Nau’ukan Cutar Kwamfuta

Idan mai karatu na tare da mu, muna yin bayani ne kan kwayoyin cutar kwamfuta da illolin su da kuma masu hakki wajen kirkiro wannan annoba.  Har wa yau, a makon da ya gabata mun kawo bayanai kan tsarin da masu wannan al’ada ke bi wajen yada kwayoyin cutar da ke ma kwamfuta illa a duniya.  A karshe kuma mai karatu ya samu bayanai kan tasirin wannan sana’a nasu, hatta ga siyasar duniya.  A yau za mu ci gaba, inda za mu kawo hanyoyin da wadannan masana harkan kwamfuta ke bi wajen shiga kwamfutocin jama’a; ko dai don yada kwayoyin cuta, ko aiwatar da satan bayanai, ko kuma don sace ma jama’a kudade da kuma aikin leken asiri. 

Karin Bayani...

Tsarin Tunani da Dabi’un ‘Yan Dandatsa (Hackers)

Cikin bayanan da muka fara kwararowa kan Kwayar Cutar Kwamfuta da nau’ukan ta da kuma yadda take haddasuwa, da masu kirkiran ta, mun tsaya ne a gabar da ke karantar da mu irin manufofin da masu wannan sana’a ke tinkaho dasu wajen yin dukkan wata ta’addanci da ta shafi cutar da kwamfutocin mutane a duniya.  A yau za mu ci gaba, in da mai karatu zai ji bayani kan ire-iren ayyukan da wadannan ‘Yan Dandatsa (Hackers) suke yi wajen yada wadannan cututtuka da suke kirkira.  Bayan haka, za kuma muji irin tasirin da hakan ke yi a duniyar yau.  Kada mai karatu ya mance cewa a cikin kasidun da suka gabata, mun nuna cewa wannan sana’a ta Dandatsanci (Hacking), ta yadu sosai musamman cikin manyan kasashen da suka ci gaba wajen tsarin sadarwa ta zamani, irin su Amurka, Ingila, Awstiraliya, Sin, Jamus, Rasha da Jafan.  Ina mana wannan matashiya ne don mu dada fahimtar yadda tasirin ayyukan su na Dandatsanci ke cin karensa ba babbaka a yau, kamar yadda za mu karanta a yau.  Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau Kura.

Karin Bayani...

Asalin ‘Yan Dandatsa (Hackers) da Alakarsu da Kwayar Cutar Kwamfuta (1)

A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai ne kan kwayoyin cutar kwamfuta da tsarin su da yadda suke yaduwa, da kuma tasirin su.  A karshe kuma sai muka kawo nau’ukan wadannan cututtuka da ke damun kwamfuta da hana ta sakewa.  A yau idan Allah Ya yarda za mu ci gaba da kwararo bayanai ne ; za mu san su waye ke da alhakin yada ire-iren wadannan kwayoyin cututtuka da kuma irin mummunan abin da suke haifarwa a duniya gaba daya.  Za mu san shahararren suna ko lakabin da aka san su dashi a duniyar fasahar sadarwa a yau, da kuma tarihin wannan sana’a tasu mai mummunan sakamako.  Idan Allah Ya bamu dama, za mu kawo bayani kan manufar wadannan mutane ; me  yasa suke wannan aiki?  

Karin Bayani...