Tsarin “Cashless” Da Hanyoyin Inganta Shi a Najeriya (4)

Fa'idojin Tsarin "Cashless"

Masu fashin baƙi kan harkokin zaɓe a Najeriya sun tabbatar da cewa babu zaɓen da kuɗi yayi ƙarancin tasiri a cikinsa irin wannan da ya gabata.  Dalilin kuwa ɗaya ne; an toshe dukkan hanyoyin da a baya ake amfani dasu wajen sayen ƙuru’u lokacin zaɓe. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 17 ga watan Maris, 2023.

127

Fa’odojin Samar da Tsarin “Cashless”

Kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya, an samar da wannan tsari na “Cashless” ne don tabbatar da wasu manufofi masu alaƙa da cin gaban ƙasa ta ɓangaren tattalin arziƙi da tsaro.  A ƙarƙashin waɗannan manufofi akwai fa’idoji da dama da ake tsammanin samunsu yayin da aka gama ɗabbaƙa wannan tsari mai matuƙar tasiri.  Musamman ganin cewa ta wannan tsari ne kaɗai gwamnati ke da cikakken iko kan hada-hadar da mutane ke yi na kuɗaɗe ta amfani da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani.  Daga cikin fa’idojin da ake tsammani sun haɗa da:

Rage Yawan Sace-Sace

Tsarin “Cashless” yana rage yawan takardun kuɗaɗe ne dake hannun mutane.  Da zarar an gama ɗabbaƙa wannan tsari yadda ya kamata, yawan takardun kuɗaɗe da za su riƙa yawo a hannun jama’a bazai wuce kashi 30 ba cikin 100.  Ragowan kashi saba’in ɗin duk ta hanyar kafofi da na’urorin sadarwa na zamani za a riƙa aikawa da karɓarsu.  Wannan, ta ɓangaren tsaro, zai rage yawan sace-sace masu alaƙa da takardun kuɗaɗe.  Idan ba masu shagunan sayar da kayan masarufi ba, ko masu sayar da hatsi, da wahala kaga mutane riƙe da takardun kuɗaɗe.  Don, haka kasuwar masu sace-sace a kasuwanni da gidajen jama’a, da masu fashi da makami a ƙauyuka don ƙwace kuɗaɗen mutane, za ta ƙaranta matuƙa.

Rage Yawan Garkuwa da Mutane

Haka kasuwar masu garkuwa da mutane ma, ana sa ran ita ma za ta samu naƙasa.  A baya ba abin mamaki bane kaji an sace mutum ana neman maɗuɗun kuɗaɗe kusan miliyan ɗari ko sama da haka; kuma duk takardun kuɗi suke nufi.  A yanzu ko an yi garkuwa da mutum aka nemi waɗannan kuɗaɗe da wahala a same su ta daɗi.  Idan kuma tiransfa suka ce a musu, cikin sauƙi za a iya kama su.  Tunda dole ta taskar banki za a sa kuɗin, kuma cikin sauƙi hukuma na iya gano mai taskar ajiyar, a kuma kama shi.  Haka idan suka karɓe katin ATM ɗin wanda suka kama, ba zai musu amfani ba.  Domin ko akwai adadin kuɗin da suke buƙata a ciki, ba za su iya cirewa cikin lokaci guda ba.  Hakan ya faru ne saboda tarnaƙin aka sanya wa kowane taskar ajiya na iya adadin kuɗaɗen za a iya cira a yini ko a mako.

Rage Hanyoyin Maguɗin Zaɓe

- Adv -

Wannan na cikin mafi girman fa’ida da ake tsammanin samu.  Kuma hakan ya bayyana musamman a zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘Yan Majalisun Tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da ta gabata.  Masu fashin baƙi kan harkokin zaɓe a Najeriya sun tabbatar da cewa babu zaɓen da kuɗi yayi ƙarancin tasiri a cikinsa irin wannan da ya gabata.  Dalilin kuwa ɗaya ne; an toshe dukkan hanyoyin da a baya ake amfani dasu wajen sayen ƙuru’u lokacin zaɓe.  Domin daman da takardun kuɗaɗe ake amfani, musamman a ƙauyuka.  Ko dai wajen sayen katin zaɓe, ko ribace masu jefa ƙuri’a ta hanyar basu kuɗi don su zaɓi ɗan takarar da ake so, ba wanda suke so ba.  Amfani da hanyar tsarin “Cashless” zai ci gaba da yin tasiri matuƙa wajen rage wannan badaƙala, tare da samar da tsari da tsafta cikin siyasar Najeriya.

Toshe Kafofin Satar Kuɗaɗen Ƙasa

Yawan amfani da takardun kuɗaɗe a hukumomin gwamnati na Fedara ko Jiha ko Ƙananan Hukumomi na cikin hanyoyi masu sauƙi na sace kuɗaɗen jama’a; ko dai wajen karɓan kuɗaɗen a hannu yayin da aka gudanar da wata hidima ga jama’a, ko wajen ciro su don aiwatar da wasu ayyuka.  A yanzu galibin hanyoyin karɓa da biyan kuɗaɗe a hukumomin gwamnatin Tarayya (da ma wasu jihohi), duk sun koma ta hanyar amfani da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani.  Wannan ke rage yawan karɓa da ta’ammali da takardun kuɗaɗe a ma’aikatu da hukumomin gwamnati.  Tsarin “Cashless” zai ci gaba da warware wannan matsalar iya gwargwadon yadda aka jajirce wajen ɗabbaƙa shi.

Sauƙin Cinikayya

A baya galibin cinikayya ana gudanar dasu ne ta amfani da takardun kuɗaɗe, amma a ƙarƙashin tsarin “Cashless” komai zai koma ta hanyar tiransfa – ko dai ta hanyar na’urar POS, ko biya kai tsaye a taskar ajiyar mai shago, ko ta amfani da shafukan Intanet na hukumomi don biyan kuɗaɗe kai tsaye a taskar gwamnati, kamar yadda ake amfani da shafin Remita wajen biyan kuɗaɗe a asusun hukumomin gwamnatin tarayya a yanzu.  Yawo da takardun kuɗi zai ragu, za a koma amfani da hanyar tiransfa, ko katin ATM, wajen biyan kuɗaɗe yayin saye da sayarwa.  Wannan wani ƙarin sauƙi ne ga ‘yan kasuwa.

Ƙarancin Haɗari da Hasarar Kuɗaɗe

A duk sadda gobara ta tashi a manyan kasuwanninmu akan samu hasarar kuɗaɗe masu ɗimbin yawa, ba wai na kayayyaki kaɗai ba.  Saboda galibin ‘yan kasuwa kan ajiye takardun kuɗaɗensu ne a shago.  Amma da zarar tsarin “Cashless” ya tabbata, in sha Allahu wannan matsala za ta ragu sosai.  Ba za ta kau ba gaba ɗaya, tunda ba za a taɓa rasa daina amfani da takardun kuɗi ba musamman wajen cinikayya.  Amma hatsarin zai ragu nesa ba kusa ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.