Nan Gaba Za A Fara Amfani Da Keɓantaccen Suna (Username), Maimakon Lambar Wayar Salula Don Rajista A Whatsapp

Manufar samar da wannan tsari dai, shi ne don tabbatar da ƙarin tsaro ga masu amfani da wannan manhaja, musamman na lambobin wayarsu da kowa ke iya gani a Zaurukan WhatsApp a duk sadda ka aika saƙo. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 9 ga watan Yuni, 2023.

118

A ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni ne labari ya bayyana cewa kamfanin Meta (Facebook), wanda ya mallaki manhajar hirar ga-ni-ga-ka mai suna WhatsApp, na shirin samar da wani tsari da zai baiwa masu amfani da manhajar damar amfani da keɓantaccen suna (username), maimakon amfani da lambar wayar salula kamar yadda yake a yanzu.   Wannan shi ne abin da shafin WABetaInfo ya tabbatar a cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi da ta gabata.

Shafin WBBetaInfo dai shafi ne da ya shahara wajen yin gwajin sababbin tsare-tsaren da ake shirin samarwa a manhajar WhatsApp, kamar yadda kamfanin Meta yake fitarwa lokaci zuwa lokaci.  A wannan sabon tsari, wanda a halin yanzu ake yin gwajinsa, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan zai bai wa mutane damar yin rajista ta amfani da suna keɓantacce, wato: “username” kenan           a WhatsApp, maimakon amfani da lambar wayar salula, kamar yadda yake a halin yanzu.

Manufar samar da wannan tsari dai, shi ne don tabbatar da ƙarin tsaro ga masu amfani da wannan manhaja, musamman na lambobin wayarsu da kowa ke iya gani a Zaurukan WhatsApp a duk sadda ka aika saƙo.  Manufa ta biyu ita ce don samar da ƙarin sauƙi wajen neman wanda kake nema ta amfani da suna maimakon lambar wayar salula.  Dalili na uku da ya hadda samar da wannan tsari shi ne buƙatuwar masu amfani da manhajar WhatsApp, musamman yadda satar account a WhatsApp ya zama ruwan dare a kullum.

A nasa ɓangare, kamfanin WBBetaInfo ya tabbatar da cewa a halin yanzu dai yana can yana gwajin wannan sabon tsari da ake shirin samarwa a WhatsApp, kuma ta la’akari da yadda tsarin yake, akwai alamar nan gaba ma za a ɓoye lambobin wayar salula; babu wanda zai iya ganin lambar wayarka ko da kuwa yana cikin abokanka.  Sai dai kawai yaga sunanka. Da wannan suna ne kuma zai iya nemo ka cikin sauƙi.  Kamfanin Meta dai ya fitar da wannan sabon zubin manhajar (Beta Version) ne don gwaji kamar yadda ya saba, ga ƙwararru dake gwajin sababbin zubin manhajar a duk sadda ake shirin fitar da sani sabon tsari.

Ana sa ran ɗora wannan sabon tsari a sabon zubin WhatsApp da za a fitar nan da wasu ‘yan lokuta dake tafe.  Idan har wannan sabon tsari ya tabbata, zai zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da manhajar WhatsApp ta samu tun sadda aka ƙirƙir wannan manhaja.

- Adv -

Sauye-Sauyen da Suka Gabata

Cikin shekarar 2009 ne wasu matasa biyu – Brian Acton da Jan Koun – tsofaffin ma’aikatan kamfanin Yahoo! suka ƙirƙiri manhajar da a halin yanzu ta rikiɗe zuwa Whatsapp, don aiwatar da sadarwa a tsakaninsu a gajeren zangon sadarwa (Local Area Network – LAN).  Cikin watan Nuwamba ne aka fitar da zubin farko na manhajar Whatsapp wadda ke aiki a kan wayar iPhone.  Daga baya aka samar da zubin WhatsApp dake aiki a kan wayoyin salula nau’in Android.  Cikin watan Oktoba na shekarar 2014 ne kamfanin Meta (Facebook, a wancan lokacin) ya saye wannan kamfani da manhaja ta WhatsApp kan zunzurutun kuɗi dala biliyan ashirin da biyu ($22bn).

Ya zuwa yau wannan manhaja ta WhatsApp ta samu ƙarin sauye-sauye masu ƙayatarwa.  Manya daga cikinsu sun haɗa da: samar da zubin manhajar WhatsApp na kwamfuta, da zubin manhajar WhatsApp na kasuwanci (WhatsApp Business) don taimak wa masu ƙananan sana’o’i.  Sai kuma sauyin da ya samar da tsarin kiran murya (Voice call) da na bidiyo (Video Call), da kuma tsarin ƙirƙira da aika saƙon murya (Voice note), da samar da hanyoyin tsaro da suka haɗa da amfani da tambarin yatsu wajen buɗe manhajar.

Daga cikin sauye-sauyen har wa yau akwai bayar da damar amfani da WhatsApp akan wayoyin salula sama da guda ɗaya, da lambar wayar salula ɗaya.  Wannan na cikin sauyin baya-bayan nan da aka ƙara.  A baya ba ka iya amfani da layin wayar salula mai rajistan WhatsApp a kan wayar salula sama da ɗaya.  Amma a watan da ya gabata kamfanin Meta ya samar da wannan tsari.  Kafin nan, an samar da tsarin saƙonni masu gushewa bayan wasu ‘yan sa’o’i ko kwanaki.  Wannan tsari shi ake kira: “Disappearing Messages”.  Kamfanin Meta ya samar da wannan tsari ne don taƙaita lokacin da wasu za su iya ganin saƙonninka, musamman a zurukan WhatsApp.  Idan ka saita wannan tsari, duk saƙonnin da ka aika ko wasu suka aiko maka zasu gushe ko su ɓace bayan kadadar lokaci ko sa’annan da ka saita hakan ya faru.

Sai sauyi na ƙarshe wanda ya ƙunshi bayar da damar gyara saƙo bayan ka rubuta ka aika, amma da sharaɗin tazarar lokacin bai shige mintina takwas ba.  Wannan sauyi zai taimaka matuƙa wajen ingancin saƙonni.  Idan ka gyara wani saƙo da ka rubuta a baya, waɗanda suka karanta saƙon a baya za su iya ganin alamar anyi wa saƙon gyara, amma ba za su iya sanin me aka gyara ba.  Idan wannan tsari na yin rajista da suna maimakon lambar wayar ya tabbata, zai zama shi ne tsari mafi girma da tasiri da aka ƙara wa manhajar WhatsApp a wannan shekara ta 2023.

 

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.