YouTube: Taska Mafi Tsada Da Haɗari a Intanet (3)

Haɗarin Dake Tattare Da Shafin YouTube

Mafi muni cikin ire-iren waɗannan tashoshi shi ne wanda ke ɗauke da hoton wani cikin manyan malamai a ɓangare ɗaya, a ɗaya ɓangaren kuma asa hoton wata mace cike da tsaraici, wai don a nuna abin da malamin ke magana ko fatawa a kai. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 2 ga watan Yuni, 2023.

139

Taska Mai Haɗari

Bayan waɗancan fa’idoji da bayaninsu ya gabata a makon jiya, a yau mai karatu zai san wasu daga cikin manyan haɗarorin dake tattare da wannan manhaja ko shafi na YouTube.  Ga kaɗan daga ciki nan:

Yaɗa Ƙarerayi da Jita-Jita

Akwai saƙonnin bidiyo masu ɗimbin yawa da aka ɗora su musamman don yaɗa jita-jita da ƙarerayi kan wasu mutane, ko wata al’umma, ko wani addini, ko wata hukuma, ko wata ƙasa, ko wasu hajoji na kasuwanci da dai sauransu.  Ƙarya da jita-jita, kamar yadda yake birjik a dandalin sada zumunta irin su Facebook da Twitter, haka yake birjik a tsarin bidiyo a dandalin YouTube.  A kowane lokaci ba a rasa wani jita-jita da ya shahara a duniya da ake yaɗa shi a shafin Youtube.  Misali, shekarar da aka yi cutar Corona, an ta yaɗa ƙarerayi da dama kan dalilinsa, da wanda ko ƙasar da ta samar dashi (kamar yadda ake riyawa), da adadin mutane da cutar ke kashewa a duk yini.  Haka sadda fasahar 5G ta bayyana, an ta yaɗa saƙonnin bidiyo na ƙarya dake bayyana cewa lallai wannan fasaha ce da za ta riƙa yaɗa cuta ta hanyar sinadaran maganaɗisun lantarki na sadarwa.  Wasu ma suka ce ita ce silar yaɗa cutar Corona, da dai sauran ƙarerayi makamantan wannan.  Idan baka san me kaje nema ba, sai ka kwashi ƙarya ka zuba a ƙwaƙwalwarka.

Satar Fasaha (Copyrihgt Infringement)

Akwai saƙonnin bidiyo na sata da yawa a YouTube.  Wasu fina-finai ne.  Wasu kuma waƙoƙi ne masu haƙƙin mallaka.  Wasu kuma darussa ne na ilmi da wani ya taɓa ɗorawa a tasharsa a YouTube, sai a sauke, a canza musu bayanai sannan a sake ɗora su da sunan sababbai.  Manyan dalilan dake sa wasu satan bidiyon wasu – a YouTube ko a wajen YouTube – shi ne, don samun daloli dasu a tasharsu ta YouTube.

A ƙa’ida, hukumar YouTube na da fasahar dake iya gane cewa saƙon bidiyon da ka ɗora a tasharka, naka ne ko kuma daga tashar wani ka sato a nan YouTube.  Muddin an taɓa ɗora saƙon a YouTube, fasahar na iya ganewa.  To amma saboda ɗabi’ar ɗan adam ta waskiya, ana amfani da wasu manhajojin haɗa hotuna da bidiyo don jirkita bidiyon da aka sato, sannan a sake ɗora shi a matsayin sabo.  A duk sadda hukumar Youtube ta gano irin wannan bidiyo na sata, takan nusar da mai tashar da ya cire.  Idan yaƙi cirewa, sai ta zaftare dukkan kuɗaɗen  da ya samu daga bidiyon, sannan ta daina nuna shi ma gaba ɗaya.  Idan yaƙi cirewa sai kawai ta kore shi daga dandalin.  Ko ta dakatar da tasharsa daga tsarin biyan kuɗi na Adsense.  Kusan kullum na hau YouTube sai na ci karo da ire-iren waɗannan bidiyon.  Saboda na san asalin tashar da aka sato bidiyon.

Don haka, sai ka kiyaye, idan ba haka ba, kana iya ɗaukan ilmi jirkitacce daga jirkitattun saƙonnin bidiyo na sata.

- Adv -

Batsa Da Ashararanci

A tare da cewa shafin YouTube yana da tsafta idan an kwatanta shi da wasu shafuka makamantansa, duk da haka akwai saƙonni masu ɗauke da batsa da ashararanci birjik.  Wannan kuma na nan cikin kowane harshe.  Kana iya gane ire-iren waɗannan bidiyon daga tambarin hoton dake kan saƙon kafin ka buɗe, da kuma sunan bidiyon.  Wannan ba wani abu bane ɓoyayye.  Galibin samari a arewacin Najeriya musamman, kan buɗe tasha na musamman don yaɗa ire-iren waɗannan saƙonni cikin sunaye munana da ɗaukan hankali, da hotuna masu jan hankali.  Wasu hotunan ma cike suke da suran mata a yanayi mara tsafta.

Mafi muni cikin ire-iren waɗannan tashoshi shi ne wanda ke ɗauke da hoton wani cikin manyan malamai a ɓangare ɗaya, a ɗaya ɓangaren kuma asa hoton wata mace cike da tsaraici, wai don a nuna abin da malamin ke magana ko fatawa a kai.  Misali, idan wani Malami yayi zance kan kyautata wa miji wajen kwanciya, sai a ɗauko hoto mara tsafa asa, a haɗa da hoton malamin, sannan a rubuta take mai ɗaukan hankali.  Masu yin wannan assha dai galibi suna yi ne don jawo hankalin mutane su kalli bidiyon, sannan sun matsa alamar “Subscribe”, don ƙara musu shahara a ɓangare ɗaya, da kuma kawo musu ‘yan daloli, a ɗaya ɓangaren.  Wannan ruwan dare ne a shafin YouTube.  Don haka sai a kiyaye.

Yaɗuwan Miyagun Aƙidu da Al’adu

Kamar yadda yake a sauran wurare a Intanet, yaɗuwar miyagun aƙidu da al’adu ruwan dare ne a shafin YouTube.  Sai dai kuma tasirinsu ya fi gamewa a shafin YouTube, saboda tasirin gani, da kuma ji, wanda malaman ilmin ɗabi’a suka ce su ne manyan dalilan da suka sa saƙonnin bidiyo suka fi zama tunani da zuciyar mai kallonsu, sama da rubutattun bayanai ko waɗanda aka saurara.

Daga addini zuwa al’adu, da kasuwanci, da zamantakewa, da uwa uba siyasa, duk za ka samu miyagun aƙidu da al’adu ana yaɗawa kai tsaye babu tsoron Allah.  Masu yin hakan na amfani ne da dabaru da yawa.  Daga cikinsu akwai amfani da hotuna da bidiyo masu alaƙa da abinda suke tallatawa, wanda kuma suka samo daga wani shafi na Intanet, ko daga zahirin rayuwa, don tabbatar da abin da suke tallatawa.  Mafiya haɗari cikin ire-iren waɗannan saƙonni dai su ne masu alaƙa da addini.

Kammalawa

A ƙarshe dai, shafin YouTube taska ce mai matuƙar muhimmanci, wanda na koyi abubuwa da yawa a ciki, tare da fa’ida da fa’idoji masu ɗimbin yawa.  Sai dai kuma, ma’amala da bayanai a wannan dandali na buƙatar taka-tsantsan, da basira, da kuma ilmi kan haƙiƙanin abin da kake nema.  Idan kawai kana shawagi ne don kallon duk abin da ya ƙayatar dakai, to, watarana za ka samu kanka cikin kwatami.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.