Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet (2)

Wannan kashi na biyu kenan kan Ka’idojin Mu’amala a Intanet. Mun kawo ka’idoji guda goma. Sauran na tafe a kasidun dake biye.

210

Matashiya

A makon da ya gabata ne muka fara bayani kan Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet, inda muka yi bayani kan ma’ana da amfani da kuma tsarin da ke tattare da bin ka’ida wajen mu’amalar rayuwa gaba daya.  Daga karshe kuma muka yi alkawarin fara jero wadannan ka’idoji da nace kirkirarru ko fararru ne daga gareni, duk da yake lafazinsu ba wasu sabbin abubuwa bane da bamu taba ji.  A yau za mu ci gaba, in da masu karatu za su samu Dunkulallun Ka’idoji kan mu’amala da wannan fasaha mai harshe biyu; amfani da illa.  To, a halin yanzu ga wadannan ka’idoji nan:

In Kana Son Tsira, Shiga da Alwalarka

 Wannan Magana haka take.  Duk mai son tsira wajen samun abin da yake so ko kauce ma abin da yake ki a duniyar Intanet, to dole ne ya shiga da alwalansa, cikakkiya kuwa, ba mai lam’a ba.  In kuwa ba haka ba, to zai ta walagigi ne, ba car ba ar, har dan abin da ya tanada ya kare.  Watakil mai karatu yace: “af, Intanet ta kuma ya zama sai kana da alwala za ka shiga?”, to ba asalin alwala ake nufi ba a nan.  Abin da kalmar alwala ke nufi a nan itace: shiga da manufarka, na abin da kake son yi ko samu; shiga da iliminka, na abin da kake nema ko son yi; shiga da al’adanka mai kyau, don akwai al’adu masu dimbin yawa da za ka tarar.  Idan ka kuskure ka shiga ba tare da alwala ba, to dayan biyu; ko dai ka sha wahala wajen yawo ba tare da ka tsinana komai ba, ko kuma sai ka sha dan Karen wahala kafin samun abin da kake nema.  In ma ka samu, to dace ne.  Amma idan ka shiga da ilimin cewa ga abin da kake son zuwa ka yi, cikin dan kankanin lokaci sai ka samu abin da kake so. Sauran lokutan da ka saya su zama maka rara. Haka idan da manufa kaje, duk wata manufar da ta saba ma naka, sai dai ka kura mata ido kawai.  Haka za kai ma sauran al’adun da suka sha banban da naka.  Me kake son yi da har ka sayi lokaci don yin lilo da tsallake-tsallake?  Ina manufarka?  Nemo a halin yanzu, idan baka da ita, don ita ce tsiranka.  Har wa yau, shiga da alwalarka, in kana son tsira.  Wannan ita ce ka’ida ta farko wacce ta fi kowacce muhimmanci cikin dunkulallun ka’idojin mu’amala a Intanet.  To me yasa?

Ba Dukkan Fari Bane Fari. . .

 Sosai kuwa!  A duniyar Intanet ba dukkan abin da yai kama da gaskiya bane ke zama gaskiya, yanke.  Yadda ka san cewa ba dukkan launin fari bane yake fari; wani farin akwai baki-baki a cikinsa, idan kana da yanar ido ba za ka taba sani ba ko da kuwa ka zo kusa dashi.  Don haka bayan manufa ko ilimi da kayi tanadinsa, yana da kyau ka san cewa a Intanet akwai wasu abubuwa masu kama da juna, amma hakikaninsu ya sha banban, nesa ba kusa ba.  Ba dukkan bayanai bane za ka dauka abin kafa hujja.  Idan ba haka ba sai masana suyi ta maka dariya baka sani ba.  Akwai bayanai kan fannoni da dama, amma kana bukatar sanin me kake nema, don kada ka dauki bayanan da basu da alaka da maudu’in da ake Magana a kai, ka cakuda su.  Ko ka nemo bayanan da ba su malaminka ke so ba, ka cakuda masa aiki.  Me kake nema?  Ka tuna, ba dukkan fari bane fari.

Ko Cikin Gaskiya Akwai Karya. . .

 Haka ma ko cikin karya akwai gaskiya.  Wannan ka’ida ce mai zaman kanta.  Kada mu dauka akwai warwara, babu ko kadan.  Idan ka shigo da alwalarka, kuma ka fahimci cewa ba dukkan ilimi bane za ka dauka; akwai wanda ya cancance ka, da wanda bai cancanci abin da kake nema ba, haka kuma ka san cewa, wani nau’in bayanin da za ka dauka karya ne, to akwai kamshin gaskiya a cikinsa.  Haka kuma wasu lokuta kana iya daukan wani abu a matsayin karya ne, amma idan ka bincika sosai sai ka ga ashe gaskiya ne abu kaza.  Duk wadannan ka’idoji biyu na biye ne da ka’idar shiga da alwalarka, kuma za su taimaka maka ne wajen neman bayanai a dukkan inda kake zaton samu.

Daji Mara Kofa, Shiganka Sai Da Hikima

 Wannan haka yake.  Intanet wani duniya ne wanda bai da takamaimen kofa, don haka shiga cikin sa da gudanar da mu’amala na bukatar cikakkiyar hikima, wacce za ka damfara ta da ilimi ko manufar da ka shigo da ita.  Hikima wajen sarrafa lokacinka.  Hikima wajen mu’amala da wadanda za ka hadu dasu a wurare da dama.  Hikima wajen iya neman abin da kake so.  Hikima wajen iya sadar da sakonnin neman alfarma.  Ka tuna, a Intanet ba a san fuskanka ba; ba wanda ya san kalan jikinka, balle tsawonka.  Me aka sani a Intanet?  Rubutunka, mai dauke da manufarka, wacce ke bayyana hakikaninka.  Don daji ne mara kyaure (Sakkwatawa ku gafarce ni), shigansa sai da hikima.

Ko Da Me Kazo, An Fi Ka

 Ai ba birnin Dabo bane kadai da wannan kirari, sam ko kadan.  A Intanet duk abin da kaje dashi, sai ka samu wanda ya fi ka.  Duk iliminka, sai ka hadu da wanda ya shallake ka, nesa ba kusa ba.  Duk kwarewarka, sai samu wanda zai karantar da kai.  Duk iya tsiyanka, sai ka hadu da wanda zai maka darasi.  Duk kamun kan ka, sai ka samu wanda ya fi ka rikewa.  Duk hakurinka, sai ka samu wanda zai kure ka.  Duk fushinka, sai ka samu wanda zai kwantar maka da hankali.  A Intanet babu shugaba, balle a ce ga wanda yafi wane abu kaza, ko a ce wane ne kadai ya iya abu kaza.  Idan aka ce yau kaine wanda ya iya abu kaza a duk duniuyar, to nan da mako guda sai ka samu wanda zai koya maka abin da kake tutiyar iyawa.  Idan takamarka iya rufe gidan yanar ka ne da hanyoyin tsaro na fasaha, wani kallon gidan yake a bude, tsirara.  A yau duk Intanet ana maganar Google  wajen iya tsara manhajan neman bayanai na Matambayi Ba Ya Bata.  Shekara mai zuwa sai kaji ana maganar wani.  A da, kamfanin Microsoft ce ta rike wuta, a yanzu ba ita bace.  Don me?  Don duniya ce, wacce ko da me kazo, an fi ka.  Idan yau kai ne, to gobe fa, wani ne; kana son sa ko baka son sa.

- Adv -

Kogi Ba Ya Kin Dadi

 Duk da cewa Intanet duniya ne wanda da zaran ka shigo, to ko da me kazo an fi ka, yana da kyau mai karatu ya san cewa kogi fa ba ya kin dadi.  Wannan tasa ake cewa nau’in ilimi dai-dai ne baza ka samu a Intanet ba.  Don a kullum kawo sabbin abubuwa ake iya, gwargwadon yadda duniyar ta kai wajen wayewa kan ilimi a fannonin rayuwa daban-daban. Domin ba don makoyi ba, da gwanaye sun kare ai. Don haka kada ka dauka don an ce “ko da me ka zo an fi ka,” kace, “af, kenan bari in zauna kawai, tun da in ma naje ba wani sabon abu na kawo ba”, a a, duk abin da ka sani na ilimi, ko da kuwa akwai wasu da suka yi rubutu suka zuba, zai dace kaima ka zuba naka.  Wannan zai ba mai neman bayanai zabi da kuma tantance banbance-banbancen da ke tsakanin naka bayanan da wanda wasu suka zuba.  Don me, ba dukkan fari bane fari.  Wannan a tsarin neman bayanai kenan, amma a wasu gidajen yanar sadarwa ko wasu majalisun tattaunawa, abin ba haka yake ba.  Amma duk da mun san “kogi ba ya kin dadi”, zai dace mu kuma san cewa “teku kam yana kin dadi”.  Wannan tasa da zaran an yi ruwan sama, za ka ga teku na ta ambaliya.  Don me?  Don nau’in ruwan da ke zubowa daga sama mai gardi ne, mai dadi, amma wanda ke cikinsa ruwan gishiri ne.  Kuma tunda akwai shamaki tsakanin ruwan gishiri da na gardi ko dadi, dole a samu rashin jituwa.  Abin nufi, ba dukkan majalisun Intanet bane za ka je ka kawo wani abu sabo, wanda ba a kanshi aka assasa majalisar ba; ba dukkan gidajen yanar sadarwa bane za ka je ka kawo musu wani abu sabo, sai wanda ya dace da abin da suke so; kowace majalisa na da nata maudu’i.  Don haka mu sani, idan kogi ba ya kin dadi, to teku na ki, sosai kuwa.

Abincin ka, Guban Wani

 Wannan shi ne dalili.  A yayin da kake ganin wannan bayanin ko kuma wannan tsarin ko wannan Maganan ya kamata a fade ta don tana da fa’ida, to ka san cewa tana da muhallinta na musamman.  Kowane irin ilimi na da muhallinsa.  Idan wani abin yayi maka, to kada ka dauka dole ma ya yi ma kowa.  Domin ba haka tsarin rayuwa take ba.   Shi yasa idan ka shiga wasu gidajen yanar sadarwan, ka ga irin abubuwan da suke tallatarwa, sai mamaki ya kama ka.  To ina ruwanka?  Su a wajensu abu ne mai kyau, don watakil yayi daidai da al’adu ko addini ko tsarin rayuwarsu.  A yayin da wasu ke shiga don neman bayanai kan abin da zai ciyar da su gaba, wasu na zuwa ne wasan kwamfuta kadai.  A yayin da wasu ke zuwa don yada addini, wasu na zuwa ne don yada tsana da kiyayya a tsakanin al’adu ko addinai ko launin fata.  A yayin da wani ke zuwa don zuba bayanai masu amfani, kuma kyauta, wani kuma fatansa shi ne ya cutar da wasu ta hanyar amfani da fasaha ko kwarewarsa.  A yayin da wasu ke tallata hajoji masu amfani wajen habbaka rayuwa da tunanin dan Adam, wasu kuma assha suke yadawa.  Gashi nan dai; kowa da inda ya dosa.  Don me?  Abincin ka, guban wani.

Araha Ba Ta Ado

 Ko kadan kuwa!  Da tana yi, da duniya ta cika da kwalliya.  A Intanet akwai manhajojin kwamfuta (computer softwares) da ake bayar da su kyauta.  Wadannan manhajoji ko masarrafai suna da muhimmanci sosai.  Akwai wadanda za su taimaka maka gina gidajen yanar sadarwa.  Akwai na wasannin kwamfuta.  Akwai na kididdigan lokuta.  Akwai na koyon harsunan duniya (Ingilishi da Faransanci da Jamusanci da Mandarin dsr).  Akwai na koyon addini.  Akwai na koyon rubutu da karatu.  Akwai na koyon iya kwankwansa allon rubutun kwamfuta, wato Keyboard.  Akwai na sauraran wakoki.  Akwai na gyaran kwamfuta.  Duk wadannan, in kana so, za ka same su kyauta, har ka diro dasu kan kwamfutarka, ka rinka amfani dasu.  To amma ba a nan gizo ke sakan ba.  Galibin ire-iren wadannan manhajoji da za ka ji ana kururuta su, za ka samu suna da wani mummunan tasiri a kwamfutarka.  Idan ka loda su da yawa, za ta fara zazzabi; domin masu gina manhajojin na yi ne da wata manufa ko dai manufar kasuwanci ko kuma manufar ta’addanci, ko kuma, a karo na karshe, a samu kuskuren tsari wajen fasahar gina manhajar (wato Bugs), wanda hakan na iya cutar da kwamfutarka.  Idan baka yi sa a ba, a yayin da kake diro da wannan manhaja, lokacin kuma kake diro da gurbatattun bayanai masu rikita maka kwamfutar, wato Virus ko Spyware.   Kuma kafin ka cire su, kana bukatar manhaja na musamman don yin haka.  Ka ga anyi ba yi ba kenan.  In ka kebe tarin bayanai da za ka samu ka karanta, galibin abubuwan da ake samun su kyauta a Intanet, na tattare da wani nau’i na amfani ga mai shi, ko da kuwa baka sani ba. To dole ka lura, ka kuma rike wannan ka’ida kam a hannunka, musamman idan kwamfutar taka ce.  Ka san cewa: Araha fa, ba ta ado.

 Akan Tsinci Dame A Kala

Eh, sosai kuwa!  Duk da cewa a kan samu irin wannan cutarwa cikin galibin abubuwan da suke kyauta ne a Intanet, sau tari sai kayi dacen samun amfani sau bakwai kafin ka hadu da cutarwa daya (da sharadin kana rike da alwalarka, bata warware ba).  In kuwa haka ne, to ashe akan tsinci dame a kala kenan.  Wannan ka’ida ce mai kyau, kuma ya kamata a rike ta sosai.  Muddin ka san abin da kake nema, to za ka yi arkizi sosai a Intanet.  Amma idan ka sake ka shiga ba tare da sanin makama ko mashigi ba, za ka ji jiki kafin idanun ka su washe.  Har wa yau dai, akan tsinci dame a kala.

 Inda Ka Kwana, Nan Wani Ya Tashi

 Wannan a fili yake!  A Intanet za ka iya zubawa ko fadan duk abin da ka sani na ilimi ko kawo duk abin da ka sani na ilimin fasaha, amma kada ka taba riya cewa tunda kai ne farkon wanda ya kawa hakan, ilimi ya kare a wajen, sam.  Ko a ka’idar rayuwar yau da kullum ma ba haka abin yake ba, balle a Intanet.  A Intanet, inda ka kwana, to fa nan wani ya tashi.  In da ka ajiye alkalaminka, nan wani ya tsoma nasa cikin kuttun tawada.  Idan bamu mance ba, a kasidun baya mun ta ambaton sunayen wasu shahararrun mutane da suka kirkiri fasahohi da dama da manhajojin da suka taimaka wajen habbaka wannan fasaha ta Intanet, shekaru kusan ashirin da suka gabata ko kasa da haka.  To amma a halin yanzu, su kansu sun san cewa jiya ba yau ba.  Misali, wanda ya kirkiri ka’idar sadarwa ta World Wide Web (www) ko kuma Hypertext Transfer Protocol (http), wato Farfesa Tim Bernes-Lee (Baban Intanet), gwani ne sosai wajen ilimin kwamfuta da Intanet, amma a halin yanzu ya san cewa akwai wadanda suka sha gabansa.  Don me?  Don inda ya ajiye alkalaminsa a shekarun baya, tuni wasu suka tsoma nasu, don ci gaba.  Wannan ka’ida na cikin dalilan da suka sa Intanet ya zama gagarau a yanzu;  a kullum kara kasaita yake, sai kace bajimin sa.  Don, inda wani ya kwana, tuni wani ya tashi, don ci gaba da al’amura.

Kammalawa

 A halin yanzu za mu dakata a nan, don kauce ma tsawaitawa.  Idan mai karatu bai mance kirgan ba, mun kawo ka’idoji ne guda goma a yau; 1) In kana son tsira, shiga da alwalarka; 2) Ba dukkan fari bane fari, kamar yadda ba dukkan baki bane baki; 3) Ko cikin gaskiya akwai karya; 4) Daji mara kofa, shiganka sai da hikima; 5) Ko da me kazo, an fi ka; 6) Kogi ba ya kin dadi; 7) Abincin ka guban wani; 8) Araha ba ta ado; 9) Akan tsinci dame a kala; 10) Inda ka kwana, nan wani ya tashi.  Wadannan su ne goman farko, kuma mako mai zuwa za mu kawo cikon goma sha-dayan da suka rage.  Kamar kullum, duk abin da ba a fahimta ba, a rubuto.  Inda kuma aka samu kura-kurai, a tunatar damu.  Muna kara mika godiyarmu ga Sashen Hausa na BBC, musamman ma’aikatanta da ke ofishin watsa shirye-shiryen su da ke nan Abuja.  Har wa yau, wannan fili na mika godiya ga dukkan masu karatu, kuma da fatan ba za a gaji da rubutowa ba.  A ci gaba da kasancewa tare da mu a kullum.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    Malam ai mune da godiya.

    Fatan mu Allah ya karawa rayuwa Albarka da nisan kwana masu Albarka Amin

Leave A Reply

Your email address will not be published.