Binciken Malaman Kimiyya Kan Tsibirin Bamuda (2)

A kashi na biyu cikin jerin binciken da muke yi kan tsibirin Bamuda, za mu dubi rubuce-rubuce da binciken da masana suka yi a baya ne kan wannan tsibiri, da irin abubuwan da suka hango.

2,336

Rubuce-Rubuce Kan Tsibirin Bamuda

Yawan faruwar ire-iren wadannan hadarurruka masu ban mamaki ya haifar da rubuce-rubuce daga masana da malaman jami’a da sauran masu sha’awar rubutu kan  abubuwan mamaki.  Wadannan rubuce-rubuce sun hada da kasidu da kuma littafai masu bayani iya gwargwadon fahimta ko binciken da suka yi.  Kasidar farko da ta fara bayyana, wacce kuma ta fara jawo hankulan mutane kan ire-iren wadannan hadarurruka ita ce wacce Mista E. Y. M. Jones ya rubuta ranar 16 ga watan Satumba, shekarar 1950.  Wannan kasida, wacce marubucinta ya yi bayani kan wannan wuri mai dauke da al’amuran mamaki, kamfanin dillacin labaru na Associated Press (AP) ne ya buga tare da yada ta, kuma ana kyautata zatpm cewa ita ce kasidar farko da ta fara bayani kan wannan wuri.  Shekaru biyu (1952) bayan rubuta wannan kasida, sai mujallar Fate Magazine ta buga wata kasida mai take: Sea Mystery at Our Backdoor, wacce George X. Sand ya rubuta.  A cikin wannan kasida ne ya kawo hadarin mamaki da ya samu tawagar jiragen sojin Amurka na Flight 19, da sauran jiragen sama da suka bace babu amo babu labari kafin shekarar 1952.  A cewar malaman tarihi, wannan marubuci ne ya fara kiran wannan kusurwa da suna: Bermuda Triangle.

Cikin shekarar 1962 kuma sai mujallar American Legion ta sake hakaito labarin hadarin jiragen Flight 19, bayan Mista George X. Sand kenan.  Ana nan kuma sai ga Mista Vincent Gaddis da kasida ta musamman shi ma, kan wannan kusurwa ta Bamuda.  Ya rubuta wannan kasida ne cikin shekarar 1964.  Taken kasidar kuwa shi ne: The Deadly Bermuda Triangle, kuma mujallar Argosy Magazine ce ta buga wannan kasida.  Shekara daya da rubuta wannan kasida, sai Mista Vincent ya kara bincike, inda ya mayar da wannan kasida zuwa littafi guda, ya kuma sa masa suna: Invisible Horizons.  A cikin wannan littafi, kamar wadanda suka gabace shi, ya koro bayanai ne kan hadarin Flight 19 da sauran hadarurrukan da suka shafi jiragen saman da suka bace babu labari.  Bayan wannan, cikin shekarar 1969 sai ga marubuci John Wallace Spencer da littafinsa mai suna Limbo of the Lost, wanda a ciki ya hakaito nasa labaran tare da fahimtarsa kan abinda ke faruwa a wannan mahalli mai ban mamaki.  Cikin shekarar 1974 ne kuma aka samu wani sabon littafi mai suna The Bermuda Triangle, na shahararren marubuci Charles Berlizt.  Kafin karshe wannan shekarar har wa yau an sake samun wani littafi kan wannan kusurwa mai suna The Devil’s Triangle, wanda Richard Winer ya rubuta.  Kuma shi ne ya fara kiran wannan kusurwa da sunan “Kusurwar Shedan”, ko The Devil’s Triangle”, domin taken da ya baiwa littafin da ya rubuta kenan a shekarar 1974.

Tun kasidar farko da aka fara rubutawa kan wannan kusurwa, kusan dukkan mahangar marubutar nahiya daya ta dosa.  Wannan nahiya kuwa ita ce nahiyar ta’ajjubi da mamaki, da kuma cewa wadannan hadarurruka da ke faruwa sun cancanci a jinjina musu wajen tsumar da duniya sanadiyyar faruwarsu.  Amma wanda ya fara kaddamar da bincike na kololuwa da bin kwakwaf, ya kuma saba wa sauran marubuta wajen mahangar abin da ke haddasa wadannan hadarurruka shi ne Farfesa Lawrence David Kusche.

- Adv -

Farfesa Lawrence malami ne a Jami’ar Arizona da ke kasar Amurka, kuma shi ne mutum na farko da ya fara kaddamar da bincike ta mahangar da ta sha bamban da ta wadanda suka gabace shi, cikin shekarar 1975.  A cikin littafinsa mai suna The Bermuda Triangle Mystery: Solved, ya bi diddigin dukkan labaran da aka yi ta bayarwa ne a baya, masu nuna cewa ba abin da ke haddasa wadannan hadarurruka illa aljanu da kuma wasu halittu da ke shigowa wannan duniya tamu daga wasu duniyoyin daban, wadanda ake kira Aliens.  Farfesa Lawrence a nashi bangaren ya kalubalanci ra’ayoyin da suka gabata ne, ta hanyar zuwa da wani sabon tsarin bincike da ke nuna cewa babu wani abin mamaki wajen wadannan hadarurruka da suka faru, kuma ma galibin labaran karairayi ne, wasu kuma an yi karin gishiri a cikinsu.  A karshe dai ya tabbatar da cewa duk labaran da ake bayarwa na faruwar wadannan hadarurruka, ire-irensu ko ma wadanda suka fi su zama abin mamaki sun faru a wasu bangarorin duniya, musamman ma a gabashin Asiya.  A tarihin wannan kusurwa ta shedan da ke tsibirin Bamuda, ana daukan wannan littafi na Farfesa Lawrence a matsayin wata sabuwar mahanga da ta sha bamban da mahangar baya, kamar yadda bayanai suka gabata.

A shekarar 1984 kuma sai ga wani marubucin da nashi binciken, wanda ya sanya wa suna The Evidence for the Bermuda Triangle.  Wannan marubuci dai shi ne David Group. Ya kuma yi tsokaci ne kan samuwar wadannan ababen mamaki da Farfesa Lawrence yake kokarin korewa a cikin littafinsa.  Bayan littafin David Group kuma sai ga Daniel Berg cikin shekarar 2000 da wani littafi shi ma kan wannan kusurwa da ire-iren ababen da a cewarsa sun tabbata kuma sun cancanci mamaki da al’ajabi.  Sunan wannan littafi shi ne: Bermuda Shipwrecks.  Littafin karshe da ya shahara kan wannan kusurwa na shedan shi ne wanda Gian J. Quasar ya rubuta cikin shekarar 2003.  Wannan littafi mai suna: Into the Bermuda Triangle: Pursuing the Truth Behind the World’s Greatest Mysteries, abin karatu ne sosaiKamar kundi ne da ya tattaro kusan galibin ra’ayoyi da kuma mahangar da marubutan baya suka tafi a kai.  Har wa yau, Mista Gian ya yi amfani ne da makaman bincike na kimiyyar zamani wajen nemo dalilan da suke haddasa bacewar jiragen sama da na ruwa.  Ya kawo dalilai da a cewarsa suna iya zama musabbabai wajen aukuwarsu, kamar yadda mai karatu zai karanta nan gaba.

A halin yanzu dai wadannan su ne shahararru kuma sanannun kasidu da littattafan da aka rubuta kan wadannan hadarurruka na mamaki da suke faruwa tsakanin tsibirin Bamuda da gabar Fulorida da na Puerto Rico.  Bayan littattafai da kasidu, akwai Fim guda daya da gidan talabijin UK Channel 4 ya gabatar mai take: The Bermuda Triangle cikin shekarar 1992.  Wanda ya shirya Fim din shi ne Mista John Simmons.  Kamar galibin littattafan da suka gabata, mahangar wannan shiri ko Fim shi ne “…akwai wasu halittu ko abubuwa boyayyu da ke haddasa wadannan hadarurruka.”  Wannan ya karkasa mahangar marubuta kan wannan kusurwa zuwa kashi uku, kamar yadda bayanai ke tafe a kai.

Wadannan ra’ayoyi gaba dayansu suna sassaba wa juna ne; babu dacewa da hadewa a tsakaninsu.  Bibiyarsu daya bayan daya ne zai taimaka wa mai karatu wajen fahimtar hakikanin abin da ke faruwa, ba wai don samun gaskiya a ra’ayi daya daga cikin wadannan ra’ayoyi mabanbanta ba.  Babban abin da ya haddasa hakan kuwa ba wani bane mai wahalar fahimta, domin shaharar wurin, da irin abubuwan da aka hakaito cewa sun faru ko suna faruwa, a baya ko a halin da ake ciki, da irin rubuce-rubucen da aka yi a baya da wadanda ake yi da wadanda ma nan gaba ba abin mamaki bane idan aka ce an samu wasu rubuce-rubuce.  A shashen da ke tafe mai karatu zai ga wadannan ra’ayoyi da masu ra’ayoyin, da kuma dalilan da suka sa suka dauki wadannan ra’ayoyi a matsayin matsaya na ilimi ko fahimta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.