Fasahar “SMS”: Shekaru 30 Bayan Ƙirƙira (1)

Ga masu bibiyar wannan shafi namu mai albarka, shekaru kusan 11 da suka gabata mun gabatar da jerin maƙaloli na kusan rabin shekara kan wayar salula da dukkan ɓangarori da abubuwan da suka shafeta.  – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 9 ga watan Disamba, 2022.

194

Mabuɗin Kunnuwa

A ranar asabar da ta gabata (3 ga watan Disamba, 2022) ne fasahar aika gajeren saƙo ta wayar salula – saƙon tes –  wato: “Short Message Service” (SMS) ta cika shekaru 30 da ƙirƙira a aikace.  Hakan ya samo asali ne daga saƙon da wani matashi ɗan ƙasar Burtaniya mai suna Injiniya Neil Papworth ya aika ta wayar salular kamfanin Vodafone a ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 1992.  Ga hoton wayar salular da yayi amfani da ita nan a sama, ɗauke da saƙon da ya aika, wanda nauyinsa gaba ɗaya kilo 2 ne.

Kamar yadda fasahar Imel ta zama tagwaye ga fasahar Intanet, haka fasahar saƙon tes take tagwaye ga fasahar wayar salula.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, yadda fasahar wayar salula take haɓaka, haka fasahar saƙon tes ita ma take haɓaka.  Kamar yadda a ita ma fasahar Intanet ke haɓaka, haka fasahar Imel take haɓaka.  Dalili kuwa shi ne, dukkanin fasahohin sun taso ne cikin mahalli ɗaya, a kusan lokaci ɗaya, kuma a yanayi iri ɗaya; tare da cewa kowannensu aikinsa daban ne, haka ma manufar samarwa.  A zamanin yau da wahala ka samu wayar salula da ba ta iya aika saƙon tes; ma’ana, ba ta ɗauke da fasahar aika saƙon tes.  Sai in wayar da aka ƙirkira tsakanin shekarun 1940 ne zuwa 1989.

Ga masu bibiyar wannan shafi namu mai albarka, shekaru kusan 11 da suka gabata mun gabatar da jerin maƙaloli na kusan rabin shekara kan wayar salula da dukkan ɓangarori da abubuwan da suka shafeta.  A ɓangaren tarihin wayar salula, mun bayyana cewa asalin wayoyin salula na farko, kira kaɗai ake yi dasu; babu saƙon tes kuma babu fasahar Intanet.  Amma daga baya aka samar da fasahar saƙon tes, wato Short Message Service (SMS), wanda yake ta haɓaka iya girma da saurin haɓakar da wayoyin salula keyi.  Ta yaya hakan ya faru?

Samuwa da Bunƙasar Fasahar SMS

Duk da cewa saƙon tes na farko da aka fara aikawa ta wayar salula a watan Disamba ne na shekarar 1992, sai dai asalin ilimi da ƙa’idar wannan fasaha ya samo asali ne a shekarar 1984.  Wanda ya samar da wannan tunani da ƙa’ida kuwa shi ne Matti Makkonen, a ƙasar Jamus.  Ƙa’ida ce ta samar da wani kadadar sadarwa (wato killataccen tsarin sadarwa) don aikawa da karɓan gajeren saƙon tes tsakanin wayoyin salula.  Sai dai ba a ɗabbaƙa wannan ƙa’ida a aikace ba, sai sadda wannan matashi ɗan asalin ƙasar Burtaniya wato Injiniya Neil Papworth, lokacin yana aiki da kamfanin wayar salula mai suna Vodafone, ya gina wannan ƙa’ida a kan kwamfutarsa.  Daga nan sai yayi gwaji.  Kwamfa!  Nan take saƙon ya isa kan layin wayar da ya aika.  Cikin wani hira da aka yi dashi shekarun baya, ya ce shi kanshi bai ɗauka wannan gwaji da yayi zai yi aiki ba.  Ko ma dai mene ne, wannan fasaha ta samu, kuma ta haɓaka fiye da zaton waɗanda suka samar da tunani da asalinta.

Wannan dace da Papworth yayi dai ya zo daidai da ƙaddamar da ƙa’idar sadarwa ta wayar salula ta GSM ne a shekarar 1990.  Allah buwayi gagara misali.  Ƙarƙashin wannan ƙa’ida ne aka gina ƙa’idar sadar da rubutu ta hanyar layin sadarwar wayar tarho, sakamakon hijira da aka yi daga tsarin sadarwar “Analogue”, zuwa tsarin sadarwa ta “Digital”, wanda tsari ne dake sadar da bayanai a tsarin lambobin “0” da “1”.  Wataƙila da ya gwada yin hakan gabanin wannan lokaci ne, da ba a dace ba.  Komai da lokacinsa.

- Adv -

Asalin manufar samar da saƙon tes dai a farkon lamari, shi ne don aiwatar da sadarwa ne tsakanin ma’aikatan kamfanoni.  Kuma sadarwar kan zama tsakanin kadadar sadarwa ne guda ɗaya; kamar dai yadda asalin wayar salula take.  Wannan yasa saƙonnin ma kyauta ake aika su. Tun da ba wani kamfanin wayar salula bane yake bayar da damar yin hakan.

Nokia, 1994

Sai bayan shekaru biyu, wato a shekarar 1994, kamfanin Nokia ya samar da wayoyin salula masu ɗauke da fasahar wayar salula, kuma ya tanadi allon shigar da bayanai (Keyboard) tsarin T9, wanda ke sawwaƙe rubutawa da kuma aika saƙonnin ta wayoyinsa.  Kuma a lokacin ne kamfanin Nokia ya samar da sautin shigan saƙon tes (SMS Beep), wanda aka ƙirƙira ta hanyar haruffan da lambobi da ɗige-ɗige.

1997

A shekarar 1997 ne sauran kamfanonin wayar salula dake Turai suka ɗora fasahar saƙon tes, bayan kamfanin Nokia.  Wannan shi ne karon farko da fasahar saƙon tes ya fara zama-gari.  Kuma daga nan ne aka killace iya yawan haruffan da kowane saƙon tes zai iya ɗauka zuwa haruffa 160.  Wannan koyi ne kamfanonin suka yi da ƙa’idar wani masani ɗan ƙasar Jamus mai suna: Friedham Hillebrand, cewa saƙon da ya kai haruffa 160 shi ne wadataccen gajeren saƙo.  Wannan yasa jama’a suka fara amfani da taƙaitattun haruffa  na salon zance, don taƙaita yawan haruffa tare da samun damar isar da saƙon da ake son isarwa cikin ƙaidin saƙo ɗaya.

A farkon lamari mutane kan yi hakan ne saboda taƙaita yawan kuɗin da za a caje su wajen aikawa da saƙon.  Musamman idan ya faɗa cikin saƙo na biyu.  Kuma wannan al’adar ce ta zarce har zuwa yau, inda ake taƙaituwa kalmomi cikin hira a hanyoyin sadarwa na sada zumunta, irin su: WhatsApp, da Facebook Messenger, da Twitter da sauransu.  Daga wannan al’adar ce ma kamfanin Twitter ya taƙaita yawan saƙon da ake iya rubutawa a shafinsa zuwa haruffa 140 kacal.  Manufar Twitter ita ce, don ya zama duk irin wayar da kake amfani da ita wajen amfani da manhajar Twitter, za ka iya ganin saƙonnin da aka rubuta, kuma ka iya rubutawa.

A wannan lokaci, duk sadda ka wuce adadin haruffa 160, za ka ga an gicciye lamba 2 a gaban adadin (misali: 160/2).  Alamar cewa ka shiga saƙo na biyu kenan.  Kuma idan aka tashi cajanka, za a cajeka kuɗin saƙonni biyu ne, ba ɗaya ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.