Dandalin Facebook a Mahangar Binciken Ilimi (2)

Wannan kashi na biyu kenan, cikin binciken da muke yi mai zurfi kan Dandalin Facebook. Asha karatu lafiya.

79

Tsarin Mu’amala a Dandalin Facebook

Tsarin mu’amala a dandalin Facebook ba wahala.  Abu na farko da ake bukata wajen duk mai sha’awar yin hakan shi ne yin rajista a zauren gidan yanar sadarwar kamfanin, wanda ke www.facebook.com.  Yin rajista dai kyauta ne, kamar yadda na tabbata mai karatu ya san hakan.  A lokacin yin rajistan za a bukaci sunanka ne, da suna ko lakabin da  kake so ka rika shiga shafinka da shi (Username ko User ID), da kalmomin iznin shiga (Password), sai kuma adireshin Imel dinkaKana gama shigar da wadannan bayanai, za a sanar da kai cewa an tura maka sako a akwatin Imel dinka, sai kaje can ka budo.  Idan ka budo za ka ga sakon da ke ciki, mai dauke da rariyar likau din da za ta kai ka can shafin da ka bude.  Da zarar ka matsa rariyar da aka aiko maka, za ta zarce da kai ne shafinka kai tsaye.

Daga nan sai ka ci gaba da shigar da bayanai; kamar cikakken sunanka (idan kana son yin hakan), da adireshin gida da na ofis, da adireshin shafin Intanet idan kana da shi, da aikin da kake yi, da ra’ayoyinka na siyasa ko addini misali, da irin dandanon da kake da shi a rayuwa (kamar abubuwan da kake so – abin ci ko sha ko aiki ko duk abin da ke baka sha’awa), da dai sauran abubuwa da sai ka shiga za ka gani.  Bayan haka sai ka shigar da hotonka ko na duk abin da kake so, da suna ko lakabin da kake son a rika shaida shafinka da shi, da dai sauran abubuwa.  Kasancewar wannan dandali ne na abota da haduwa da juna, akwai masarrafar da za ta baka damar gayyatar abokanka da kake da adireshin Imel dinsu a akwatin sadarwarka ta Imel.  Idan kuma ba ka da su, duk bai baci ba; akwai inda za ka yi tambaya, a nemo maka mutanen da suke nahiyar da ka fito, ko irin aikin da kake yi, ko irin makarantar da ka gama, ko irin jinsinka, ko kuma irin dabi’u da dandanonka.  Duk wadannan hanyoyi ne da za ka iya samun abokanai don yin mua’amala a tsakaninka da su.

Idan ka gama gyatta shafinka, kana iya gayyatar mutane kamar yadda bayanai suka gabata, sannan akwai bango da aka tanada maka (wato Wall) don shigar da bayanai saboda masu ziyara su karanta. Wannan bango yana tsakiyan shafin ne daga sama zuwa kasa.  Akwai kuma inda za ka rika rubuta ra’ayoyinka, da abin da ko halin da kake ciki.  Wannan wuri shi ake kira Status, kuma da shi ne dukkan abokanka za su rika sanin halin da kake ciki, ko yanayin da kake ciki, ko inda ka tafi; muddin ka rubuta su, to za su gani.  Sannan dukkan bayanan da suke dauke cikin wannan wuri masu bayyana hali ko yanayinka, za su rika bayyana a cikin bangonka, kuma duk wanda ka taskance a matsayin abokinka, zai rika ganin wadannan bayanai a bangonsa – kamar yadda kai ma za ka iya ganin nasa a bangonka.

Bayan haka, akwai masarrafar yada labarai (wato Live Feeds), wacce ke kwaso maka wainar da ake toyawa tsakaninka da abokanka, ko tsakanin abokanka da abokansu, da wadanda ke kulla alaka, da kuma tsokacin da wasu ke yi a shafinka (wato Comments).  Kana da damar shigar da bidiyo a shafinka, wadanda ka dauka a wayarka ta salula ko kyamarar bidiyo dinka.  Sannan kana da damar shigarwa ko bude albom na hotuna iya son ranka.  Wadannan hotuna ana iya ganinsu a shafinka; musamman ma abokanka.  Sannan kai ma kana iya ganin hotunansu da suka zuba, har ma kayi tsokaci ko Karin bayani na yabo ko suka kan hotunan.  A bangaren raha kuma akwai masarrafar naushi ko tsikari (Poke) wacce kana iya yinta ga kowane cikin abokanka.  Da zarar ka matsa alamar a shafinsa, sai alamar masarrafar ta alamanta a sunansa cewa “wane ya tsikari wane”, a misali.  Kana kuma iya taskance bayanan sirri a masarrafar allon rubutunka da ke shafinka, wato Notes. 

Kana kuma iya yin hirar ga-ni-ga-ka (wato Intstant Chat) kamar yadda ake yi a manhajar Yahoo Messenger misali.  Akwai kuma dan karamin shagon saye da sayarwa (wato Market Place) da ke cikin kowane shafi.  A wannan shago, kana iya tallata kayayyakin da kake da su na sayarwa.  Amma wannan masarrafa ta fi amfani ne ga wadanda ke sauran kasashe inda tsarin kasuwanci irin wannan ke ci.  Dukkan wadanann masarrafai, da ma wasu, za ka same su a shafin da ka bude.  A karshe kuma dole ne kayi hakuri da tarin hotunan tallace-tallace da ke kowane shafi.  Da su ne masu gidan yanar sadarwar ke samun kudaden shiga.  A takaice dai duk wadannan hanyoyin mu’amala da bayanansu suka gabata sun samu ne sanadiyyar babbar masarrafa ko manhajar da ke gidan yanar sadarwar, wacce ke ba da damar kirkirar kananan masarrafan da ke sawwake tsarin mu’amala a shafukan duka.  To yaya tsarin wannan masarrafa ko manhaja yake?

- Adv -

Babbar Manhajar Facebook

Daga lokacin da ka shiga gidan yanar sadarwar dandalin Facebook, ka shigar da bayanai, ka gayyaci abokai, ka amince wa masu nemanka da abota, ka yi tsokaci kan bayanan wasu, ka sanya hotuna ko ka kalli na wasu, ka kai ziyara ko kuma kayi hira da wani  kai tsaye, har zuwa lokacin da za ka fice daga gidan yanar sadarwar ko dandalin, kana yin hakan ne a saman wata manhaja ko babbar masarrafa (wato Software Platform) da dandalin ke gudanuwa a samanta.  Wannan masarrafa ita ce ruhin dandalin gaba daya.  Wannan babbar manhaja ko masarrafa, ita ce masu gidan yanar suke kira “Facebook Markup Language”.  Manhaja ce da aka gina ta da dabarun gina manhajar kwamfuta.  Kuma da wadannan dabaru ne har wa yau duk mai sha’awar gina wa dandalin manhajar da za a rika amfani da ita don sadarwa ke dogaro.

Dukkan masarrafan da masu amfani da shafin Facebook ke amfani da su suna damfare ne da wannan babbar manhaja; daga gareta aka kago su, kuma a kanta suke rayuwa, tare da habaka.  Daga masarrafar bayar da kyaututtuka (wato Gift App), har zuwa masarrafar da masu shafin ke amfani da ita wajen sanya bidiyo da na wasan kwamfuta (wato Chess), duk daga wannan babbar manhaja suka samo asali.

Wannan masarrafa ko babbar manhaja ta Facebook Markup Language ta fara bayar da damar kirkirar kananan masarrafai ne tun cikin shekarar 2007, kuma ya zuwa shekarar 2008 an kirkiri kananan masarrafai sama da dubu talatin da uku (33,000).  Ba wai masu gidan yanar sadarwar kadai ke wannan aiki na samar da hanyoyin yada abota da zumunci a wannan dandali ba, a a, duk mai sha’awa, wanda kuma ke da kwarewa ta ilimin gina manhajar kwamfuta (wato Developer ko Web Programmer) yana da damar da zai iya taimakawa. Ya zuwa shekarar 2009 an samu masu wannan hidima sama da kwararru dubu dari hudu (400,000).

Wannan babbar manhaja bata tsaya wajen bayar da damar mu’amala da dandalin Facebook ta kwamfutar kan tebur (Desktop) da kuma ta tafi-da-gidanka (wato Laptop) kadai ba, hatta ga wayoyin salula masu tsarin mu’amala da fasahar Intanet ma na iya mu’amala da shafin kai tsaye, tare da ribatan habakakkun masarrafan da ke saman wannan manhaja, iya gwargwadon damar da masu kera wayar suka bata wajen yin hakan.  Masarrafar da aka gina mai bayar da damar mu’amala da dandalin Facebook a wayar salula nau’in Samartphones dai ita ce: “Facebook iPhone App”, wacce aka kirkira a watan Agusta ta shekarar 2007. Kintsatssiyar nau’in wannan masarrafa a yanzu dai ita ce Facebook iPhone App 3.0, wacce kamfanin ya fitar a shekarar 2009.  Duk mai wayar salula irin ta zamani nau’in Smartphone na iya shiga wannan shafi ya kuma yi mu’amala da mutane kamar a kwamfuta yake. Haka kamfanin Nokia Corporation ma ya samar da wannan masarrafa a cikin wayoyin salularsa masu dauke da babbar manhajar S60 (misali N97) ta hanyar masarrafar ovi Store da ke dauke a wayar.  Idan muka ziyarci kamfanin Google shi ma haka za mu gani.  Ya samar da wannan masarrafa cikin babbar manhajar wayarsa ta salula da ya kera mai suna Android 2.0.  A karshe har wa yau, akwai wannan masarrafa cikin wayoyin salula nau’in Blackberry. Idan ka samu wadannan nau’ukan wayoyin salula duk kana iya mu’amala da dandalin Facebook kai tsaye, tare da masarrafan da suka dace da tsarin wayarka.

Wannan babbar manhaja ta Facebook Markup Language na dauke ne cikin manyan kwamfutoci ko kace Uwargarke mai bayar da damar mu’amala da bayanan da ke cikinta.  Masarrafar da wannan Uwargarke ke amfani da ita wajen bayar da damar mu’amala da shafin (wato Front-end Servers) dai ita ce PHP LAMP, wato Hypertext Preprocessor LAMP.  Wannan manhaja ce ta musamman da ake gina ta da tsarin gina manhajar kwamfuta a gidajen yanar sadarwa mai suna PHP.  Aikinta dai shi ne ta sadar da kai da Uwargarken, ta hanyar nuna maka shafukan da ka bukata, a irin yanayin da suka kamata.  Masarrafar da ke can kurya mai lura da babbar manhajar kuma an gina ta ne da dabarun gina manhajar kwamfuta nau’uka daban-daban, wadanda suka hada da: C++, da Java, da Phython, da kuma Erlang.  Na san ba lalai bane mai karatu ya fahimci wadannan abubuwa, saboda fahimtarsu na bukatar zurfin karatu cikin fannin kimiyyar sadarwa ta kwamfuta da yada bayanai.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    MASHA ALLAH

Leave A Reply

Your email address will not be published.