Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet (1)

Bayan makonni hudu da muka kwashe muna ta shan bayanai kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke kunshe cikin Intanet, a yau za mu juya akala don yin wata duniyar kuma. Makalarmu ta yau ta ta’allake ne kacokan kan Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet; wato hukunce-hukunce na rayuwa da suka lazimci dukkan mai son yin mu’amala a duniyar Intanet ba tare da matsala ba, muddin ya bi su sau-da-kafa.

296

Gabatarwa

Bayan makonni hudu da muka kwashe muna ta shan bayanai kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke kunshe cikin Intanet, a yau za mu juya akala don yin wata duniyar kuma. Makalarmu ta yau ta ta’allake ne kacokan kan Dunkulallun Ka’idojin Mu’amala a Intanet; wato hukunce-hukunce na rayuwa da suka lazimci dukkan mai son yin mu’amala a duniyar Intanet ba tare da matsala ba, muddin ya bi su sau-da-kafa. A lura, wadannan sun sha banban da ladubban mu’amala da muka kawo su a makalar Zauren Hira da Majalisun Tattaunawa. Su wadannan ka’idoji ne na tabbatar da wani abu ko kore yiwuwansa a Intanet. Sun fi ladubba fadin ma’ana, kuma a ko ina kana iya amfani da su, don a yanzu ma aro su muka yi daga ka’idar gamammiyar rayuwa ta yau da kullum. Mun yi haka ne saboda akwai kamaiceceniya ta asali tsakanin rayuwar yau da kullum da wacce ake gudanarwa a Intanet. Don haka in da hali, zai dace mai karatu ya haddace su. Shi yasa za mu daddatsa makalar zuwa kashi uku, in ta kama, don fadada bayanai iya gwargwadon hali. Hakan zai taimaka mana fahimtar wadannan ka’idoji. A halin yanzu ga mukaddima nan, kafin mu fara koro ka’idojin.

Ma’anar Ka’ida da Muhimmancinta a Rayuwa

Da farko, kalmar “ka’ida” dai kalma ce da ke da asali daga kalmar larabci, kuma tana nufin “asali” ko “matabbata” ko “mazauni” ko kuma “mizanin” tafiyar da wani aiki ko tsari. Amma Hausawa da suka aro kalmar, sai suka bata ma’anar karshe kawai, wato “mizani ko ma’aunin gabatar da wani aiki ko tsari.” Da wannan ma’anar ko mahangar za mu gabatar da wannan makala gaba daya. Amma Dunkulallun Ka’idoji na nufin “curarrun hunkunce-hukuncen da ke tabbatar da yadda wani tsari ke yiwuwa, ko gudanuwa, ko ake tafiyar da shi – ko kuma kore rashin yiwuwa, ko guanuwa ko yadda ake tafiyar da shi – a rayuwa ta al’ada ko addini ko wani fanni na ilimi.” A matsayin mizani da tsari na tafiyar da al’amura, Dunkulallun Ka’idoji sun samu shahara a bakin masana harkokin rayuwa kan addini da al’adu/adabi da sana’o’i, da fannonin ilimi daban-daban. Ba don komai ba sai irin kebantacciyar amfanin da wannan tsari ke da ita wajen gabatar da abubuwa cikin sauki da tsarin da ya dace, don samun sakamako mai matukar muhimmanci, ba tare da wata wahala ba.

Wannan ita ce dunkulalliyar manufa da amfanin da Dunkulallun Ka’idoji ke tattare da ita a dukkan fannoni na rayuwa. Da haka za mu samu malaman kiwon lafiya na da na su ka’idar, cewa hanya mafi sauki wajen kare cuta ita ce ta hanyar riga-kafi. Haka suka sake cewa dukkan wata cuta ana magance ta ne da kishiyarta. Shi yasa da zaran zazzabi ya kama mutum yana barin sanyi, suka ce a zuba masa ruwan sanyi, zafin jikin zai sauka nan take. Da dai sauran ka’idojin da suka tanada a wannan fanni nasu. Idan muka koma wajen adabi ko al’adar Malam Bahaushe, za mu samu shima ya tanadi nasa dunkulallun ka’idojin na tafiyar da rayuwarsa gaba daya, kamar sauran kabilu ko al’ummai.

Wadannan dunkulallun ka’idoji suna kunshe ne cikin Karin Magana da yake rayuwa da su. Yakan ce: riga-kafi yafi magani; kowa ya daka rawar wani, sai ya rasa turmin daka tasa; sara da sassaka ba ya hana gamji tofo; in kaji gangami, da labari; a sa a baka, yafi a rataya. Da dai sauransu. Bayan nan, Malaman luggar larabci su ma fa ba a barsu a baya ba wajen tsara dunkulallun ka’idojin rayuwa ko koyon wannan harshe. Suka ce duk kalmar da ke nuna mai aiki (faa’il), dole ta kare da rufu’a; duk wacce ke nuna wanda aka yi aiki a kanshi, dole ne ta kare da fataha. Duk wadannan ka’idoji ne da ke nuna ma mai koyo hanya mafi sauki wajen sanin abin da yake son koyo, cikin sauki. Duk inda ya ga kalmar suna ta kare da rufu’a, ya san kai tsaye, sunan wanda yayi aiki ne. Haka idan muka nufo zauren malaman addinin musulunci, suma ba a bar su a baya ba; malaman fikihu na da nasu, abin da suke kira Al-kawaa’idul Fiqihiyyah. Haka Malaman Hadisi da tafsiri da dukkan fannonin ilimin addini, duk za ka samu suna da dunkulallun ka’idoji masu sawwake ma mai koyo hanyar tara karatu cikin ‘yan kananan kalmomi gajeru. Malaman fikihu suka ce; dukkan ayyukan shari’a, ana lura da su ne ta hanyar niyyar mai aikin; idan aka baka ajiya, sai kayan ya bace ko aka sace, ba za ka biya ba; shari’ar musulunci ta zo ne don gyara dan Adam; duk abin da aka haramta, don yana cutarwa ne; duk abin da aka halasta, akwai amfani tattare dashi; ba a yin ijtihadi idan akwai nassi kan abin da ake Magana a kai. Wadannan dunkulallun ka’idojin fikihu kenan.

Idan muka ziyarci malaman mandiki kuwa, su ma ba a bar su a baya ba. Suka ce: duk wata halitta mai tafiya da kafan ko cikinta ta a doron kasa, to dabba ce; dan Adam dabba ne mai Magana. Da sauran ka’idojin da suma suka assasa. Da wannan, na tabbata mai karatu ya fara fahimtar inda muka dosa wannan mako. To amma wani na iya tunanin cewa ”wai me ya shafi Intanet, wajen muhimmanci, da har za a samar masa wasu ka’idoji dunkulallu? Wani amfani hakan ke da shi ga masu lilo da tsallake-tsallake a duniyar Intanet?”. Fahimtar amfanin da ke tattare da hakan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.

Duniyar Intanet da Ka’idojin Rayuwa

- Adv -

Idan masu karatu basu mance ba kuma suna tare da wannan shafi, mun sha nuna cewa tsarin rayuwa a Intanet, kadan ya sha banban da tsarin rayuwa a zahiri. Shi yasa ma za ka samu a kusan dukkan kasashen Turai da bangaren Amurka, suna da dokoki na musamman kan wannan fasaha, wanda galibinsu kusan iri daya ne da wadanda ake da su a cikin kundin mulkin kasashen. Suna haka ne don kada wani ya dauka cewa akwai banbancin tsari tsakanin rayuwa ta zahiri da wacce ake yi a Intanet. Yadda za ka tafka laifi a zahiri a kai ka kotu, to haka idan ka aikata makamancin sa a duniyar Intanet, kuma aka kama ka, sai a zarce da kai kotu, don yanke maka hukuncin da ya kamata. Ba nan kadai ba, idan muka shiga gidajen yanar sadarwan fatawowi na musulunci, za mu ga kusan dukkan tambayoyin da ake aiko musu masu alaka da hukuncin da ya shafi mu’amala da/a Intanet, amsoshin daga tsarin mu’amalar zahirin yau da kullum ake ciro su, don kwatanta abin da ya shafi hukuncin, tare da bayar da fatawa. Wannan ya faru ne saboda dukkan nassoshin da ake kafa hujja da su, basu takaitu da wani zamani ko shekaru ko yankin mutane ban da wasu ba, a a, kawai mizani suke tattare dashi, wanda da zaran an auna aikin da aka yi, sai a san hukuncin, daga irin ka’idar da nassin ya bayar. Kenan, wannan ke nuna mana cewa akwai alaka mai karfi tsakanin rayuwa ta yau-da-kullum da kuma wacce ake gabatar da ita ta hanyar fasahar Intanet.

Daga bayanan da ke sama, a tabbace yake cewa akwai alaka tsakanin tsarin rayuwa a Intanet, da kuma rayuwa a zahiri. In kuwa haka ne, kenan da akwai bukatar ka’idoji da za su taimaka ma dukkan mai rayuwa a wadannan duniyoyi biyu masu kama da kuma alaka da juna. Shi yasa ma muka ciro tsarin ka’idojin rayuwa dunkulallu a duniyar yau, don dora su a mizanin tsarin rayuwar Intanet. Banbancin kawai, shi ne na harshe da kuma al’ada. A nan, kusan dukkan ka’idojin Bahaushe ne muka dauko, kuma mun yi haka ne saboda samun cikakkiyar fahimta kan sakon da muke son isarwa. Wannan bai hana wani ya kirkiro irin wadannan dunkulallun ka’idoji da wani harshe daban ba, duk za su dauka. Duk wannan, don mai karatu ya samu tsira ne, in ya so, yayin da yake mu’amala da wannan fasaha a duk inda ya samu kansa. Riga-kafi, inji Hausawa, ya fi magani. Idan kuwa ya rasa wani abin da zai taimaka masa ganin hanya, to fa, duniyar Intanet wata duniya ce mai cakude da rikitattu da kuma natsattsun al’amura, idan baka da mizanin tantance su, za ka samu matsala. Wata duniya ce wacce hatta kofar shigarta (kwamfuta), na da wani kebantaccen tasiri ga kwakwalwan mai mu’amala. Kana bukatar dunkulallun ka’idojin da za su kwaranye maka yanar da ke idanunka, don ganin hanya da kyau, kada ka yi ta cin karo da kaya da sauran su.

Duniya ce da za ka yi mu’amala da dukkan nau’ukan mutanen da ka san suna duniyar zahiri, amma a wani yanayi da kimtsin day a sha banban da wanda kake kai yanzu. Kaga idan baka dauko ka’idar ka ta yau da kullum ka sa a gaba ba, ina rayuwa zata yi kyau? Duniya ce da akwai tabbacin sai alakar kasuwanci ta hada ka da wani ko wasu, wanda kuma dole ne ka yi wannan alaka. Kana bukatar mizani don tantance waye za ka iya ingantacciyar alaka da shi don samun abin da kake so. A duniyar Intanet, kusancin al’adu da cakuduwar su yafi kusancin da ke tsakanin mutane a zahiri, masu banbancin al’adu. Kana bukatar samun abin da zai haskaka maka don tsintar al’ada mai kyau da guje ma mara kyau. In kuwa ba haka ba, za ka jefar da naka mai kyau ka dauki wanda bai da kyau ko bai dace da kai ba, ba tare da ka sani ba.

A halin yanzu, yana da kyau mai karatu ya lura, cakuduwar ka da mutanen wasu kasashe ta hanyar Intanet, shi yafi sauki fiye da a ce ka sadu dasu a bayyane; wani mutumin da za ka hadu dashi a Intanet, ta yiwu ma har duniya ta nade ba zaku sake haduwa ba, saboda irin tazaran da ke tsakanin kasashenku. Har wa yau, yadda ka san za ka bukaci abokiyar zama don kulla alakar aure a duniyar zahiri, haka galibin wasu suke yi ta hanyar Intanet. Makonni biyu da suka gabata, gidan talabijin tauraron dan Adam da ke Gabas-ta-tsakiya mai suna Al-Arabiyyah, tai hira da wani saurayi dan kasar Ingila da yace ya rasa yadda za a yi ya samu matar da zai aura, kuma duk abin ya ishe shi. Don haka sai kawai ya bude gidan yanar sadarwa (web site), inda yake shelan wacce zata zama matarsa. Ai kafin kace me, ya samu yan mata sama da talatin da tara, daga kasashe daban-daban, da hotunansu da kuma tarihin su. Wannan bai sa ya rude ya bi na kyaun hotuna ba, sai da ya samu mizani da ka’idar tantance wacce ta fi masa, duk da nisan da ke tsakanin kasarsa da na wannan budurwa, sannan ya dace. Kan ka ce me! Sai gashi sun kulla aure, bayan ya ziyarce ta, yaga irin yanayin rayuwarta a can kasar Austiraliya (Australia). Na san wannan ba kowa bane zai iya yi a wannan bangaren duniya da muke ciki, saboda tsarin rayuwa da al’adun mu. To amma mu lura, me ya cece shi? Samun ka’ida mai kyau wacce tai masa, kafin zaban wacce zai aura.

Duniyar Intanet na cike ne da miyagun akidu a bangare daya, da kuma nau’ukan ilmummuka masu amfani a daya bangaren, sai kuma aka cakuda su a muhalli daya. Idan ba ka da ka’idar rayuwa da mu’amala, gaya min yadda za ka yi wajen tantance su? Haka idan muka zo kan addini; ai mun sha jin labarin wadanda ke musulunta sanadiyyar karanta kasida ko makala dangane da tsarin musulunci, da ace bundun-bundun suka yi ta yi a gidajen yanar sadarwa, ai idan ba tsananin rabo ba, babu yadda za a yi su samu bayanan. To amma sun san abin da suke nema, da kuma in da za su je su same shi. Kuma duk abin da ka basu, idan ba shi suke nema ba, za su mayar maka da kayanka. Idan basu shiga da ka’idojin binciken da za su yi ba, ta yaya za su samu abin da suke so?

A karshe, Intanet wata duniya ce wacce dan karamin aikin da za ka yi wajen matsa wani mashigi ko fita daga wani wuri, na iya tasiri wajen sauya rayuwarka gaba daya, kamar yadda wasu suka yi haka, suka samu farin ciki ko bakin ciki dawwamamme a rayuwarsu. Allah Yai mana jagora, amin. Duk wadannan, ishara ne nake mana na dalilan da suka sa dole mu samu dunkulallun ka’idojin da za su taimaka mana gabatar da mu’amala a Intanet.

Kammalawa

Daga karshe, zan so mai karatu ya san cewa wadannan ka’idoji nine na kirkire su a wannan tsari. Zai kuma yi wahala kaje wani littafi ko gidan yanar sadarwa ka same su a rubuce a jumlace. Na yi la’akari ne da irin tsarin da muke dashi a rayuwa ta al’ada da addini, na ga dacewar kawo mana su don samun makama a wannan duniya mai cakude da fari da baki. Bayan haka, asalin ka’idojin nan fa ba wasu sabbin kalamai bane wanda bamu taba jin su ba, a a, kari ko salon Magana ne da Bahaushe ke amfani da su a matsayin dunkulallun ka’idojin sa na rayuwar yau da kullum. Sai muka dora su a matsayi ko tsarin rayuwa ta Intanet, in da mai karatu zai kara sanin dangantar da ke tsakanin wadannan filayen rayuwa biyu; rayuwar zahiri da ta Intanet. A karkashin kowace ka’ida, akwai bayanai filla-filla kan yadda mai karatu zai sarrafa ta. Sannan wasu ka’idojin sun yi ma wasu ka’idojin kaidi, ma’ana akwai ka’idojin da ba dukkan lokuta za ka yi amfani dasu ba, suna da kayyadadden lokaci ko wuri ko yanayi, kamar yadda ka’idar masu shirya ka’ida ke cewa: kowace ka’ida da kaidinta.

A mako mai zuwa za mu fara kawo wadannan dunkulallun ka’idoji da bayanan su. Ka’idojin guda ashirin da daya ne, kuma za mu kawo guda goma sha daya a mako mai zuwa, sauran kuma mu karasa su a makon sama. Sai a biyo mu don samun cikakkun bayanai. Idan da abin da ba a fahimta ba, sai a rubuto. Har wa yau, idan an samu kurkurai sai a sanar damu don gyara. Muna mika sakonnin gaisuwa da godiyar mu ga dukkan masu bugo waya ko rubuto sakonnin gaisuwa da ban gajiya. Allah bar zumunci, amin.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Abdul majid says

    Allah ya jagora baban sadik

Leave A Reply

Your email address will not be published.