Manyan Fasahohi 5 Masu Tasiri a Duniya Waɗanda Har Yanzu Galibin Mutane Basu Fahimci Haƙiƙaninsu Ba a Aikace (3)

A taƙaice dai, wannan sabuwar duniya ta Metaverse na kan haɓaka ne.  Kuma ana sa ran nan da shekaru 10 masu zuwa, komai zai kankama. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 3 ga watan Fabrairu, 2023.

158

Fasahar Metaverse dai ba wata fasaha ce a zahirin rayuwa ba, kuma ba wani mahalli bane dake wajen wannan duniyar tamu.  A a.  Nau’in mahalli ne da ake samar dashi a giza-gizan sadarwa na zamani.  Kamar yadda kake iya hawa shafin Intanet ta amfani da adireshi shafin, har ka iya ma’amala da mutane ta hanyar bidiyo ko sauti ko rubutattun saƙonni, haka ma wannan fasaha ta Metaverse ake shiganta, amma ba ta hanyar adireshin Imel kaɗai ba, ta amfani da na’urar tabarau na sadarwa, wanda kowane kamfani yana da irin nasa.  Na kamfanin Google ana kiransa Oculus.

A wannan duniya ta Metaverse, akwai “garuruwa”, da “ƙauyuka”, da “kasuwanni” a misali, waɗanda aka gina su akan filaye ko fuloti, kamar dai yadda muke sayan filaye a zahirin rayuwa don gina shaguna da gidaje da mahallin kasuwanci.  Sannan kamfanoni na iya gina wuraren tarurruka, da ofisoshi, da masana’antu.  Kai hatta gidaje ana ginawa a ciki.  Kana iya gayyatar abokinka, yayi amfani da adireshin gayyatar da ka masa bayan ya ɗora tabaransa, ya ziyarci gidanka, ku zauna kana ganinsa yana ganinka, kana taɓa jikinsa yana taɓa naka; kuna hira kuna nishaɗi, har kuci kuma ku sha, idan kun so, duk a wannan duniya ta Metaverse.

- Adv -

Dangane da wuraren kasuwanci da masanan’antu, akwai shaguna maƙare da kayayyaki kana gani.  Idan wuraren tarurruka ne, kana akwai tebura da na’urorin sauti da kofunan shayi da duk abin da ake buƙata a wurin, cikin sauƙi.  Haka idan wuraren shaƙatawa ne, akwai gidajen rawa, da gidajen holewa ga masu sha’awan hakan.  Idan ka shiga wajen ma za ka yi kaciɓis da sauran mutanen da su ma suka je don shaƙatawa.  A taƙaice dai, mahalli ne mai kama da irin mahallin da muke rayuwa a ciki a zahirin rayuwa, don gudanar da abubuwan da aka saba gabatarwa a zahirin rayuwa.  Amma kuma, ta yaya ake mallaka da kuma shiga wannan sabuwar duniya ne ta Metaverse?

Kamar yadda na sanar a baya, akwai kamfanoni dake gina waɗannan mahallai, daga cikinsu akwai kamfanin Microsoft, da Google, da Apple, da kuma Facebook ko Meta.  Idan kana buƙata, akwai na’urar tabarau da zaka saya a wajensu, sannan za ka sayi fili ko fuloti, idan mahallin kasuwanci kake son mallaka, sannan za ka musu bayanin yadda kake son shagon ko gidan ko ofishin ya kasance, don su gina maka, ko ka gina da kanka.  A halin yanzu ma akwai kamfanonin da suka sayi filaye a duniyar Metaverse, har sun fara gina shaguna da ofisoshi.  Sai dai babu jama’a a duniyar har yanzu.

A taƙaice dai, wannan sabuwar duniya ta Metaverse na kan haɓaka ne.  Kuma ana sa ran nan da shekaru 10 masu zuwa, komai zai kankama.  Galibin hada-hadar kasuwanci da ayyukan kamfanoni musamman a ƙasashen da suka ci gaba  a fannin tattalin arziƙi, duk za su koma kan wannan duniya ne.  Manufar ita ce, don samar da aminci, da nagartar sadarwa, da kuma sirri daga ‘yan dandatsa.  Fahimtar yadda dukkan waɗannan tsare-tsare za su kasance a aikace ba ƙaramin aiki bane.  Sai lamarin ya kankama a aikace sannan mutane zasu fahimci haƙiƙanin yadda wannan fasaha take.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.