Shawarwari Ga Gwamnatin Tarayya Kan Hanyoyin Ciyar Da Najeriya Gaba A Fannin Kimiyya Da Ƙere-Ƙere (6)

Cibiyoyin bincike su ne ƙashin bayan ci gaban kowace ƙasa wajen kimiyya da ƙere-ƙere.  Daga ƙasar Amurka zuwa Ingila, da Sin, da Malesiya, da Singafo, har zuwa ƙasar Indiya da Jafan, duk da cibiyoyin binciken ilmi suke taƙama.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 21 ga watan Yuli, 2023.

45

Shawarwari Kan Hanyoyin Ci Gaba

Hanyoyin ci gaba a fannin kimiyya da fasahar ƙere-ƙere ga kowace ƙasa ce, a fili suke, musamman a wannan zamani dake cike da hanyoyin mallakar ilmi mai yawa kuma cikin sauƙi.  Duk da cewa ba wai hanyoyin bane muka jahilta, a a, sadaukar da kai ne kawai muka rasa da kishin ƙasa.  Amma duk da haka, kogi ba zai ƙi daɗi ba. Mai Girma Shugaban Ƙasa, ga wasu daga cikin hanyoyin nan:

Nazarin Fasahohin Zamani Daga Waje

Akwai kayayyakin ƙere-ƙere da hanyoyin ci gaba a fannin kimiyya da suka shigo mana har muke amfani da su.  Me zai hana gwamnati ta kafa cibiyoyi na musamman don yin nazari da “dubiya” kan tsari da kimtsin yadda aka ƙera waɗannan kayayyaki?  Galibin ƙasashen da suka ci gaba basu mallaki ƙwarewar da suke takama da ita ba sai ta ire-iren waɗannan hanyoyi.  Wannan zai taimaka mana a hanyoyi biyu; na farko, za mu riƙa ƙera waɗannan kayayyaki cikin sauƙi kuma a ƙasarmu, sannan kuma ‘yan ƙasa za su mallaki fasahar ƙera su ba tare da sai sun je asalin ƙasashen da aka kero su ba.  A wasu lokuta ma idan zuwa ƙasar ta kama, ana iya zuwa.  Ga motoci nan bila-adadin, ga ƙerarrun mashinan zamani, ga injinan ƙera abubuwa da yawa – daga na tatse lemun tsami, da gyaɗa, da na markaɗe da dai sauransu – duk muna iya bibiyar asalin fasahar da aka yi amfani da ita wajen ƙera su.  Akwai yara da ɗalibai masu hazaƙa a makarantunmu dake amfani da hazaƙarsu wajen ƙera ire-iren waɗannan injina, sai dai babu wani kulawa ne a ɓangaren hukuma.

“Satar Fasaha” (Industrial Espionage)

- Adv -

A fannin ilmin ci gaban kasuwanci da ƙere-ƙere, “Satar Fasaha”, wanda a harshen turanci ake kira “Industrial Espionage”, shi ne leƙen asiri kan asalin ilmin fasahar yadda ake ƙera wasu kayayyaki – kamar injina, da mashina, da motoci, da sauran hajojin kasuwanci – ta hanyar ƙarƙashin ƙasa.  Da wannan tsari ne galibin kamfanoni ke amfani wajen satar fasahar yadda wasu kamfanonin ke ƙera hajojinsu.  Hakan kuwa na samuwa ne ta hanyar bincike a Intanet, da littattafai, da nemo bayanai ta ƙarƙashin ƙasa daga ma’aikatan wasu ƙasashe ko kamfanin dake ƙera irin fasahar da ake buƙatar haɓɓakawa.  Duk wannan, idan za mu yi da gaske, ba wani bane mai wahala ko kadan.  Saɗaukar da kai kaɗai muke buƙata da kishin ƙasa.

Yanayin Karatu Mai Inganci a Makarantu

A tabbace yake cewa ilmi ba ya samuwa ta sauƙi, amma hakan ba ya nufin a yi ta yinshi ne cikin wahala da ƙunci.  Akwai irin yanayin da karatu ke buƙata kafin ya tabbata a zuciya ko kwakwaklwar wanda ke ɗaukansa.  Idan ba a samu wannan yanayi ba, to babu yadda za a yi ya zauna, balle har a iya amfana dashi. Hakan ya haɗa da samar da malamai masu nagarta, da tarbiyya ta hanyar lura da doka da oda a ko ina ne cikin ƙasa, da samar da na’urori da kayayyakin ɗaukan darasi da karatu masu inganci, irin su littattafai, da azuzuwa masu ɗauke da wutar lantarki, da ruwan sha, da ɗakunan ɗalibai masu inganci, da kayayyakin binciken ilmi masu inganci, da kuma sauƙaƙa farashin karatu

Tallafi Ga Cibiyoyin Binciken Ilmi

Cibiyoyin bincike su ne ƙashin bayan ci gaban kowace ƙasa wajen kimiyya da ƙere-ƙere.  Daga ƙasar Amurka zuwa Ingila, da Sin, da Malesiya, da Singafo, har zuwa ƙasar Indiya da Jafan, duk da cibiyoyin binciken ilmi suke taƙama.  A wasu ƙasashe ma ba wai gwamnati kaɗai ke mallakar cibiyoyin ilmi ba, hatta kamfanonin ƙere-ƙere kan kafa ire-iren waɗannan cibiyoyi.  Tabbas tafiyar da cibiyar binciken ilmi abu ne mai wahala, domin yana buƙatar maƙudan kuɗi da ƙwarewa da kuma tallafin wasu ƙasashe, amma duk da haka, wannan ba ya nufin ba za mu iya ba, tunda ga ƙasashe masu yawa, waɗanda ma ake ganin ba kowa bane su, sun riƙe ire-iren waɗannan cibiyoyi.  Muna da cibiyoyin binciken ilmi tsakanin fannin haɗa magungunan cututtukan jikin ɗan adam zuwa na dabbobi, har zuwa na binciken ƙananan ƙwari, amma idan ka shiga cikinsu sai ka tausaya musu.  Galibinsu da kyar suke dogaro da kansu.  Kuɗaɗen da ake tura musu na biyan albashi ne kaɗai ba wai na gudanar da binciken ilmi ba.  Akwai hukumomi da yawa a sauran ƙasashen duniya dake ba da tallafi a fannonin binciken ilmi da yawa, wajibi ne ga gwamnatin tarayya da na jihohi su samar da wani tsari da zai tabbatar da yiwuwar hakan don ciyar  ƙasarmu gaba.

Bayan haka, wajibi ne gwamnatin tarayya da na jihohi har wa yau su riƙa ware wasu kuɗaɗe na musamman a matsayin tallafi don gudanar da binciken ilmi a wasu fannonin da muke da matuƙar buƙatuwa a cikinsu.  Alƙaluman bayanai daga wasu ƙasashen za su tabbatar da cewa tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa a wannan fanni bai taka kara ya karya ba idan ka gwama shi da na wasu ƙasashe.  A taƙaice dai, kason da gwamnatoci ke baiwa fannin kimiyya da ƙere-ƙere yayi ƙaranci sosai.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.