YouTube: Taska Mafi Tsada Da Haɗari a Intanet (1)

Asali da Bunƙasar Shafin YouTube

Saye wannan shafi ko dandali na YouTube daga waɗancan matasa yasa kamfanin Google ya jinginar da asalin shafinsa na bidiyo mai suna Google Video, ya kuma ci gaba da inganta tsari da kimtsin wannan manhaja ta YouTube har zuwa yadda take a wannan lokaci da nake wannan rubutu. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 19 ga watan Mayu, 2023.

122

Gabartarwa

Daga cikin shahararrun wurare dake ɗauke a giza-gizan sadarwa ta duniya da muke kira da suna Intanet, akwai shafi ko dandalin YouTube. Wuri ne shahararre, kuma ya keɓanta da abubuwa da dama da mafi rinjayen wurare ba su da irin siffofinsa a Intanet. Waɗannan keɓantattun siffofi ne suka bambanta abin da wannan dandali ke ɗauke da na fa’idoji da sauransu. A wannan mako zuwa makon dake tafe, za mu yi bayani ne a taƙaice kan asalin shafin YouTube, da fa’idojin dake ɗauke cikin wannan shafi, da kuma abubuwan da suke da matuƙar haɗari, amma kuma suna nan su ma ɗauke kan wannan dandali.

YouTube, Daga Ina Kake?

Kafin samuwar wannan shafi ko ma kalmar “YouTube” a Intanet tsakanin shekarar 2000 zuwa 2004 misali, akwai shafukan yaɗawa da ɗora bidiyo irin su Daily Motion, da Google Video, da sauransu da a halin yanzu sun ɓace. Amma shafin Google Video, wanda na kamfanin Google ne, ya ci gaba har zuwa watan Fabrairu na shekarar 2005, lokacin da aka samu wani sabon dandalin ɗorawa da yaɗa bidiyo a Intanet mai suna: “YouTube”.

Waɗanda suka ƙirƙiri wannan shafi dai wasu matasa ne su uku: Steve Chen, da Chad Hurley da kuma Jawed Karim. Ga hotonsu nan na maƙalo, wanda suka ɗauka tare da tsohon shugaban ƙasar Amurka Bill Clinton lokacin da yake shugaban ƙasa. Ofishinsu na farko yana birnin San Bruno ne a jihar Kalfoniya na ƙasar Amurka. Bayyanar wannan shafi ko dandalin yaɗa saƙonnin bidiyo a Intanet ya ƙara wa fasahar Intanet shahara a duniya, saboda dandalin ya samu karɓuwa sosai, kuma mutane na ziyartarsa a kowace rana da lokaci don amfanuwa da bayanan dake cikinsa.

Cikin Oktoba na shekarar 2006 kamfanin Google ya saye wannan shafi da manhaja na YouTube daga waɗannan matasa, akan zunzurutun kuɗi dala biliyan ɗaya da miliyan ɗari shida da hamsin ($1.65bn). Ba tsabar kuɗi aka basu ba, an biya su ne da jarin kamfanin Google a wancan lokaci. Sai wannan ya sa su cikin sahun masu mallakar jarin kamfanin Google su ma.

- Adv -

Dandalin YouTube a Yau

Saye wannan shafi ko dandali na YouTube daga waɗancan matasa yasa kamfanin Google ya jinginar da asalin shafinsa na bidiyo mai suna Google Video, ya kuma ci gaba da inganta tsari da kimtsin wannan manhaja ta YouTube har zuwa yadda take a wannan lokaci da nake wannan rubutu.

Daga cikin sauye-sauye masu tasiri akwai raba manhajar zuwa gida biyu, na kyauta da na kuɗi. Ɓangaren kyauta shi ne tashar da kake cin karo dashi da zarar ka hau Youtube, shi suke kira: “YouTube Free”. Na kuɗi kuma shi ne wanda za ka yi rajista, ka ɗora katinka na ATM don riƙa biyan kuɗin tasha a duk wata, kamar yadda ake biyan na tashoshin tauraron ɗan adam irin su DSTV da Startimes. Wannan ɓangare shi suke kira: “YouTube Premium”. Ta ɓangaren nau’ukan bidiyon dake kai an kasa manhajar ne gida biyu shi me; ɓangaren saƙonnin bidiyo na wasu shirye-shirye, da bidiyo na waƙoƙi na kyauta, wannan shi suke kira: “YouTube Videos” a sake. Ɗayan kuma ya ƙunshi saƙonnin bidiyo ne na waƙoƙi masu haƙƙin mallaka (Copyrighted Music Videos), wanda yake ƙarƙashin tsarin YouTube na kuɗi da bayaninsa ya gabata a sama.

Dangane da nau’ukan bidiyon dake dandalin YouTube kuma, an kasa su zuwa ɓangare-ɓangare (Categories): akwai gajerun fina-finai, da cikakkun fina-finai, da waƙoƙi, da bdiyo masu ɗauke da tarihi da bayanin abubuwa na ilimi, da saƙonnin bidiyo na kan titi, da waɗanda jama’a ke ɗorawa kai tsaye don gabatar da shirye-shirye na ilmi ko bukukuwa ko karatuka na faɗakarwa (YouTube Live), da dai sauransu. Bayan shafin YouTube da za ka iya hawa kai tsaye a kwamfuta ta adireshin: https://www.youtube.com, akwai manhajar YouTube na wayar salula da za ka iya saukewa daga cibiyar manhaja dake Play Store ko Apple Store, idan wayarka bata zo da ita ba. Sannan kana iya hawa dandalin YouTube ta manhajar YouTube dake manyan talabijin na zamani (Smart TVs).

Kana iya amfani da shafin YouTube kai tsaye ba sai kayi rajista ba. Idan kana son yin rajista kuma sai ka mallaki adireshin Imel na Gmail. Wannan kaɗai ya isa. Ta haka ne za ka iya buɗe tasha (Channel) da suna na musamman, don ɗora naka saƙonnin bidiyon kai tsaye. Kusan dukkan kafafen yaɗa labaru na talabijin da jaridu da tashoshin talabijin na tauraron ɗan adam, da wasu cikin hukumomin gwamnati, da kamfanoni, da ɗaiɗaikun mutane, da ƙungiyoyi suna da tasha a YouTube. Kana hawa shafin za ka ci karo da nau’ukan saƙonnin bidiyo birjik; ya danganci ƙasar da kake, da yaren da kake amfani dashi a kan waya ko kwamfutarka, da sabo da hawa ko sabuntar zuwa, idan baka taɓa ta’ammali da shafin ba. Kana iya tambayo irin nau’in bidiyon da kake nema kai tsaye ta amfani da manhajar matambayi-ba-ya-ɓata (Search Engine) dake sama a shafin farko.

Bayan haka, shafin YouTube na ɗauke ne da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga. Daga ciki akwai ɗora tallace-tallace, waɗanda kake cin karo dasu kafin ko a tsakiyar bidiyo idan kana kallo, da kuɗin tasha na wata-wata da masu rajista a YouTube Premium ke biya, da sai kuɗaɗen da Google ke rabawa tare da masu haɗin gwiwa dasu wajen ɗora saƙonnin bidiyo. Misali, idan kayi rajista ka buɗe tasha, ka samu wani adadi na mutane a tasharka, za a riƙa ɗora talla a kan bidiyon da kake ɗorawa. Idan kuɗin yakai dala 100 sai a riƙa aiko maka a duk wata. A ƙarshen shekara ta 2022, kamfanin Google ya samu dala biliyan ashirin da tara da miliyan ɗari uku da ashirin ($29.32bn).

A ƙarshe, shafin YouTube ne shafi mafi shahara a duniyar Intanet bayan shafin Google Search. A shekarar 2019 misali, an ƙiyasta cewa a duk cikin minti guda, mutane suna ɗora adadin bidiyon da tsayinsa ya kai awa 500. Sannan a duk wata maziyarta biliyan biyu da rabi ne ke ziyartan shafin, kuma a kullum ana kallon bidiyon da tsayinsa ya kai awa biliyan ɗaya!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.