Kamfanin Nokia Ya Sayi Babbar Manhajar “Symbian”

Babbar manhajar wayar salula mai suna “Symbian” ita ce ke gudanuwa a kusan dukkan wayoyin salula na wannan zamani (shekara ta 2008), kuma dukkan kamfanonin kera wayoyin salula suna da lasisin amfani da ita a wayoyinsu. Bayanan dake fitowa daga kamfanin Nokia a halin yanzu shi ne, ya saye kamfanin Symbian gaba daya. Masana na ganin wannan wani kalubale ne ga sauran kamfanonin kera wayoyin salula dake gogayya da Nokia. A sha karatu lafiya.

Karin Bayani...

Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (4)

Idan masu karatu na tare damu, bamu gushe ba wajen kawo hujjoji daga Kur’ani kan ittifakin da ke tsakanin malaman kimiyyar sararin samaniya da na halittu kan gaskiyar abin da ke cikin Kur’ani wanda ya shafi kwarewa da ilimin da suke karantarwa.  A yau zamu sake dulmuya don ci gaba.  A mako mai zuwa kuma zamu yi bankwana, saboda abin da yawa, wai maye ya shiga kasuwa. A yau zamu koma kan tsarin samar da halitta ne.  Ga abin da suka ce nan:

Karin Bayani...