Yadda Ake Tacewa da Sarrafa Danyen Mai

A yau mun karkare wannan bincike kan yadda ake hako danyen mai daga karkashin kasa ko teku. Da fatan masu karatu sun amfana.

517

Bincike kan Danyen Mai, da Yadda aka Fara Hako Shi

Mutane sun dade suna amfani da wannan bangaren danyen mai da suke samu a saman kasa yana malala, kamar yadda bayanai suka nuna a baya, amma ba a fara gudanar da bincike na kimiyya mai tushe a kansa ba sai bayan shekaru dari biyar, wato cikin karni na shatara kenan.  Wannan shi ne lokacin da kasashen turai suka fara juyin juya hali kan kere-kere da kimiyya, wato Industrial Revolution.  Lokacin ne aka fara kera injina masu bukatar makamashin da za a sarrafa su da shi, da kuma sababbin hanyoyin samar da makamashin amfanin gida, irin su fitilu, da injinan amfanin gida da dai sauransu.  Bayan shekaru hamsin da shiga wannan karni ne wani masanin fannin Fiziya mai suna Abraham Gesseur, dan kasar Kanada, ya nemi hukuma ta bashi lasisin sakamakon bincike na musamman da yayi kan danyen mai, inda a karshen bincikensa ya gano cewa idan aka tace danyen mai, ana iya samun man kananzir, wato Paraffin kenan. Ya yi haka ne a shekarar 1852.  Kenan, a wannan shekara ne aka gano kananzir a tarihin duniya.

Ana cikin haka, sai wani kamfani ya gano rijiyar danyen mai a kasar Poland, cikin shekarar 1853, wato shekara daya kenan bayan wancan bincike.  A tarihin duniya, wannan ita ce rijiyar danyen mai ta farko da aka fara ganowa, wacce kuma aka hako mai, da tace shi, don sayarwa a duniya.  Kada mu mance shekarar, ita ce 1853.  Bayan shekaru biyu kuma sai ga wani masanin kimiyya mai suna Benjamin Sillimon, wani dan kasar Amurka, dauke da rahoto na musamman kan binciken da ya gudanar cikin danyen mai.  A cikin rahoton ne ya sanar wa duniya cewa lallai akwai nau’ukan makamashi da yawa a cikin wannan danyen mai, kuma masu amfani ne kwarai ga rayuwar dan adam. Benjamin ya yi wannan bincike ne cikin shekarar 1855. Da aka kara samun wasu shekaru biyu kuma, sai wani kamfanin mai ya gano rijiyoyin mai a kasar Jamus, ta hanyar amfani da na’urorin hako mai na zamani a wancan lokaci.  Wannan kamfani ya yi wannan aiki ne daga shekarar 1857 zuwa shekarar 1859.  Daga nan dai sanayya kan danyen mai da kuma amfaninsa ya ci gaba da yaduwa a duniya a hankali har zuwa wannan zamani da muke ciki.

Yadda ake Tace Danyen Mai da Sarrafa Shi

- Adv -

Duk da cewa mai tambaya bai bukaci sanin yadda ake tace wannan sinadari na danyen mai ba, na ga dacewar sanar damu wannan, don samun karuwar ilmi da fahimta.  Shi ilmi, kamar yadda muka sani, ba kaya bane da zai iya karya maka wuya don ka dauke shi da yawa.  Sai in ka sani, amma ka take – a fannin addini da hakkokin mutane.

Tace danyen mai, wanda a turancin Kimiyyar Man Fetur ake kira Fractional Distillation, wani tsari ne na ilmi da kuma amfani da na’urorin sarrafawa tare da tace danyen mai, don fitar da nau’ukan makamashi daga cikinsa. Hakan kuma na samuwa ne ta hanyar amfani da manyan injinan toya mai, da sarrafa shi, a wasu mizanin zafi na ma’aunin Santigireti.  Wadannan injina na dauke ne da wasu manyan fanfunan karfe masu daukan zafi, wadanda ake kira “Gas-heated Furnace.”  Kuma suna aikin rarrabe nau’ukan man da ke cikin danyen mai ne a mizanin zafi na Santigireti daga “00C”  har zuwa sama da ma’aunin zafi “4000C.”  Akwai matakai shida da ake bi wajen tace wannan danyen mai, kuma a kowane mataki akwai nau’in man da ake fitarwa, wanda ya dace da irin zafin tuyan da danyen man ya ji. A haka ake fitar da nau’ukan makamashin da ke cikin danyen mai, irinsu daskararren man kwalta, wato Bitumen, da man kananzir, wato Paraffin, da nau’ukan mai marasa nauyi, irin su man fetur, da man dizel, da gas, da kuma man jirgin sama.  Dukkan wannan aiki ana yinshi ne a Matatar Mai, watai Oil Refinery.

Matakin farko shi ne matakin zafin da ya wuce “400” a ma’aunin zafi na Santigireti.  A wannan mataki ne ake tace nau’in mai mai matukar kauri, wanda ake amfani da shi wajen shafe tituna, wato Bitumen kenan, ko kwalta, kamar yadda mai karatu zai fi fahimta da wuri.  A Makati na biyu kuma, wanda ya faro daga ma’aunin zafi na “330” zuwa “400” a ma’aunin zafi na Santigireti. A wannan zango ne ake tace mai da ake amfani dasu wajen rage kaushin karafa da sauran abubuwa masu tsatsa – kamar su man giris, a misali.  Sai mataki na uku da yake farowa daga ma’aunin zafi na “260” zuwa “330”.  A wannan zango ne ake tace nau’in mai mai nauyi, wanda injina masu karfi ke amfani dashi, irinsu man dizel kenan.  Sai mataki na hudu, wanda ya faro daga ma’aunin zafi na “190” zuwa “260”.  A wannan zango ne ake tace man kananzir da ire-irensa.  Sai mataki na biyar wanda ke farawa da ma’aunin zafi na “40” zuwa “190”.  A wannan zango ne kuma ake samun taco man fetur da muke amfani dashi a ababen hawanmu – motoci da mashina da injina ko wasu nau’ukan janareto kanana.  Daga nan kuma sai mataki na karshe, wanda ke farawa daga ma’aunin zafi na “0” har zuwa “40” a ma’aunin zafi na Santigireti.  Wannan shi ne zangon tace mai na karshe, kuma a wannan zango ne ake fitar da nau’ukan mai marasa kauri, masu cakude da iska, irinsu man gas, da man gas na dafa abinci (Cooking Gas), da kuma sinadaran da ake yin sabulu da su don amfanin gida da ma’aikatu.

Kammalawa

Wannan a takaice, shi ne dan abin da ya samu.  Kamar yadda mai karatu ya sani, bincike kan wannan fanni abu ne mai fadi, wanda ke bukatar lokaci da kwazo. Dan abin da muka kawo a nan ya zo ne don gamsar da tambayar mai tambaya.  Sannu a hankali za mu rika dauko wasu bangarorin da bamu tabo su ba a yau, don basu hakkinsa gwargwadon hali.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.