Fasahar “SMS”: Shekaru 30 Bayan Ƙirƙira (3)

A nan gida Najeriya ma mun ga tasirin wannan fasaha. A farkon bayyanar wayar salula jama’a sun fuskanci caji mai yawa wajen aikawa da karɓan sakonni tes a wayoyinsu.  Amma daga baya hukumomin sadarwar ƙasarmu sun yi tsayin dake wajen ganin an daidaita farashin kira da kuma aikawa da saƙonnin tes.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 23 ga watan Disamba, 2022.

152

Fasahar SMS a Zamanin Yau

Bayan shekaru 30 da samar da wannan fasaha, ci gaban da aka samu a fannin fasahar sadarwar wayar salula da kwamfuta da Intanet, duk sun shafi fasahar saƙon tes kai tsaye.  A shekarar 2020 an tabbatar da cewa babu wannan fasaha ta SMS ce aka fi amfani da ita wajen aiwatar sadarwa; ya Allah ga ɗaiɗaikun jama’a ne, ko hukumomi ko kuma kamfanoni.  Kamfanonin kasuwanci musamman, sun fi kowa amfani da wannan fasaha ta SMS.

Daga cikin manyan dalilan dake nuna shaharar wannan fasaha da bunƙasarta,  akwai yawan amfani da ita da ake yi, ta la’akari da adadin saƙonnin da ake aikawa ko karɓa a duk yini ko daƙiƙa – mafi ƙarancin lokaci cikin sa’annin yini – da kuma shekara.  Misali, a Ƙididdigar bayanai sun tabbatar da cewa a shekarar 2021 kaɗai anyi musayar saƙonnin tes wajen tiriliyon biyu da biliyan ɗari (2.1 tr).  Abin da ke tabbatar da cewa a duk yini a ƙalla ana aikawa da karɓan saƙonnin da ba su gaza biliyan ashirin da uku (23 bil).  A duk daƙiƙa (second) ɗaya kuma mutane na musayar saƙonni a ƙalla dubu ɗari biyu da saba’in (270,000).

Cikin adadin mutane sama da biliyan takwas da duniya ke ɗauke dasu, alƙaluman bayanai sun tabbatar da cewa sama da mutum biliyan biyar ne ke amfani da wannan fasaha ta saƙon tes a duniyar yau.  Wannan bazai ba mai karatu mamaki ba, musamman idan muka yi la’akari da cewa cikin kashi 100 na mutanen dake duniya, kashi 83.72 sun mallaki wayar salula.  Duk da ci gaba da haɓakar da aka samu a fannin fasahar Imel, fasahar saƙon tes na gaba da ita wajen yawan masu amfani, da kuma hanyoyin amfani.

Taƙaitaccen misali zai tabbatar mana da hakan.  Aika saƙon tes ba ya buƙatar samuwar siginar Intanet a wayar salula.  Haka ma, ko ba ka ko sisi kana iya karɓan saƙon tes a wayarka.  Aikawa ne dai ba za ka iya ba, sai kana da kuɗi a kan layinka.  Amma a ɗaya ɓangaren, ba ka iya aika saƙon Imel sai da Intanet a kan wayarka.  Haka ma karɓa; dole sai kana da siginar Intanet a kan wayarka.  Sannan hatta ta ɓangaren karɓa; mutane sun fi buɗe saƙon tes idan ka haɗa da masu buɗe saƙon Imel.  Dalili?  Muddin wayarka na kunne, nan take saƙon zai shigo, kuma za ka ji shigansa.  Amma idan saƙon Imel ne, sai ka kunna datar wayarka saƙon zai shigo.  Alƙaluman masu bincike sun tabbatar da cewa, cikin kashi 100 na masu karɓan saƙon tes a wayarsu, kashi 98 na buɗewa su ga me aka turo musu.  Dalilin hakan shi kuma, shi ne, malaman ɗabi’a suka ce a duk yini, mutane kan buɗe fuskar wayarsu (don ganin me aka aiko musu, ko don kira, ko amsa kira, ko aika saƙo dsr) a ƙalla sau 58!

Saƙon tes na da sauƙin rubutawa da aikawa.  Wanda ya rubuta saƙon tes (haruffa 160) cikin mafi ƙarancin lokaci shi ne wani matashi ɗan ƙasar Norwey mai suna Frode Ness a shekarar 2012.  Shi ne ya rubuta saƙon tes cikin daƙiƙu 34.65; wato ƙasa da rabin minti guda kenan!  Wannan yasa aka shigar da sunansa cikin littafin masu bajinta na Guesness a duniya (Guiness Book of Records).  Sannan har wa yau an tabbatar da cewa mata sun fi maza yawan amfani da fasahar saƙon tes a duniya baki ɗaya.

- Adv -

A ɗaya ɓangaren kuma, bincike ya tabbatar da cewa duk cikin fasahohin sadarwa na zamani, babu fasaha ko hanyar sadarwa mai ɗaukan hankali a wayar salula irin saƙonnin tes.  An tabbatar da cewa idan mutum ya buɗe saƙon tes yana karantawa, kashi 75 na hankalinsa kan koma kan saƙon ne gaba ɗaya.  Wannan yasa ma karantawa ko rubuta saƙon tes yayin da mutum ke tuƙi yafi komai haɗari.  An ƙara tabbatar da cewa, mai tuƙi yana karanta saƙon tes, ya fi saurin samun haɗari kan mai tuƙi cikin barasa da kashi 23.  Ma’ana, mutumin dake tuƙi yana karantawa ko rubuta saƙon tes, munin aikinsa wajen sabbaba haɗari ya fi na wanda ke tuƙi bayan ya bugu da barasa ko kayan maye.

Kammalawa

Wannan fasaha ta saƙon tes dai za ta ci gaba da haɓaka ne da kuma ƙara samun tagomashi.  Musamman ta la’akari da yadda kusan komai na rayuwa dake da alaƙa da hanya da na’urar sadarwa, bai rasa alaƙa da fasahar tes.  Misali, duk abin da za ka yi rajistansa a yau –  katin zabe ne, ko katin lasisin tuƙin mota, ko katin zama ɗan ƙasa, ko buɗe asusun ajiya a banki, ko aikawa da karɓan saƙonni daga banki – duk sai ka buƙaci fasahar saƙon tes.

Ba wannan kaɗai ba, hatta rajistan Imel, da yin rajista a kafafen sadarwa a Intanet, duk kana buƙatar fasahar SMS.  Domin ita ce hanya mafi sauƙi wajen tantance haƙiƙanin mutane ta tsarin OTP.  Wannan tsari ne bankuna ke amfani dashi a duk duniya.  Idan a yini za ka sayi kayayyaki sau ɗari ne a kafar sadarwa a Intanet, sai an aiko maka lambobin tantancewa (Verification Code) ta wayarka sau ɗari.  Waɗannan lambobi ne za ka shigar a shafin da kake rajista ko kake son sayan kayan, don bai wa bankin damar gane cewa lallai kai ne kake son biyan kuɗin ba wai wani bane ya sace wayarka yake son zambatarka.

Haka idan ka mance kalmar sirrinka na Facebook ko Instagram, ko Tiktok, ko Imel; duk ta hanyar SMS za a aiko maka lambobin tantancewa don baka damar canzawa.  A tare da cewa kana iya amfani da adireshin Imel a waɗannan kafafe, sai dai a galibin lokuta komai zai koma kan wayarka ne.

A nan gida Najeriya ma mun ga tasirin wannan fasaha. A farkon bayyanar wayar salula jama’a sun fuskanci caji mai yawa wajen aikawa da karɓan sakonni tes a wayoyinsu.  Amma daga baya hukumomin sadarwar ƙasarmu sun yi tsayin dake wajen ganin an daidaita farashin kira da kuma aikawa da saƙonnin tes.  A wasu ƙasashe, da kiran waya da amsa waya duk sai an cajeka.  Haka ma karɓa da aika saƙon tes.  Amma mu nan kira ƙadai ake caji, haka ma aikawa da saƙon tes kaɗai ake caji.  A halin yanzu kowane saƙon da bai wuce haruffa 160 ba, naira 4 ake cajanka.  Idan ya shiga ƙasa da haruffa 320 a cajeka naira 8. Idan kuma ya haura tsakanin haruffa 320 zuwa haruffa 480, a cajeka naira 12.

Daga bayanan da suka gabata za mu fahimci cewa lallai fasahar saƙon tes na cikin fasahohin da ci gaban zamani ya kasa kashe su, sai ma ƙara inganta su da yayi.  Kamar dai yadda ya kasance ga fasahar Imel.  Wannan ke tabbatar da cewa lallai samuwarsu ga al’umma alheri ne.  Saboda ɗimbin fa’idar da ake samu daga gare su ya fi cutarwar dake biyo baya.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Abubakar Adamu Muhd says

    Muna godiya Babana Allah ya saka maka da alkhairi, Allah ya qara basira.

    Nakai shekara 10 ina bibiyar rubutukanka, tunda na fara bibiyar rubutukanka har yau ba wanda ya ta6a tsallake ni.

    Na fa’idantu sosai da rubutukanka kuma na tasirantu dasu, ba abinda zance sedai Allah ya saka da alkhairi. Allah yasa wataran na hadu da kai, mu gaisa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.