Sakonnin Masu Karatu (2014) (18)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

62

Salaamun alaikum Baban Sadik, barka da warhaka, da fatan ka wuni lafiya.  Allah ya saka da alheri, amin.  A gaskiya ina matukar karuwa da kasidun da kake rubutawa a jaridar AMINIYA.  Allah ya saka maka da alherinsa, ya kara maka basira, amin.  – Salahuddeen Auwalu Rijiyar Lemu, Kano.

Wa alaikumus salam, ina godiya matuka Malam Salahuddeen, Allah ya saka maka da alheri kaima, ya kuma inganta mu baki daya, amin.


Assalamu alaikum, da fatan kana cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin.  Don Allah Baban Sadik ina son ayi mini bayanin yadda zan yi amfani da makalutun sadarwa na Intanet, wato Internet Modem. – Usman Adamu Gumel, Jigawa.

Wa alaikumus salam, barka Malam Usman.  Da farko dai, idan ka siyo Makalutun Sadarwar (Modem), sai ka jona wa kwamfutarka.  Idan ta hange shi, za ta sanar dakai cewa, sai kaje shiga “Computer” ko “My Computer,” za ka ga alamar ma’adanar filash dake dauke da makalutun sadarwar, sai ka matsa.  Nan take kwamfutarka za ta loda shi a kanta kai tsaye, wato “Install” kenan.  Idan ta gama, za ka ga alamar masarrafar a kan shafin kwamfutarka.  Duk sadda ka tashi amfani da makalutun sadarwar, sai ka shigar wa kwamfutarka shi, da zarar ta hango, za ta budo maka shafi.  Sai ka matsa inda aka rubuta: “Connect”, ka ci gaba da yawo a duniyar gira-gizai.

Idan kudin kati ya kare, za a sanar dakai.  Domin akwai katin SIM  a cikin makalutun da aka baka sadda kaje saya.  Kana iya cire katin, ka sa wayarka sannan ka loda kudi, ka sayi “Data”, wato damar da za a baka wajen yawo a Intanet kenan.  Idan kuma za ka saba mu’amala da manhajar kwamfuta, a jikin shafin makalutun Intanet din ma kana iya loda kati, ka sayi “Data” abun ba wuya, wai cire wando ta ka!  Allah sa a dace, amin.


Assalaamu alaikum, barka da asuba. Don Allah ina neman shawara ne dangane da wayoyin nan guda biyu; HTC Android, da Nokia Lumia 520 ko 625.  Don Allah Malam wacce tafi inganci ne a tsakaninsu?  A taimaka mini da shawara kan wacce zan saya.  Da yardar Allah zan bi shawararka.  Allah ya taimaki Malam! – 08065750790

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Baka fadi nau’in HTC din ba, domin kalmar “HTC” sunan kamfanin dake kera wayoyin salula ne.  Akwai nau’ukan wayoyi da dama da ya kera.  Duk haka, galibinsu suna dauke ne da babbar manhajar Windows, wasunsu kuma na dauke babbar manhajar Android.  Wani abu guda dake bambance wayoyin HTC da sauran wayoyi shi ne, suna da masarrafai na musamman da kamfanin HTC ke sanya musu, wadanda kuma ba ka iya samunsu a kowace waya.  Bayan haka, suna da kara wajen sauti, sannan gangar jikinsu (Hardware) na da karko sosai. Abu na karshe shi ne, suna da kyau matuka.  Domin tsarin kirarsu ya sha bamban da na wayoyin salula gama-gari.  Shi yasa ma suke da dan karen tsada.

- Adv -

A daya bangaren kuma, wayoyin salula nau’in Lumia na kamfanin Nokia ne asali, amma yanzu kamfanin Microsoft ya saye kamfanin ko ince bangaren wayoyin salula na Nokia gaba daya, kuma cikin watan da ya gabata (Afrailu) ne ya karbi wayoyin Nokia gaba.  Nan gaba yace zai canza musu suna.  A takaice dai nau’ukan wayoyin Lumia suna dauke ne da babbar manhajar Windows Phone na kamfanin Microsoft, kuma su ma suna da inganci.  Ba nan kadai ba, suna dauke ne da hanyoyin sarrafa waya da suka sha bamban da sauran wayoyi.  Babu wani bambanci mai nisa tsakanin Lumia 525 da Lumia 625, sai na fadin fuska, da tsawon jiki, sai ‘yan kannan bambance-bambance a bangaren masarrafa da ba a rasa ba.

Idan kana neman saukin sarrafawa ne da samun masarrafai na kyauta cikin sauki, kana iya neman HTC mai dauke da babbar manhajar Android. Idan kuma kana bukatar kariyar bayanai ne, amma tare da jure tsaurin hanyoyin mu’amala, sai ka sayi Lumia 625, don ita ce gaba da Lumia 525.  Allah sa a dace.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Don Allah ina son kayi mini bayani ne kan “Wi-Fi” da yadda ake amfani dashi.  Na gode.  – Mudassir Abdulkadir, Kantin Sauki, Gusau.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdulkadir.  “Wi-Fi” manhaja ce dake taimakawa wajen hada wayar salula ko kwamfuta da yanayin sadarwa na Intanet a inda mai wayar ko kwamfutar yake.  Idan wannan masarrafa a kunne take, da zarar ka zo inda yanayin sadarwa na Intanet yake (wato “Wireless Connections”) nan take wayar za ta hango su.  Idan na kyauta ne kana iya amfani dasu ta hanyar latsa kowanne daga cikinsu, sai kaje “Connect” ka matsa, wayar za ta jonu da wannan yanayin sadarwa, har ka iya mu’amala da Intanet a wajen.  Amma kuma da zarar ka bar wurin wannan yanayi na sadarwa zai dauke.  Kamar tsarin sadarwar wayar salula ne.  Kana iya kira ko amsa kira ne a wurin da akwai yanayin sadarwa (Network Connection), amma idan ka bar wurin shikenan, sai a yanke ka.

Idan kuma yanayin sadarwar dake wurin kaje tsararre ne (Secured Connection), dole sai an shigar maka da kalmar shiga, wanda babu mai saninsu kuwa sai wadanda sukia mallaki yanayin sadarwar.   Da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum Baban Sadik da fatan kuna lafiya.  Idan nasa wani “Removable disk” a laptop di na sai duk abin da ke ciki ya koma kamar “Shortcut.”  Kuma idan na mayar cikin waya sai yaki yi.  Hakan na nuna kwamfutar na dauke da “Virus” kenan?  –  Abubakar Tafiyau, Tudun Wada, Kaduna.

Wa alaikumus salam, Malam Abubakar barka da warhaka.  Lallai akwai tabbacin hakan.  A ka’ida ya kamata idan ka sanya ma’adanar shigar da bayanai, nan take ka riski dukkan bayanan dake ciki ne, kai tsaye.  Amma ganin alamar “Shortcut” dalili ne dake nuna cewa da matsala, musamman ganin cewa idan ka mayar cikin waya sai komai ya bace.  Dayan biyu; ko dai kwayoyin cutar kwamfutar a wayarka suke, ko a cikin kwamfutar da ka sanya daga baya.

Don haka idan kana da masarrafar tace bayanai (Anti-virus) kana iya zaburar da ita don ta tace maka dukkan kwamacalar dake cikin kwamfutar don gano su.  Kana iya barin ma’adanar bayanan a cikin kwamfutar don ita ma a tace ta.  Ta yiwu idan matsalar ba mai girma bace, ka ga an dawo maka da bayanan dake cikin ma’adanar.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.