Bincike Kan Bacci da Mafarki a Mahangar Kimiyya (6)

Wannan shi ne kashi na shida na kasidarmu kan bacci da mafarki a mahangar kimiyya. A sha karatu lafiya.

897

Matashiya

Idan mai karatu na tare damu cikin doguwar kasida mai shafuka 17 da muka gabatar  a baya mai take: Samuwar Bacci da Mafarki a Mahangar Kimiyya, na san bazai mance bayanan da suka zo tiryan-tiryan kan wannan maudu’i ba.  Bayan yabo da kirari da nayi wa Bacci, a kasidar na nuna yadda Malaman Kimiyya, cikin tsawon shekaru 50 da suka gabata, har zuwa zamanin yau, sun kasa gano meye hakikanin abin da ke haddasa wa dan adam shiga yanayin bacci.   Hakan kuwa ba abin mamaki bane da ya zama masu bincike sun kasa gano shi, domin bacci wani yanayi ne da ke da alaka ta kut-da-kut da rai.  Shi kuma rai, kamar yadda muka sani a al’adance da ma shari’ance, ba wanda ya san hakikaninsa sai Allah.  Don haka sai dai a sallama wa Allah lamarinsa kawai.  Amma ganin cewa galibin masu binciken ba musulmai bane, wasunsu ma basu yarda da samuwar Allah ba, shi yasa sallamawar ta gagara.  Har yanzu dai suna kan bincike, mu kuma muna biye dasu wajen sauraro da karanta abin da zasu gano nan gaba.

Har wa yau idan mai karatu bai mance ba, mun tsaya kan bayanai masu nuna alaka tsakanin bacci da ruhin dan adam ne, inda a karshe muka tabbatar da cewa gano lamarin bazai yiwu ba sai mun fahimci alakar dake tsakanin gangar-jikin dan adam (wato mahallin da bacci ke samuwa a jikinsa) da kuma ruhinsa, wanda shi ne Babbar Masarrafar jiki baki daya.  Mun bayyana wannan alaka har mataki biyar.  Daga nan muka je hutu.  A yau in Allah yaso za mu ci gaba ta hanyar duba wani abu na musamman dake faruwa ko aukuwa a cikin bacci.  Wannan abu kuwa shi ne mafarki.

Mafarki… Mafarki… Mafarki!!!

Daga cikin abubuwan da ke aukuwa a cikin bacci akwai mafarki.  To mene ne mafarki?  Shi mafarki wani yanayi ne dake aukuwa ta hanyar kwakwalwa da ruhin dan adam a yayin da yake bacci, mai dauke da aukuwar al’amura irin wadanda ke faruwa a rayuwarsa ta farke, ko wadanda faruwarsu bazai taba yiwuwa ba, ko kuma wani umarni ko hani daga Allah zuwa ga bayinsa (wato Annabawa da Manzanni kenan).  Wannan ke nuna mana cewa a cikin mafarki dan adam na iya gani ko samun kansa yana gudanar da wasu al’amura irin wadanda ya saba gudanarwa a rayuwarsa ta yau da gobe; wadanda ya san sun faru a baya, ko za su faru nan gaba, masu firgitarwa ko masu faranta rai.  Nau’in al’amari na biyu shi ne ganin kansa yana gudanar da wasu al’amuran rayuwa wadanda a hankali ko a al’adance ba za su taba faruwa ba. Wannan nau’in kawalwalniya kenan, wato “mirage.”  Nau’i na uku kuma shi ne nau’in umarni ko hani ta hanyar sako daga Ubangiji zuwa ga bayinsa.  Wannan bangare ko nau’i na karshe yana aukuwa ga Annabawa ne ko Manzanni kadai.  Kuma kamar yadda gaibin Malaman muslunci suka tabbatar, ya yanke, tunda babu wani Annabi ko Manzo da zai zo nan gaba, kuma har a masa wahayi.  Domin shi mafarki wata hanya ce da Allah yayi amfani da ita wajen isar da wahayi, kamar yadda Ya tabbatar a cikin Al-Kur’ani (Suratu Shoorah, Aya ta 51).

A galibin lokuta mutum na iya tuna abin da ya gani a mafarkinsa, daga farko har zuwa karshe.  A wasu lokuta kuma yana iya tuna rabi ne, ko wani bangare na abin da ya gani.  A wasu lokuta kuma yana iya yin mafarki mai daukan hankali; ta bangaren firgitarwa ko faranta rai, amma kuma da zarar ya farka sai ya mance gaba dayan abin da ya auku a cikin mafarkin.

Mafarki wani bangare ne cikin abubuwan dake aukuwa ga dan adam a yayin da yake bacci.  Wannan al’amari na da muhimmanci ga rayuwarsa, musamman ganin cewa Allah madaukakin sarki ya zabi mafarki a matsayin daya daga cikin hanyoyin aika sako ko yin wahayi ga Annabawa da Manzanninsa.  Wannan tasa da yawa cikin mutane mafarkinsu kan dame su, musamman idan munanan mafarki suka yi; su yi ta jigilar neman fassarar abin da suka gani.

Ra’ayoyi kan mafarki da abin da ya kunsa, da fassararsa, da ka’idojin fassararsa, da halaccin aikata abin da mutum ya gani a ciki ba tare da la’akari da shari’a ba, abubuwa ne da zantukan jama’a (Malamai da gama-garin mutane da ‘yan al’ada) suka  yawaita, suka fadada cike da sarkakiya a ciki.  Don haka, wannan kasida ba ta zo bane don bayanin tsarin fassarar mafarki, ko halaccin aikata abin da aka gani a ciki ko duk wani abu makamancin haka.  Kasidar za ta dubi mafarki ne a ilimance, kuma a kimiyyance.  Za mu dubi yaushe mafarki ya samu asali?  Meye ra’ayoyin al’ummomin da suka gabata kan mafarki?  Yaushe malaman kimiyya suka fara mayar da hankalinsu wajen binciken dalilan dake haddasa mafarki?  Shin, sun gano abin da suke nema?  In a a, meye dalili?  Duk wanda zai yi tambaya sai ya killace kansa ga abin da ya karanta a ciki kawai.    Da fatan masu karatu za su yi hakuri da kuntata mahallin tambaya da nayi kan wannan maudu’i.  Na yi haka ne don toshe hanyar kuskuren fahimta da sabani, sanadiyyar bambancin fahimta daga gare ni zuwa ga masu karatu ko daga masu karatu zuwa gare ni, kamar yadda a baya na sha fama dashi kan wasu maudu’ai masu alaka da addini da al’ada.

- Adv -

Mafarki, Daga Ina Kake?

Kamar yadda bayani ya gabata a baya, mafarki wani yanayi ne dake samuwa tsakanin kwakwalwar dan adam da ruhinsa a lokacin da yake bacci, mai dauke da aukuwar al’amura masu kama da irin wadanda yake aiwatar dasu a rayuwa sadda yake farke.  Mafarki ya samo asali ne tun samuwar halittar dan adam.  Duk jinsin dan adam da Allah ya halitta suna mafarki a cikin bacci.  Illa dai yanayin mafarkin ne ya bambanta, da lokacin yinsa, da kuma abubuwan da ake gani; duk sun sha bamban tsakanin mutane.  Don haka, gane iya shekarun da mafarki ya samu abu ne mai sauki in har za mu iya gane iya shekarun da dan adam yayi a doron wannan kasa.

Ra’ayoyin Al’ummomi Kan Mafarki

Duk da cewa dan adam jinsi ne, amma a karkashin jinsin nan akwai nau’uka daban-daban.  Warwatsuwarmu a doron kasa ne ke nuna dalilin bambance-bambancen dake tsakaninmu na launi, da tunani, da dabi’u, da kuma halayyar rayuwa.  Yadda muka saba a wadannan bangarori, to haka muka saba wajen tsarin tunaninmu, ciki har da tunani kan yaya mafarki ke samuwa?  Meye ma’anar abubuwan da ake gani a cikin mafarki ta bangaren fassara?  Sannan, wa ke haddasa samuwar mafarki daga wajen jiki ko kwakwalwar dan adam?  Malaman tarihi sun hakaito mana ire-iren ra’ayoyin al’ummomin duniya kan samuwa da ma’anonin da suke baiwa mafarki da fassararsu.

A bangaren maguzawan zamanin farko wadanda suka yi rayuwa shekaru sama da 4,000 da suka gabata, sun yarda cewa mafarki da duk abin da ake gani a cikinsa, wani yanayi ne da allolinsu (gumaka da sauransu) ke haddasa aukuwarsa a kwakwalwa.  A cewarsu, sun yarda cewa allolinsu ne ke amfani da hanyar mafarki don sanar da su abin da zai faru nan gaba.  Bayan wannan, suna da yakinin cewa mafarki ne hanyar da allolinsu ke amfani da ita a karo na biyu, wajen kawo waraka ga cututtukan dake damunsu a al’ummance.

A bangarensu su ma, al’ummar daular Girka, wato Girkawa, sun yi imanin cewa mafarki hanya ce dake sanar da al’umma ko wanda yayi mafarkin musamman, kan abubuwan da zasu zo nan gaba da suka shafi rayuwarsa.  A nasa bangaren kuma, babban malamin daular Girka mai suna Aristotle, ya kara da cewa lallai daga cikin dalilan dake haddasa aukuwar mafarki a yayin da dan adam ke halin bacci, akwai tasirin da tunaninsa ke yi kan dabi’arsa.  Ma’ana, idan akwai abin da ke damun mutum kuma har ya rinjayi tunaninsa, to, da zarar ya kwanta zai yi mafarki kan wannan lamari.  Wannan tunani an gina shi ne kan cewa, mafarki wani abu ne dake samuwa ko aukuwa sanadiyyar yanayin jiki ba wai Allah bane ke aukar dashi ta wasu dalilai ko sabubba.  Wannan ba abin mamaki bane idan muka yi la’akari da cewa, Girkawa da yawa cikin malamansu basu yarda da Allah ba balle tasirinsa kan halittu.   Cikin karni na 19 (19th Century) ne aka fara samun ra’ayoyi masu nuna tasirin Ubangiji kan mafarki da dan adam ke yi.

A nashi mahangar, shahararren likitan kasar Faransa mai suna Alfred Murray ya gudanar da bincike na musamman kan mafarki da yadda yake aukuwa.  A ra’ayinsa, Murray ya nuna cewa akwai alaka mai karfi tsakanin mahalli da mafarkin da mai bacci yake yi.  Yace ba abin mamaki bane idan mutum na bacci aka buga wani abu mai karfi da ya haddasa kara, idan ya farka yace yayi mafarkin ana cida.  Duk wani sauti dake muhallin mai bacci na iya haddasa aukuwar mafarki a cikin baccinsa, inji Murray.  Wannan ra’ayi nashi ya sha kasa daga wajen masana da suka zo bayanshi, kamar yadda mai karatu zai karanta nan gaba.

Bayan gushewar Alfred Murray da ra’ayoyinsa kan mafarki da dalilin dake haddasa shi, daga cikin wadanda ra’ayoyinsu suka shahara a fagen ilimi cikin karni na 19 akwai Sigmund Freud dan kasar Jamus, wanda yayi rayuwa tsakanin shekarar 1856 zuwa 1939.  Wannan bawan Allah ya rubuta littafi na musamman kan abin da ya kira “Fassarar Mafarki.”  Sunan littafin, wanda ya rubuta shi cikin harshen Jamusanci ne, shi ne: “Die Traumdeutung,” wanda aka fassara zuwa harshen turanci da suna: “The Interpretation of Dreams.”  A cikin sakamakon nasa binciken, Freud yace ya gano cewa mafarki ba wani abu bane face “Ci gaban rayuwar farke” da mutane ke yi ta hakika.  Sannan ya kara tabbatar da cewa lallai akwai alaka mai karfi tsakanin nau’in mafarkin da mai mafarki ke yi da dabi’ar jiki ko yanayinsa.  Ya ba da misalai.  Yace mutumin dake da matsananciyar bukatar saduwa tsakaninsa da mace, yana iya mafarki kan haka, muddin bai samu ba.  Haka wanda ke da sabani tsakaninsa da wani, har ta kaishi  ga bacin rai, yana iya mafarkin wannan lamari a halin baccinsa.

Zan ci gaba mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.