Tekun Atlantika, Da Albarkatun Da Ke Cikinsa (2)

A kashi na biyar, yau ma mun ci gaba da bincike ne kan tsarin tekun Atlantika, kamar yadda muka fara a makon jiya. Wannan teku akwai abubuwan mamaki a cikinsa jama’a. A sha karatu lafiya.

747

Wannan shi ne kashi na 5 cikin jerin kasidu masu taken: “Tekunan Duniya da Abubuwan da ke Cikinsu.”


Samuwar Tekun Atlantika

Binciken masana tarihi ya tabbatar da cewa Tekun Atlantika ne na biyu a tsufa daga cikin tekunan duniya gaba daya.  Abin da suke nufi da wannan shi ne, tsufa wajen ganowa a iya binciken masu bulaguro cikin teku, ba wai tsufa wajen halitta ba.  Domin, kamar yadda bayani ya gabata a baya, dukkan tekunan duniya asalinsu guda daya ne; teku ne daya da ya karkasu ta la’akari da nahiya ko tsibirai ko kuma wasu siffofi na musamman da suka kebance bangare da bigiren da yake.  Idan muka fahimci wannan bayani, cikin sauki za mu gane abin da suke nufi da cewa shi ne teku na biyu a tsufa a duniya.

Asalin wadanda suka fara gano samuwar wannan teku a duniya dai su ne masu bulaguron teku a zamanin farko daga kasashe ko daulolin Portugal da Spain, wadanda kasashe ne biyu da a halin yanzu suke cikin nahiyar Turai (Europe).  Hakan ya samu ne sanadiyyar bulaguron kasuwanci da suka fara yi daga nahiyarsu zuwa yammacin duniya, wato nahiyar da a halin yanzu kasar Amurka da Latin America suke kenan.  Bayan gano wannan teku da ya sadar dasu da nahiyar arewaci da kudancin amurka, daga nan aka fara samun bunkasar kasuwanci tsakanin nahiyar turai da amurka.  Babbar titin da ta sawwake hakan ita ce: Tekun Atlantika.  Domin a sannan babu jiragen sama, kuma babu inda mota za ta bi, idan ma akwai motocin kenan.  Abin safara a wancan lokaci shi ne jirgin ruwa; manya da kanana.  Wannan tsarin kasuwanci da ya bunkasa a tsakanin nahiyoyin biyu shi ake kira: “Transatlantic Trade.”

Binciken Kimiyya

Gano Tekun Atlantika a duniya ya zaburar da hukumomi da kasashe da ma wasu cibiyoyin binciken kimiyya musamman na teku, gudanar da bincike don tantance abubuwa da yanayin wannan mahalli.  Babban binciken kimiyyar teku na farko da aka fara gabatarwa a wannan teku na atlantika shi ne wanda kasar Ingila ta gudanar tsakanin shekarar 1872 zuwa 1876; tsawon shekaru hudu kenan.  Ta gudanar da wannan bincike ne a kan wani babban jirgin ruwa irin na wancan zamani mai suna: “HMS Challenger.”  Daga nan kuma aka sanya wa wannan shirin bincike suna: “The Challenger.”  Wannan bincike na kimiyya ya fara ne ya kuma kare duk a cikin Tekun Atlantika.

Daga shekarar 1925 zuwa 1927 sai kasar Jamus ita ma ta leko cikin tekun.  Bincikenta ya ta’allaka ne ga bangaren Kudancin tekun na atlantika, na tsawon shekaru biyu.  Wannan shirin bincike ta sa masa suna: “German Meteor Expedition.”  Bulaguro ne na binciken kimiyya da ya shafi bangaren Kudancin tekun kadai.  Cikin shekarar 1949 kuma sai Jami’ar Kolombiya dake kasar Amurka ta shirya nata binciken kan wannan teku.  Wannan bincike an gudanar dashi ne karkashin wata cibiyar binciken kimiyya dake jami’ar mai suna:  “Lamont-Doherty Earth Observatory.”  Cibiya ce dake gudanar da bincike kan dukkan abin da ya shafi kasa, da teku da abubuwan dake kansu na halittar Ubangiji.

Bincike na karshe shahararre da za mu dakata a kanshi shi ne wanda hukumar Lura da Tekuna da Yanayi na kasar Amurka ta gudanar.  Wannan hukuma ita ce: “United States Hydrographic Office.”  Ita ma ta gudanar da bincike na musamman kan Tekun Atlantika.

Shahararrun Buloguro

Tekun Atlantika teku ne da ya dara sauran tekuna samun masu bulaguro a cikinsa; ko dai na kasuwanci, ko bincike, ko yawon bude ido, ko na kuru, ko kuma don ganin ido. Farin wata ne, sha-kallo.  Wannan ba abin mamaki bane idan muka yi la’akari da bigiren da yake.  Teku ne da ya hade manyan nahiyoyin duniya uku musamman; ya hade nahiyar Turai da Amurka, domin a tsakaninsu yake kai tsaye.  Ya hade nahiyar Asiya da Afirka da Latin Amerika, ta bangaren Kudanci kenan.  Domin daga Kudancin Amurka kana iya shigowa Yammacin Afirka, daga nan kuma ka dire a Tekun Indiya ko Tekun Maliya, kamar yadda muke ambatonsa, wanda kai tsaye zai sadar da kai da nahiyar Asiya da gabashin duniya.  Idan ka koma makurar arewacin turai ma haka lamarin yake.  Tekun Atlantika ya hade da Tekun Aktik.

Wannan dalili yasa aka samu masu bulaguro da dama, musamman tun a zamanin baya har zuwa wannan lokaci da muke ciki.  A tsakanin shekara ta 600 – 400 kafin zuwan Annabi Isa (amincin Allah ya kara tabbata a gare shi), tarihi ya hakaito mana cewa babban mai bulaguron teku a wancan lokaci mai suna: “Hanno the Navigator” ya kutsa cikin Tekun Atlantika, inda ya dangana zuwa Yammacin Afirka, daga can kuma ya nausa zuwa daidai bigiren Kambun duniya (Equator).  Hanno dai shahararren mai bulaguron teku ne a wancan zamani.

Daga shekarar 980 zuwa 982 bayan daukaka Annabi Isa (AS) kuma, mai bulaguro Enrik, wanda aka fi sani da lakabin: “Enrik the Red,” shi ma ya ketara Tekun Atlantika.  Shi ne wanda ya gano tsibirin Greenland, tare da wani bangaren Kudanci da Arewacin Amurka (South and North America).  Ana shiga shekara ta 1000 kuma sai dansa mai suna Leif Ericson ya gaji sana’ar mahaifinsa, inda ya zama mutum na farko da ya fara taka kasar gabar gabashin Kanada a yau.  Da Enrik da dansa Leif dai, dukkansu ‘yan asalin kasar Norway ne, duk da cewa sun bar kasar, inda suka ci gaba da zama a duk kasar da suka bude ko suka kafa, har mutuwarsu.

Masu bulaguron teku na kasar Portugal ma sun keta Tekun Atlantika daga shekarar 1419 zuwa 1427, kuma su ne farkon wadanda suka gano kasar Madeira da Azores dake kasar Meziko a yau.  Kafin wannan bulaguro dai har wa yau, tarihi ya sake hakaito mana cewa wata bataliya ta masu bulaguro daga kasar Portugal din dai har wa yau, ta taso a shekarar 1415, inda suka nausa cikin Tekun Atlantika suka doshi  bigiren Yammacin Afirka, daga can suka tsallaka kambun duniya, suka tike a Tekun Indiya (Tekun Maliya).  Basu karasa tekun maliya ba sai cikin shekarar 1488.

Shekaru hudu bayan wannan bulaguro nasu, cikin shekarar 1492 sai Christopher Columbus yayi tasa bulaguron, inda ya tsallaka Tekun Atlantika daga Daular Spain dake gabashi, zuwa yammaci, har a karshe ya dire a wani bigiren kasar Amurka da a yanzu ake kira da suna: “Bahamas.”  Christopher Columbus dai shi ne wanda ya gano kasar Amurka ta yau, cikin wannan bulaguro da yayi a shekarar 1492.  A wancan lokaci ya sa mata suna: “New World,” kuma duk da cewa dan kasar Italiya ne shi, Sarauniyar Spain ce ta dauki nauyin wannan tafiya tasa.  Bayan wannan bulaguro ma, ya sake yin wasu zubi uku a lokaci daban-daban.

- Adv -

Bayan bulaguron Tekun Atlantika da ya haddasa gano kasar Amurka ta yau a wancan lokaci, cikin shekarar 1496, John Cabot, wani matafiyi mai zafi, shi ma ya keta ruwa cikin bulaguro zubi uku; daga birnin Bristol zuwa Arewacin Amurka.  Shekaru biyu bayan tasa bulaguron, sai Pedro Alvares Cabral ya kutsa Tekun Atlantika shi ma, inda tafiyarsa ta tike dashi a kasar Burazil ta yau. Wannan ya faru ne a shekarar 1500.  A cikin shekarar 1519 kuma sai matafiyi mai bulaguro Ferdinand Magellan ya ketara Tekun Atlantika daga Daular Spain dake gabashin tekun, ya nausa Kudancinsa, har a karshe ya dangana da babban tekun duniya, wato: Pacific Ocean.

A shekarar 1858 sai lamarin ya canza salo.  Daga bulaguron bude ido ko ganin ikon Allah, zuwa samar da hanyoyin sadarwa.  Cikin wannan shekara ne Cyrus West Field ya shimfida wayar kebul, don aiwatar da sadarwa ta amfani da na’urar Telegraph.  Shi ne mutum na farko da ya fara shimfida wannan waya a karkashin Tekun Atlantika da wannan manufa.  Wannan yunkuri na cikin abubuwan da suka taimaka wajen habbaka tsari da hanyoyin sadarwa na zamani a zamunnan baya, kafin wannan lokaci.

Daga cikin bulaguron da suka ajiye tarihi a Tekun Atlantika har wa yau, akwai yunkurin da wani babban jirgin ruwa mai suna: “RMS Titanic” yayi, inda ya taso daga kasar Ingila ya nufaci kasar Amurka, amma kafin tafiya tayi nisa, yaci karo da wani tsaunin kankara, wanda sanadiyyar haka ne ya huje, ruwa ya cike jirgin daga kasa ba tare da sanin matukansa ba, har a karshe dai ya sulmuya tare da hallakar da mutane sama da 1,500.  Wannan lamari ya faru ne a ranar 15 ga watan Afrailu, shekarar 1912.  Na san masu karatu sun san kadan daga cikin tarihin wannan lamari, musamman ganin cewa akwai fim na musamman da aka shirya mai suna: “Titanic” a shekarar 1997, daidai lokacin da lamarin ya cika shekara 85 da aukuwa kenan.

Da yawa cikin matasa na ganin jigon wannan fim ne a bangaren soyayya kadai.  Sai dai babban jigon shirin shi ne kokarin tabbatar da girma da abin al’ajabin da ya faru da wannan jirgi.  Domin jirgi ne da kafin gina shi, ba a taba samun jirgin ruwa mai girma irinsa ba.  Amma sai ga shi ya ci karo da tsaunin kankara dake karkashin teku, har ya sulmuya.  Abu na biyu shi ne, lamarin gaba dayansa ya auku ne a Tekun Atlantika, a wani yunkuri na ketare tekun ta amfani da wannan babban jirgin ruwa.  Wanda da ace hakan ya yiwu, da ya zama babban abin tarihi fiye da na baya, kan abin da ya shafi ketare Tekun Atlantika.  Amma sai  dai kash, ba haka Allah ya tsara kuma yaso ba.

Cikin watan Mayu na shekarar 1915, ranar 7 ga wata kenan, wani katon jirgin ruwa mai suna: “RMS Lusitania” shi ma, ya yi yunkurin ketare Tekun Atlantika a hanyarsa ta zuwa kasar Ireland.  Amma ya hadu da hadarin yaki, inda wani makamin mizail na karkashin teku ya harbe shi kai tsaye; mutum 1,198 ne suka rasa rayukansu.  Wannan bulaguro bai kai ga gaci ba.  Amma lamarin gaba daya ya auku ne a kan Tekun Atlantika.

Daga cikin yunkurin kerare Tekun Atlantika da tarihi ya taskance mana akwai wani shahararren atisayen jiragen ruwan yaki don shirya wa yakin duniya na daya.  Wannan atisaye ya faru ne tsakanin shekarun 1914 zuwa 1918.  Wannan atisaye da aka gudanar a Tekun Atlantika ya haifar da hadari mai girman gaske, inda jiragen ruwan yaki guda 2,100 suka nitse, sannan kananan kwale-kwalen yaki guda 53 suka hallaka.

A shekarar 1919 kuma sai ga wani yunkuri na tsallaka Tekun Atlantika daga kasar Amurka.  An gudanar da wannan bulaguro ne da wani nau’in jirgin saman ruwa, wato: Seaplane na kasar Amurka mai suna: NC-4.  Da wannan jirgi aka yi nasarar tsallaka Tekun.  Kuma shi ne nau’in jirgin ruwan sama na farko a duniya da ya tsallaka Tekun Atlantika a tarihin tekun.  Wadanda suka tsallaka tekun da wannan jirgi sun yi haka ne a shekarar 1919, kamar yadda ya gabata.  A shekarar 1927 kuma sai wani shahararren matukin jirgin sama mai suna: Charles Lindbergh, shi kadai, ba tare da wani abokin rakiya ba, ya tsallaka Tekun Atlantika daga farko har zuwa karshensa, ba tare da ya yi Zango a wani wuri ba.  Charles ya taso ne tun daga birnin Paris na kasar Faransa, ya dire a birnin New York na kasar Amurka, bayan tsallako tekun gaba dayansa.  Shi ne na farko a duniya da ya fara tsallaka tekun ba tare da abokin rakiya ba kuma ba tare da yin Zango a ko ina ba.

A shekarar 1932 sai bulaguro cikin Tekun Atlantika ya canza salo, daga mazaje masu jaruntar tuki ko sarrafa jiragen ruwa, zuwa mata masu kama da maza.  Mace ta farko da ta fara tsallaka Tekun Atlantika ita kadai ba tare da aboki ko abokiyar rakiya ba ita ce: Amelia Earhart.  Wannan mace mai kamar maza ta taso ne tun daga tsibirin kasar Kanada mai suna: Newfoundland, inda ta tike da Arewacin kasar Ireland dake nahiyar Turai.

Daga cikin bulaguro da aka yi amma da manufar yaki, akwai wanda ya auku tsakanin shekararun 1939 – 1945, wanda ya zama wani bangare na Yakin Duniya na biyu.  Wannan yaki da aka yi shi a cikin Tekun Atlantika tsakanin wadannan shekaru, ya haifar da nitsewar jiragen ruwan yaki guda 3,700.  Tirkashi!

A shekarar 1952 kuma sai ga wata macen mai suna: Ann Davidson wacce ita ma, kamar yar uwarta Amelia, ta tsallaka tekun ita kadai a jirgin ruwa.  Ann Davidson ta zama ta biyu wajen jarunta a wannan fanni ko bangare, a tarihin masu bulaguro cikin Tekun Atlantika.

Ana shiga shekarar 1984, sai ga wani jarumi mai suna Amyr Klink, wanda ya tsallaka Tekun Atlantika cikin kwanaki 100, ta amfani da kwale-kwale, shi ma shi kadai.  Klink ya faro bulaguronsa ne daga bakin gabar Tekun Atlantika dake kasar Namibiya, ya tike a bakin gabar dake kasar Burazil.  A kwale-kwale.  Shi kadai.  Cikin kwanaki 100.  Lallai ya sha sanyi.

Bayan shekaru 10 (a shekarar 1994), sai ga Guy Delage, shahararren dan ninkaya a cikin teku, ya tsallaka Tekun Atlantika da ninkaya.  Babban magana!  Guy Delage dai shi kadai ne yayi wannan kuru, ta amfani da jirgin ruwan fito, inda ya taso daga tsibirin Cape Verde zuwa tsibirin Barbados dake nahiyar Karibiyan (da jirgin ruwan fito).  Daga nan ya ajiye jirgin ruwan fiton, ya fara ninkaya daga tsibirin/garin Benoit Lecomte, har ya tsallaka Tekun Atlantika da ninkaya.  Sau daya kawai yayi Zango na kwanaki 10 a tsibirin Azores.  Wannan bawan Allah ya ciri tura cikin masu bulaguro a Tekun Atlantika, sanadiyyar amfani da ninkaya wajen tsallakawa.  Wata jarumtar sai da sayar da rai.

A shekarar 1999 kuma sai ga wata macen kuma mai suna: Tori Murden, wacce ta tsallaka Tekun Atlantika ta amfani da jirgin kwale-kwale, cikin kwanaki 81.  Masu kididdiga suka ce ta ci tazarar kilomita 4,767 ne a wannan bulaguro nata, daidai da tazarar mil 2,962 kenan.  Malama Tori ta fara bulaguronta ne daga bakin gabar tekun dake Gualdeloupe, inda ta tike a tsibirin Canary (Canary Islands).  Tirkashi!

Da zamani ya kara gaba, aka samu karin hikimomi cikin fasahar kere-kere, sai ga wani jarumi mai suna: Alan Priddy, tare da ‘yan rakiyarsa guda uku, ya tsallaka Tekun Atlantika ta bangaren arewaci (North Atlantic Ocean), cikin sa’o’i 103, wato cikin kwanaki 4 kenan!  Ba wannan bane kadai abin mamaki, Alan ya yi wannan tafiya ne ko bulaguro ta amfani da jirgin ruwan roba irin ta zamani mai suna: Rigid-hulled Inflatable Boat (RIB), inda ya taso daga tsibirin kasar kanada dake bakin gabar tekun mai suna: Newfoundland, ya ratsa ta tsibirin Greenland, inda a karshe ya tike a kasar Scotland.  Duk wannan cikin kwanaki hudu.  Wannan, a binciken malaman tarihi, na nuna shi ne wanda ya tsallaka Tekun Atlantika cikin mafi karancin lokaci, ta amfani da abin hawa mafi hadari.  Wannan lamari ya faru ne a shekarar 2003.

Wadannan, a babin takaitawa, su ne kadan daga cikin wadanda suka kutsa Tekun Atlantika da nufin bulaguro ko wata bukata ta musamman, a tarihin tekun a duniya.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Ukashatu Husaini says

    We really appreciate the efforts may Allah grant you the ability to maintain the quality of being reliable in any matter at any time,and any place.

Leave A Reply

Your email address will not be published.