar sadarwar, sai ka matsa alamar “essay” da ke sama a hannun hadu.  Idan shafi ya budo, sai ka shigar da taken kasidar da kake so ko kuma taken binciken da kake son yi, a wani fili da aka tanada maka a kasa, daidai inda aka rubuta: “Search for Essays in the Essayworld Database”.  Kana matsa enter, za a budo maka tarin kasidun da suka shafi abin da kake nema; ka zabi na zaba. Wannan kadan ne cikin alfanun da ke tattare da wannan fasaha ta Intanet wajen taimaka wa mai bincike a kowane fanni ne na ilimi.

Kammalawa

Fasahar Intanet duniya ce makamanciyar wacce muke rayuwa ciki, amma a wani irin tsari da kimtsi da ya sha bamban da wannan duniyar tamu da zahiri.  Duk abin da kake bukata na bayanai kan wani nau’in ilimi a duniya, in Allah Ya yarda kuwa za ka same shi.  A wani lokacin kyauta, a wani lokacin kuma sai ka biya taro da kwabonka.  Duk da haka, samuwar fasahar Intanet a wannan zamani da muke ciki ya samar da dama ga dalibai zuwa har malamansu, wajen fadada binciken ilimi da kuma sanayya kan wannan duniya ta mu da irin al’ummar da ke makare cikinta.  Duk da yake yin hakan ba ya samuwa ta dadi ba tare da mai bincike ya san wasu ka’idoji ko matakan da zasu sawwake masa binciken ba.  Dole ya kiyaye ingancin bayanan da zai ci karo dasu yayin da yake nema; ya kuma fahimci alakar da ke tsakanin bayanan da kuma fannin bincikensa.  Idan ya san wannan, abu na karshe da ya rage masa shi ne yin amfani da kalmomin da zasu nemo masa abin da yake so, a muhallin da ya dace da wannan fannin da yake bincike a ciki.  Da wannan, sai mai bincike ya tsinci dame a kala.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Abdulmalik hassan danmoyi says

    muna godiya

Leave A Reply

Your email address will not be published.