Dandatsanci: Wani Sabon Salon Yaki Tsakanin Kasashen Duniya (4)

Kashi na hudu kuma na karshe, cikin jerin kasidun dake nazari kan sabon salon yakin kutse a tsakanin kasashe. A sha karatu lafiya.

130

Tasiri Kan Siyasar Kasashe…

Bayan barna na biliyoyin daloli da wannan al’ada mummuna na Dandatsanci ya haifar ga kamfanoni da hukumomi da kuma daidaikun jama’a a duniya, da yawa cikin jama’a basu lura da mummunar tasirin wannan sana’a kan yadda ya sauya tsarin siyasar duniya ba.  Wannan ba abin mamaki bane, musamman idan muka yi la’akari da irin halin da muke rayuwa a ciki yanzu; inda kananan abubuwa ke tasiri wajen haddasa manyan al’amura a tsarin duniya gaba daya.  Watakila saboda tasirin ci gaban tsarin sadarwa ne a duniya shi yasa.  Ko shakka babu, masana sun yarda cewa tsarin dandatsanci ya haifar da sauyi kan mahangar siyasar duniya.

Manyan alamu kan haka kuwa duk basu wuce yadda zargi da tuhuma suka yawaita kan wasu kasashe na musamman, wadanda ko a sauran bangarorin harkokin rayuwa a duniya, kasashen Yamma basu tsagaita zargi a kansu ba.  Babban abin damuwa, wanda kuma har yanzu babu wanda zai iya cewa ga abin da zai je ya dawo sanadiyyar wannan al’amari, shi ne: me zai faru, me zai biyo bayan wadannan tuhumce-tuhumce?

Kamar yadda mai karatu ya gani a baya, akwai zargi na musamman, kuma mai karfi da kasar Amurka ke wa kasashen Rasha, da Sin, da kuma Koriya ta Arewa.  A daya bangaren kuma, akwai zargi na musamman, kuma mai girman gaske da kasar Koriya ta Kudu ke wa babbar makwabciya kuma ‘yar uwarta, wato Koriya ta Arewa.  Idan muka koma gabas ta tsakiya kuma, akwai zargi mai girman gaske, tare da tuhuma mai zafi da kasar Isra’ila ke wa kasar Iran kan harkar Dandatsanci.  A daya bangaren kuma, kasar Isra’ila dai har wa yau, na zargin kasar Rasha (ko ‘yan Dandatsar kasar Rasha) da laifin taimaka wa kasashen Larabawa don daukan fansa a kanta, ta hanyar dandatsanci.  Idan mai karatu ya lura, zai ga duk wadannan zarge-zarge suna samo asali ne daga zaman doya da manja da kasashen ke yi da juna, sanadiyyar rigegeniya wajen neman karbuwa a fagen siyasar duniya.  Domin dukkansu (da mai zargi da wanda ake zargi) tsoffin abokan hamayya ne a wasu bangarorin.

Wata Daban…

Sanadiyyar abin da ta kira tsananin tsokana da cin mutuncin ‘yancin kai, kasar Amurka na daukan ire-iren wadannan hare-hare da ake kai mata (duk da cewa ita ma tana kaiwa a boye; gwano ba ya jin warin kanshi) da biyu ne.  Wannan a fili yake. Domin lamarin ya kai har daya daga cikin manyan hafsoshin na kasar na nuna cewa, “Lokaci ya kusa da ya kamata masu kai ire-iren wadannan hare-hare su san cewa yin hakan, bashi da bambanci da harin yaki na makami a rayuwar zahiri.  Kuma kasar Amurka za ta rika daukansa a haka…”  Abin da wannan zance ke nufi kuwa shi ne, duk wanda ya kai wa hukuma ko wani kamfani na kasar Amurka harin dandatsanci (ta hanyar kwamfuta), to za ta dauki wannan hari ne a matsayin takala a fagen yaki.  Wannan zai sa ta dauki matakin da ya dace, muddin gwamnati ta tsayar da matsayi na musamman a kan hakan.

- Adv -

To amma daya daga cikin masana harkar sadarwar kwamfuta na kasar yace wannan kuskuren fahimta ne.  Ya kuma nuna cewa babu wata doka ta duniya da za ta iya bayar da dammar a kai wa wata kasa harin yaki na zahiri don kai ta darkake kwamfutocin wata kasa a Intanet.  Mu kaddara ma an gano cewa lallai kasar ce ta kai harin kai tsaye, ko tayi amfani da wasu wajen yin hakan.  Idan wannan zance ya mutu a yau, sanadiyyar rashin hujja mai karfi da zai sa a aiwatar dashi, babu wanda ya san abin da gobe za ta haifar.

To amma duk da haka, akwai wata mahanga kan wannan lamari.  Idan kai hari na zahiri bai yiwu ba, to akwai tabbacin nan gaba idan haka ta ci gaba, wasu ‘yan dandatsa ko wata kasa na iya amfani da wannan al’ada na dandatsanci wajen kai wa wata kasa hari, tare da ruguza dukkan harkokin rayuwa gaba daya a kasar. Shekaru ashirin da suka gabata idan wani ya fadi zance makamanciyar wannan  zai zama abin al’ajabi.  To amma a yau faruwan hakan ba zai zama da mamaki ba.  Duk wanda ya ziyarci kasahen Turai da Amurka da sauran kasashen da suka ci gaba a fannin kimiyyar sadarwa da kere-kere, zai ga kusan dukkan rayuwarsu na dogaro ne kan harkar sadarwa.  A asibitoci; tun daga rajistan marasa lafiya, da duba lafiyarsu, da kwantar dasu, har zuwa yin tiyata, duk wadannan al’amura suna dogaro ne da tsarin sadarwa, wanda ke samuwa ta hanyar kwamfutoci, da na’urorin tiyata, da na’urorin duba sassan jikin marasa lafiya da dai sauransu.

Haka a bangaren aikin banki. Duk kasar da aka darkake kwamfutocin bankunanta, aka goge bayanan da ke cikinsu, sannan aka hana musu sakat wajen karban bayanai daga cibiyarsu zuwa sauran cibiyon da wasu rassa na kasan, ko daga gare su zuwa wasu bankunan, nan take an gama da ita. Haka idan hari ya darkake kwamfutocin da ke lura da cibiyan tsaron kasar, musamman wadanda ke lura da harba manyan makamai masu hatsari, wannan lamari ba zai yi kyau ba. A bangaren safara ma haka lamarin yake.  A duk inda ka duba harkar kimiyyar sadarwar zamani ta ratsa. Daga jiragen kasa zuwa na’urorin bayar da hannu a kan titina, duk akwai tasirin kimiyyar sadarwar zamani a kansu yana gudanuwa.  A bangaren hukumomi da ma’aikatu ma haka lamarin yake. A yayin da a shekarun baya ake kashe awanni takwas kacal a ofis a tashi zuwa gida, a yanzu rayuwar jama’a ta koma ofisoshi gaba daya; a zahirance ne ko a ma’anance. Harkar sadarwa ne ke tafiyar da komai, duk inda ka leka.  Idan muka koma makarantunsu ma haka lamarin yake. Kai a takaice dai babu wani bangare na rayuwa da kimiyyar sadarwar zamani bata ratsa ba.

Wannan ke nuna cewa duk sadda wata kungiya ko kasa ta darkake wani bangare daga cikin wadannan bangarorin rayuwa, ta janibin sadarwa, to rayuwa zai canza nan take.  Abin zai fi muni idan ta bangaren tsaron kasa ne.  Domin kamar yadda hukumar lura da cibiyar makamashin Nukiliya na kasar Iran ta sanar cikin shekarun baya cewa an darkake kwamfutocin da ke sarrafa wanna cibiya da kwayar cutar kwamfuta, wanda hakan na iya kaiwa zuwa ga hana kwamfutar motsi ko yin aikinta, ko ma wani ya sojantar da ita daga wata uwa duniya, ya zama ba ta iya karbar umarni daga wanda ke sarrafa ta.  Duk wannan wani abu ne mai yiwuwa, duk da cewa ba fata ake yi ba.  A yadda harkar kimiyyar sadarwa ta bunkasa a yau, kana iya shiga kwamfutar wani dake kasar Sin a misali, kai kana Najeriya, ta amfani da kalma daya ko biyu daga kwamfutarka.  Abu mai wuya kawai shine a ce baka san lambar kwamfutarsa ba (IP Address).  Amma da zarar ka sani, kuma kana da kayan aiki da hikimar aiwatarwa, duk ba abu bane mai wahala, wai cire wando ta ka.

Da wannan masana ke ganin cewa, ta la’akari da yadda jami’an hukumomi ke zare ido a yayin da suke tuhumar wata kasa da kai musu hari ta hanyar sadarwar kwamfuta, baa bin mamaki bane idan yaki ya tashi daga daukan makamai na zahiri, zuwa amfani da kwamfutoci, don cinma burin siyasa ko daukan fansa.  Ire-iren wadannan labaru ko al’amura a baya muna jinsu, mun kuma kalle su a fina-finai, wanda a lokacin muna daukawa romon ka ne kawai; bazai taba faruwa ba.  Fina-finan kan al’amura irin wannan sun yawaita, duk da cewa an yi su ne don caza kwakwalwa (Science-Fiction), al’amura na kokarin canzawa zuwa zahiri.  Allah sawwake.

Kammalawa

A karshe dai, wannan shi ne halin da duniya ke ciki, a boye.  Kuma abubuwa irin wannan za su ci gaba da faruwa, musamman ganin cewa a yanzu ne kowace kasa ke fadaka dangane da muhimmancin gwanancewa a fannin kimiyyar sadarwa a duniya. Ba don ci gaban tattalin arziki da siyasa kadai ba, har da kokarin amfani da wannan fanni wajen ceto kasa daga hatsarin da ka iya faruwa bagatatan.  Kasashe masu tasowa kam ba a maganarsu.  Domin a yayin da suke ta kokarin ganin sun ci moriyar wannan fanni a bangaren tattalin arziki da saukin shugabanci, wasu kasashen na can suna amfani da shi wajen cinma manufofin siyasa da diflomasiyya.  Gaba-dai gaba-dai!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.