Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (5)

Nau'i da Mizanin Batir

Kasancewar wayar salula na’ura ce da ake tare da ita a jiki a kowane lokaci, saboda yanayin girmanta (shi yasa ake kiranta da suna “Mobile Phone” – wato wayar da ake tafiya da ita duk inda ake), yasa batirinta na ɗauke ne da sinadaran dake iya riƙe makamashin lantarki an tsawon lokaci, sannan kuma ana iya cajin batirin lokaci zuwa lokaci.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 1 ga watan Satumba, 2023.

56

Nau’i da Mizanin Batir

Daga cikin dalilan dake sa wayar salula tsada ko arha, akwai nau’i da mizanin batirin da aka ƙera ta dashi.  Da farko dai, shi batir aikinsa shi ne samar da makamashin lantarki ga wayar salula.  Wayar salula ba za ta iya tashi da gudanar da kowane irin aiki ba idan babu makamashin lantarki a tare da ita.  Domin dashi ne kusan dukkan mahimman ɓangarorinta ke dogaro wajen gudanar da ayyukansu.  ɓangarori mafi buƙatuwa ga makamashin lantarki, wanda batirin wayar salula ke samarwa, su ne ɓangaren sikirin, wanda bayaninsa ya gabata a maƙala ta 2, da kuma cibiyar sarrafa bayanan wayar salula, wato “System on Chip”, ko “SoC”, wanda bayaninsa ke tafe nan da mako mai zuwa, in Allah Ya so.

Shi ɓangaren sikirin ma kusan ya fi kowane ɓangaren wayar salula cin makamashin lantarki; iya gwargwadon girma da faɗi da kuma nau’insa.  Domin shi ne ɓangaren dake nuna maka dukkan ma’amalar da kake yi da wayar.  Daga rubutu, da karatu, da kallo har zuwa saurare, duk fuskar wayar ke maka wannan aikin.  Wannan yasa sikirin ke ci da tumurmusan makamashin lantarki.  A ɗaya ɓangaren kuma, babbar cibiyar sarrafa bayanan wayar salula, wato: “SoC”, kamar yadda a makon gobe za mu gani, tana cin makamashin lantarki sosai ita ma.  Domin nan ne cibiyar dake sarrafa bayanai da kuma dukkan umarnin da kake baiwa wayar.  Gaba ɗayan ƙananan na’urorin dake cikin wannan cibiya suna dogaro ne kacokam da makamashin lantarki wajen iya gudanar da aikinsu.

Daga bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa lallai makamashin lantarki shi ne “abincin” wayar salula ma baki ɗaya.  Domin dukkan wani ɓangare da ke da ruwa tsaki wajen gudanuwar wayar, yana dogaro ne ga makamashin lantarki.  Wannan makamashi kuma batir ne ke samar dashi kai tsaye.  A taƙaice ka iya cewa, “Idan babu batir, to, babu wayar salula.”

Batirin wayar salula dai ya kasu kashi biyu ta la’akari da mazauninsa a cikin wayar salula.  Akwai wanda ake iya cirewa.  Wannan shi ake kira: “Removable battery”.  Sai kuma wanda a al’adance ba a cire shi, sai in wata matsala ce ta faru. Kamar mutuwar batirin, ko ana son cire wani ɓangaren wayar salula wanda batirin ke zaune a samansa, ko makwabtaka dashi.  Wannan zai sa a cire shi.  Shi wannan nau’i na batir ana kiransa: “Non-removable battery”, kuma idan buƙata ta kama a cire shi ma, sai mai gyara wayar salula ne kaɗai zai iya cire shi.  Hakan ya faru ne saboda yadda ake dabaibayeshi da sauran ɓangarorin wayar salula masu haɗarin taɓawa.  Kusan kashi 90 cikin 100 na wayoyin salular zamani a yau duk suna zuwa ne da baitirn da aka gina shi a cikin wayar kai tsaye.

- Adv -

Kasancewar wayar salula na’ura ce da ake tare da ita a jiki a kowane lokaci, saboda yanayin girmanta (shi yasa ake kiranta da suna “Mobile Phone” – wato wayar da ake tafiya da ita duk inda ake), yasa batirinta na ɗauke ne da sinadaran dake iya riƙe makamashin lantarki an tsawon lokaci, sannan kuma ana iya cajin batirin lokaci zuwa lokaci.  Abin da cajin batirin wayar salula ya ƙunsa shi ne, ƙara zaburarwa da zuba sinadaran dake samar da makamashin lantarki a cikin batirin kai tsaye, don jadda sinadaran lantarkin da wayar salula ke buƙata.  Wannan yasa ake kiransu da suna: “Rechargeable batteries”.  Ma’ana, nau’ukan baitiran da ake iya cajinsu don ƙara samar da makamashin lantarki a cikinsu.  Nau’in sinaran kimiyyar dake samar da ƙaruwar makamashin lantarki a batirin wayar salula shi ake kira: “Lithium-ion”.  Duk da yake a halin yanzu akwai wata fasahar cajin batiri da aka samar, wannan nau’i na Lithium-ion shi ne a ɗauke a kusan kashi 99 na batirin da wayoyin salular zamani ke zuwa dashi.

Siffa ta ƙarshe, shi ne mizani ko girman ƙarfin batirin wayar salula.  Wannan mizani na daga cikin dalilan dake sa a jima ana amfani da wayar salula ba tare da cajinta ya ƙare ba.  Ana auna mizanin batirin wayar salula ne da mizanin makamashin lantarki mai suna: “Mega Ampere” ko “mAh” a gajarce.  Kuma mizanin galibin wayoyin salula a wannan zamani na farawa ne daga 2,500 mAh.  Wasu wayoyin kan zo da batir mai mizanin 3,500 mAh.  Wasu kuma 4,000 mAh.  Galibin wayoyin da aka ƙera daga shekarar 2021 zuwa yanzu kanzo ne da batira masu mizanin 5,000 mAh zuwa 6,000 mAh.  Ƙaruwan mizanin wayoyin salila ya samo asali ne daga cikin ci gaban da ake samu wajen sababbin abubuwan amfani da kamfanonin wayar salula ke samarwa a wayoyin, waɗanda kuma suna buƙatar ƙarin makamashin lantarki.

Misali, galibin wayoyin salula masu manyan sikirin da ya kai inci 5 (5 inch), ko 5.5 (5.5 inch), ko inci 6 (6 inch), ko inci 6.5 (6.5 inch), har zuwa inci 7 (7 inch), za ka samu girman sikirin ɗinsu na ƙaruwa ne tare da girman mizanin batirinsu.  Wannan ne zai tabbatar da daidaito wajen amfani da makamashin lantarkin da wayar za ta buƙata idan ana amfani da ita.  Kamar yadda na sanar, ba abin da yafi sikirin ɗin wayar salula cin batir, musamman idan ya an ƙure hasken dake shafin.  Wannan yasa kusan dukkan wayoyin salula na zamani suke ɗauke da tsarin daidaita hasken sikirin ɗin wayar salula ta la’akari da yanayin da mai amfani da wayar yake.  Ma’ana, idan a waje kake inda akwai haske sosai, sai wayar da ta ƙara hasken sikirin ɗin da kanta.  Idan a cikin duhu kake ko cikin dare inda ba haske, sai wayar ta rage kaifi da hasken sikirin ɗin, don daidai maka yanayin ganinka.

Waɗannan siffofi da suka gabata suna cikin manyan dalilan dake sa wayar salula ta yi tsada ko araha.  Galibin wayoyin salula masu ɗauke da manyan mizanin batir sukan fi waɗanda mizanin batirinsu kaɗan ne, tsada.  Haka ma akasin hakan.

A mako mai zuwa za mu ci gaba, inda za mu yi bayani kan babbar cibiyar sarrafa bayanai na wayar salula, wato “System on Chip”, ko “SoC”, a gajarce.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.