Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada Ko Araharta (19)

Ƙarƙashin wannan sashi mun yi bayani ne a taƙaice kan ci gaban da aka samu shekaru kusan 20 da suka gabata zuwa yau.  Daga kan tsarin ƙirar gangar-jikin wayar salula, zuwa ci gaban da aka samu wajen haɓaka da ƙayatar da babbar manhajarta.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 15 ga Watan Disamba, 2023

22

Kammalawa

Bayan tsawon makonni goma shatakwas muna bayani kan dalilan dake haddasa tsada ko arahar wayar salula na zamani, a yau za mu kammala bayani kan wannan maudu’i mai matuƙar mahimmanci ga masu saya ko yunƙurin sayan wayar salula na zamani.  Dalilin fara wannan maƙala dai ya biyo bayan yawan tambayoyi da nake samu ne daga masu karatu kan wace irin waya ya kamata su saya?  Ko me yasa wata wayar tafi wata wayar kuɗi da tsada, bayan kuma mai arahar kamar tafi girma? Da dai sauran tambayoyi makamantan wannan.  Shi yasa naga dacewar gabatar da jawabi gamsasshe.

Mabuɗin Kunnuwa

Ƙarƙashin wannan sashi mun yi bayani ne a taƙaice kan ci gaban da aka samu shekaru kusan 20 da suka gabata zuwa yau.  Daga kan tsarin ƙirar gangar-jikin wayar salula, zuwa ci gaban da aka samu wajen haɓaka da ƙayatar da babbar manhajarta.  Haka an samu sauyin kamfanonin wayar salula daga wancan lokaci zuwa yanzu; wasu sun haɗe da wasu, wasu kuma sun kwanta dama, wasu kuma sun ƙara ci gaba.  Babbar manhajar wayar salular da taci karenta ba babbaka a shekaru ashirin da suka wuce ita ce Symbian.  Ya zuwa yanzu, da yawa cikin matasa masu shekaru ƙasa da ashirin da biyar a yau basu san wannan nau’in babbar manhajar wayar salula ba. Wacce suka sani ita ce Android da iOS na kamfanin Apple.

A ɓangaren tsarin ma’alama da wayar salula ma an samu ci gaba sosai.  A baya wayoyin salula suna ɗauke ne da maɓallai wajen shigar da bayanai da bata umarni, sai ƙaramar fuska wacce ke nuna maka lambar da kake latsawa ko sunan wanda kake kira ko yake kiranka, sai kuma saƙonnin da kake karɓa da waɗanda kake aikawa, tare da sanarwar waya na shigowan saƙo da dai sauransu.  A halin yanzu kashi 98 cikin 100 na wayoyin salula suna ɗauke da shafaffen fuska ne, wato “Touch screen”.  Abu na ƙarshe cikin manyan ci gaba akwai sauyin yanayin sadarwa sanadiyyar ci gaban marhalar sadarwa, wato: “Mobile Phone Newtwork Generations”, daga 0G zuwa 5G da muke ciki a yau.

Dalilan Arha ko Tsadar Wayar Salula

Dalilan arha ko tsadar wayar salula suna da waya, shahararru daga cikinsu ne muka zayyana.   Abu na farko shi ne fuskar wayar salula. Shi ne abin da yafi komai cin makamashin wayar salula.  Me yasa ya zama dalilin tsada ko arahar waya?  Fuskar wayar salula, wanda a turance ake kira: “Screen Display”, ko sikirin, ya kasu kashi biyu ne.  Akwai nau’in LCD, wanda shi ne kan galibin ƙananan wayoyin salula.  Idan nace ƙanana ina nufin wayoyin salula masu ƙarancin farashi, ko masu araha dai a taƙaice.  Wannan nau’i na sikirin yana cin makamashin batir sosai, amma yafi araha.  Na biyun shi ne nau’in LED, wanda ya ɗara na farkon ƙarko.  Kuma ya fi nuna baƙin launi raurau.  Bayan haka, ba ya cin makamashi da yawa.  Amma ya fi na farkon tsada.  Wayar dake ɗauke da sikirin nau’in LED, ta fi wacce ke ɗauke da nau’in LCD tsada.

- Adv -

Na biyu shi ne ƙwaƙwalwa ko cibiyar sarrafa bayanan wayar salula.  Wannan shi ake kira: “Chipset” ko kuma “System on Chip” – SoC.  Wannan cibiya na ɗauke ne da ɓangarori wajen shida dake taimaka ma wayar salula karɓa da sarrafa bayanai.  Daga abin da ya shafi adana bayanai, zuwa siginar sadarwa, da siginar Intanet, da naɗewa tare da nuna saƙonnin bidiyo da sauti, sai ɓangaren da ya shafi sarrafa saƙo idan ya shigo cikin wayar. Mizanin wannan cibiya ya sha banban.  Iya girman mizaninsa, iya tsadar wayar salula.

Sai ɓangaren kyamarar wayar salula.  Shi ma yana cikin manyan dalilai.  Kyamarar wayar salula dai nau’i nau’i ne ta ɓangaren zahirin siffarta ko aikinta.  Akwai kyamarar asali, ita ake kira “Rear camera”, kuma tana goye ne a bayan wayar salula.  Sai wacce ke gaban wayar salula da ake kira: “Selfie camera”, ita kuma an ɗora ta ne don sawwaƙe wa mai waya hanyoyin da zai ɗauki kansa kai tsaye.  waɗannan nau’ukan kyamara duk suna da mizani da matsayi.  Idan mizaninsu da matsayinsu iya tsadar wayar salula.

Abu na gaba shi ne ma’adanar wayar salula, wanda mahalli ne da ake adana bayanan manhaja da bayanan mai waya, da kuma tsarin amfani da manhajar wayar salula.  Akwai ma’adanai nau’uka uku.  Akwai ma’adanar wucin-gadi wacce ake kira da suna RAM (Randon Access Memory).  Wannan ita ce ma’adanar dake riƙe bayanan manhajar da kake aiki da ita a kan waya.  Da zarar ka rufe manhayar, sai su koma ma’adana ta biyu da ake kira tabbatacciyar ma’adana, ko “Internal Storage” kenan.  Dukkan abinda ke kan wayarka ta salula, a cikin wannan ma’adanar suke. Sai ma’adana ta uku wacce ke baka damar faɗaɗa wannan ma’adana ta biyu idan ta cike.  Misali, idan wayarka ta ɗauke da ma’adana mai mizanin 64GB ne, kana iya ɗora mata ma’adanar memori, wato: “Multimedia Memory Card” kenan, ko MMC a gajarce.  Dukkan waɗannan ma’adanai suna da mizani ne daban-daban; iya girma da yawan mizanin, iya tsadar wayar salula.

Abu na gaba dake sa waya tayi tsada ko araha shi ne mizanin batirin wayar.  Batiri shi ne ma’adanar makamashin lantarki da wayar salula ke amfani dashi. Idan babu batir, to, ba wayar salula.  Domin ko tashi ba za ta iya yi ba balle ta iya sarrafa maka bayanan da kake mika mata ko son karɓa daga gareta.  Shi batirin wayar salula yana ɗauke ne da sinadaran dake iya taskance makamashin lantarki nau’in “Lithium-ion”, a harshen turancin kimiyyar ƙere-ƙere.  Iya girman mizaninsa iya tsadar wayar salula.

Abu na ƙarshe dai shi ne fasahar senso da wayar salula ke amfani dashi wajen gano yana da halin da take ciki, don bai wa wasu manhajojin cikinta damar aiwatar da aikin da aka ƙera su aiwatarsa.  Wannan fasaha dai ta kai kusan takwas a jikin wayar salula. Akwai wacce ke lura da yanayin haske ko duhu na inda wayar take, da wacce ke lura da tsayuwa ko kwanciyar wayar idan an riƙe da dai sauransu.

Cikawa

A ƙarshe dai, wannan shi ne kammalawa ko cikon bayani na waɗancan maƙalolin da suka gabata tsawon watannin baya.  Kamar yadda na sanar a makon shekaranjiya, mako mai zuwa za mu shiga wani sabon maudu’i in Allah Ya so.  A ci gaba da kasancewa tare da jaridar AMINIYA.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.