Bikin Murnar Cika Shekaru 50 da Fara Zuwa Duniyar Wata

Ranar Talata, 16 ga watan Yuli, 2019 ne aka fara bikin murnar cika shekaru 50 da fara zuwa duniyar wata, wanda kasar Amurka ta aika mahaya kunbo Apollo 11 zuwa duniyar wata. Wannan kunbo ya bar duniyarmu ne ranar 16 ga watan Yuli, 1969, ya isa duniyar wata ranar 20 ga watan Yuli na shekarar. Wannan yasa muka dauki wannan mako don taya masu karatu murnar wannan lokaci mai tarihi a rayuwar dan adam. An buga wannan makala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2019.

1,156

Ga wadanda suke bibiyar labaru musamman kan fannin kimiyyar sararin samaniya, ranar Talata, 16 ga watan Yuli, 2019 da muke ciki ne aka fara bikin murnar cika shekaru 50 da fara zuwa duniyar wata daga wannan duniya tamu.  Sanadiyyar haka ne sashen Hausa na DW dake Jamus suka tattauna dani na tsawon mintuna wajen 10, don yin sharhi kan mahimmancin wannan rana ko shekara, da irin ci gaban da aka samu tun sannan, da kuma darasin da kasashe masu tasowa musamman kasarmu Najeriya za ta iya dauka.  Idan masu karatu basu mance ba dai, ranar 16 ga watan Yuli na shekarar 1969 ne hukumar Cibiyar Binciken Sararin Samaniya na kasar Amurka, wato NASA, ta harba kumbo dauke da motocin ziyara a sararin samaniya (Lunar Rovers) guda 3, don aika kwararru su gano abin da Allah ya tanada a duniyar wata, wato tauraron wannan duniyar tamu kenan.  Wannan tawaga na mahaya dai ya dauki tsawon kwanaki hudu ne daga tashinsa daga cibiyar da aka harba shi, ya kuma isa duniyar wata a ranar 20 ga watan Yuli, shekarar 1969.  Wannan ke nuna muna cikin shekara na 50 kenan da faruwar wannan lamari.

Tun daga wancan lokaci kasashe suka fara musabaka da juna wajen zuwa duniyar wata da shuka taurarin dan adam don manufofi daban-daban.  Bayan kasar Rasha ta aika kumbonta dauke da Yuri Gagarin, mutum na farko da ya fara shiga sararin samaniyar wannan duniya tamu, a shekarar 1961, sai kasar Amurka ta aika da tawagar farko dauke da su Neil Armstrong da Buzz Aldrin da kuma Michael Collins, zuwa duniyar wata a shekarar 1969.  Daga nan aka samu kasashe da dama irin su kasar Burtaniya su ma suka aika nasu.  Abin da ya fara daga zuwa duniyar wata, wanda shi ne tauraron wannan duniyar tamu, ya zuwa yanzu an kai ziyara zuwa duniyoyi guda 6, da kuma duniyar watanni guda 3.

Dangane da haka hukumar NASA ta kasar Amurka ta shirya bukukuwa da tarurruka da bitoci kan wannan al’amari, wanda ta fara tun cikin watan Afrailu (2019), zai kuma zarce har zuwa watan Janairu na shekarar 2020.  Duk wannan don kara fadakar da jama’a ne mahimmancin dake cikin wannan al’amari.  Ba hukumar NASA kadai ba, kafafen yada labarai na gwamnatocin kasashe da masu zaman kansu, da jaridu da mujallu musamman na kimiyya da sararin samaniya, duk sun rubuta makaloli da dama don nuna murna da zagayowar wannan rana.  Daga cikin kafafen yada labaru na rediyo da talabijin da suka baiwa wannan rana da lokaci mahimmanci akwai kafan sadarwa ta BBC dake kasar Burtaniya, da tashar DW Radio dake kasar Jamus.

- Adv -

Daga wannan wata da muke ciki har zuwa karshen wannan shekara za a ci gaba da ta tattauna wannan al’amari a matsayin wata marhala mai matukar mahimmanci a fannin sararin samaniya, wanda hakan ya haifar da ci gaba mai girma a bangarorin tsaro, da sadarwa, da yanayi, da kuma kimiyyar kere-kere.

A namu bangare kuma ga wadanda suka saba karanta wannan shafi shekaru bakwai zuwa goma da suka gabata, sun san mun gabatar da bayanai masu yawa kan wannan maudu’i.  Don haka, daga wannan mako zuwa makonni hudu dake tafe in Allah Yaso, za mu yi waiwaye, abin da Bahaushe ke kira adon tafiya, kan wadancan bayanai da muka gabatar, don baiwa masu karatu musamman wadanda basu samu daman karanta wadancan makaloli da suka gabata a baya, damar karantawa da samun karuwar ilimi da fahimta.

Bayanan da muka gabatar dai sun hada da amsar tambayoyi da wasu cikin masu karatu suka aiko, da kuma makaloli na musamman da na rubuta kan wannan maudu’i, musamman wadanda suka shafi tauraron dan adam, da kumbon da kasashe ke harbawa zuwa sararin samaniya, da halittar rana da wata, da yadda wannan duniya ke gudanuwa a kimiyyance, da dai sauran bayanai masu alaka da wannan ilimi mai matukar mahimmanci musamman a duniyar yau.

Da fatan masu karatu za su ci gaba da kasancewa tare damu.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    👍👍👍

  2. Auwal ibrahim danbaba says

    Allah ya saka da alkhairi

Leave A Reply

Your email address will not be published.