Bangarorin Wayar Salula (2)

Kashi na tara cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

354

Sai bangare na biyar, wato Allon Shigar da Bayanai, ko Keypad a Turance.  Kamar yadda kowa ya sani, aikin wannan bangare shi ne taimaka wa mai mu’amala da wayar salula don shigar da lamban da yake son kira, ko amsa kira, ko rubuta sakon tes, ko karanta su, da kuma dukkan hanyoyin mu’amala da fasahohin da ke cikin wayar – irinsu daukan hoto, da daukan bidiyo, da kallon talabijin, da mu’amala da fasahar Intanet ko Bluetooth ko Infra-red, da dai sauransu.  Hakan ya faru ne saboda yana dauke ne da dukkan haruffa da lambobin da ake bukata don mu’amala da wayar.  Shi allon shigar da bayanai nau’i-nau’i ne. Ya danganci tsari da kimtsin wayar.  Galibin wayoyin salula suna dauke ne da allon shigar da bayanai guda daya.

Akwai wasu wayoyin salula na musamman masu dauke da alluna guda biyu.  Da wanda ke saman marfin wayar, da kuma wanda ke ciki idan an bude.  Sannan shi kanshi allon shigar da bayanai din ya sha bamban wajen tsari.  Akwai wanda tsarinsa iri daya ne da na kwamfutocin tafi-da-gidanka, wato Laptop.  Ire-iren wadannan su ake kira Standard Keypad, kuma suna dauke ne a manyan wayoyin salula na musamman nau’in Smartphones ko Blackberry a takaice.  Allon shigar da bayanai dai na manne ne da asalin injin wayar, mai dauke da gurabun da kowane harafi ko lamba ko alama/tambari ke zaune.  Duk lambar da ka matsa, za ta doshi gurbinta ne, don sanar da wayar irin harafi ko lambar da za ta nuna a fuskarta nan take.

Bayan Allon shigar da bayanai, bangare na gaba mai muhimmanci ga kowace wayar salula duk kankantarta, shi ne Ma’adanar Bayanai, wato Memory, a takaice.  Wannan ma’adana ne ke dauke da dukkan manhajojin da ke cikin wayar, wadanda take amfani dasu don baiwa mai mu’amala damar gudanar da abin da yake so, a lokaci ko yanayin da yake so.  Wannan ma’adana kuwa ta kasu kashi uku ne: akwai tabbatacciyar ma’adana, wacce ke dauke da babbar manhajar wayar. Wannan bangaren ma’adana shi ake kira Read Only Memory (ROM). 

Dukkan wata manhaja da ke cikin wayar na dauke ne cikin wannan ma’adana.  Da zarar ka kira kowace irin manhaja ce, sai manhajar ta shigo cikin ma’adanar wucin-gadi, wato bangaren ma’adana ta biyu kenan.  Wannan bangare kuma shi ake kira Random Access Memory (RAM).  Idan wayar tana kashe, wannan ma’adanar na zama holoko ce, wofintacciya; babu komai ciki.  Da zarar ka kunna wayarka, sai masarrafan da ke fuskar wayar (irinsu agogo da alamar yanayin sadarwa, da na cajin batir da sauran bayanai) su shigo cikin RAM, don fara gudanar da aikinsu.  Duk masarrafar da ka budo, cikin wannan ma’adana na RAM take zuwa.  Da zarar ka gama amfani da ita, ka rufe, sai bayananta su koma can cikin tabbatacciyar ma’adanar, wato Read Only Memory (ROM). 

Sai bangaren ma’adana ta uku, wacce sanyawa ake yi, ba wai tare ake gina shi da wayar ba.  Ma’ana, kana iya sanya mata a kowane lokaci, sannan a kowane lokaci kana iya cirewa, ko da kuwa wayar na kunne ne.  Wannan bangare shi ake kira Removable Storage.  Wannan nau’in kuwa ya kumshi Ma’adanar Katin Waya na musamman da ake iya saya a sanya mata, mai suna Memory Card (MMC). Wadannan su ne nau’ukan ma’adanai da galibin wayoyin salula ke mu’amala da su.  Kowace wayar salula na zuwa ne da ginanniyar ma’adanar bayanai – da nau’in ROM da na RAM.  Amma ba kowace waya bace ke zuwa da nau’in Removable Storage.  Har wa yau, tsawon rayuwar wadannan ma’adanai ya ta’allaka ne da irin nau’ukan bayanai da ake sanyawa cikinsu, da kuma tsabta ko ingancin bayanan, da kuma dacewarsu da muhallin ma’adanar.  Idan aka shigar musu da bayanai masu dauke da kwayoyin cuta, wato Virus, suna iya kamuwa nan take, har su lalata asalin manhajojin da ke dauke cikin wayar, ta kowane irin hali.  Bayanai kan haka na nan tafe in Allah Yaso.

- Adv -

Sai bangare na karshe da za mu dakata a kansa, ba don sun kare ba.  Wannan bangare kuwa shi ne marafan wayar; da na gaba da na baya da wanda ke tsakiya – ya danganci yanayin kirar wayar.  Kowa ya san amfani murfi ga wayoyin salula.  Kariya ne ga kura da datti da dauda da dukkan abin da zai iya zama barazana ga lafiyarta. Haka kariya ne ga lafiyar mai amfani da wayar, a yayin da take kunne.  Domin akwai abubuwan da ka iya cutar da shi idan babu murfi, musamman ta bangaren wutar lantarki.  Bayan nan, su kansu marafan ado ne ga wayar, wajen bata kima da kwarjini da kuma kamannin da ya dace da ita.

Tsari da kimtsin marafan wayar salula sun sha bamban wajen kira, dangane da kamfanin da ya kera wayar.  Akwai marafan da tsabar ado ne su.  Babu wahala sun fashe ko tsage idan aka mu’amalance su da tsauri.  Akwai wadanda kuma su a matsayin kariya kawai suke. Galibinsu za ka samu basu da wani kwarjini a ido, amma kuma suna da inganci wajen baiwa wayar kariya ga lafiyarta da na manhajojin da take dauke dasu.  Wayoyin salular da galibi aka kera su don ado (irin na mata misali), za ka samu basu da aminci sosai.

Bayan haka, akwai wayoyin da ke zuwa da marafa har guda biyu.  Daya na tare da ita, dayan kuma na ajiye.  Idan kana bukatar sauyi, sai ka tube ta ka sanya mata sabon.  Galibin wayoyin salula ana iya samun marafansu a saya a kasuwa.  Duk da yake akwai daidaiku wadanda baka samun murfinsu, muddin wanda ke tare da su ya lalace. Misali, wayoyin salula irin su Nokia 5320 XpressMusic tana zuwa ne da murfinta na asali, kuma kamfanin Nokia bai kera mata makwafi ba.  Idan suka lalace, sai dai ka saya mata jabu, wadanda ake kera su ba-kai-ba-gindi.  Wanda kuma galibinsu basu cika zama daram a jikin wayar ba.  In ma baka yi sa’a ba, su lalata maka wayar; musamman wajen amfani da allon shigar da bayanai.

Kafin mu shiga bayani kan Manhaja ko Ruhin Wayar Salula, akwai abin da na kira “Makale-makalen Wayar Salula”, ko kuma Mobile Phone Accessories.  Wadannan su ne ire-iren kayayyakin amfani da ake iya makala wa wayar salula don sauraron bayanai, ko kallon hotuna – masu motsi ko daskararru – ko mu’amala da fasahar Intanet, ko kuma shigarwa ko fitar da bayanai daga ma’adanar wayar.  Daga cikin wadannan kayayyaki akwai na’urar caji, ko Charger a turance.  Wanda ake amfani dashi wajen caja wayar, da kara mata karfi ta hanyar karfin sinadaran lantarki.  Sai lasifikar kunne (Head Phone), da lasifikar amsa kira (Hands-free), masu taimakawa wajen sauraron kade-kade da wake-wake, da kallace-kallace.

Har wa yau akwai Wayar Karba ko Shigar da Bayanai, wato Data Cable, ko USB Cable.  Da wannan waya za ka iya shigar da bayanai na sauti ko hotuna ko bidiyo, daga kwamfutarka zuwa wayar salula, ko kuma daga wayarka zuwa kwamfuta – ta kan tebur ce ko ta tafi-da-gidanka. Wannan tsari na shigar da bayanai ta hanyar USB Cable na amfani ne da kogon shigar bayanai mai suna Universal Serial Bus (USB), kuma yana cikin hanyoyin zamani da ake amfani dasu a kayayyakin sadarwa na zamani.

Abu na karshe da za mu dakata a kai shi ne abin da har wa yau na sanya wa suna da “Tsinken Ligidi”, ko kuma Joy Stick, a tsarin sadarwa ta zamani.  Wannan tsinke ana amfani dashi ne wajen shigar da bayanai ko lodo su ko kuma shiga wurare a cikin wayar salula.  Galibin wayoyin salular zamani na musamman, suna zuwa ne da wannan tsinke mai matukar tasiri wajen sadarwa.  Saboda sawwake sadarwa da mu’amala da wayar salula musamman a lokutan da mai mu’amala da wayar ke cikin natsuwa ko nishadi.  Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin karikitan da ake iya makala wa wayar salula da sawwake mu’amala a lokuta dabam-daban.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.