Baban Sadik

Baban Sadik marubuci ne, kuma mai bincike a fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwar zamani da tasirinsu ga al'umma. Ya tanadi wannan shafi ne don taskance dukkan maƙalolin da yake gabatarwa a shafinsa na "Kimiyya da Ƙere-Ƙere" a jaridar AMINIYA wanda ya faro tun shekarar 2006.

Asalin ‘Yan Dandatsa (Hackers) da Alakarsu da Kwayar Cutar Kwamfuta (1)

A makon da ya gabata mun fara kawo bayanai ne kan kwayoyin cutar kwamfuta da tsarin su da yadda suke yaduwa, da kuma tasirin su.  A karshe kuma sai muka kawo nau’ukan wadannan cututtuka da ke damun kwamfuta da hana ta sakewa.  A yau idan Allah Ya yarda za mu ci gaba da kwararo bayanai ne ; za mu san su waye ke da alhakin yada ire-iren wadannan kwayoyin cututtuka da kuma irin mummunan abin da suke haifarwa a duniya gaba daya.  Za mu san shahararren suna ko lakabin da aka san su dashi a duniyar fasahar sadarwa a yau, da kuma tarihin wannan sana’a tasu mai mummunan sakamako.  Idan Allah Ya bamu dama, za mu kawo bayani kan manufar wadannan mutane ; me  yasa suke wannan aiki?  

Karin Bayani...

Ma’ana da Asalin Kwayar Cutar Kwamfuta (Virus)

Daga wannan mako in Allah Ya yarda, za mu fara bayanai kan manyan matsalolin da ke damun kwamfuta da masu amfani da ita a wannan zamani da muke musamman.  Kamar dai yadda dan Adam yake ne; yana da damuwoyi da dama da ke masa kaidi wajen tafiyar da rayuwa ingantacciya kuma cikin sauki.  Haka na’urar kwamfuta take; akwai matsaloli da ke mata karan-tsaye wajen gudanar da ayyukan da aka kera ta don yin su, cikin sauki.  Wadannan matsaloli suna da yawa, amma za mu dauki wadanda suka shafi lafiyarta da kwakwalwarta ne kadai, don su ne manyan matsalolin da suka fi kowanne tasiri wajen dama mata lissafi, musamman cikin wannan zamani da aka samu kwararru kan ilimin ta, birjik a duniya.

Karin Bayani...

Mu Leka Duniyar ‘Yan Dandatsa (Hackers) (1)

‘Yan Dandatsa kwararru ne kan harkar kwamfuta da abin da ya shafi ruhinta, masu amfani da kwarewarsu wajen shiga kwamfutocin mutane ba tare da izni ba, a nesa ne ko a kusa ; masu aiko ma kwamfutoci cututtuka da dama, don satan bayanai ko aikin leken asiri.  A takaice dai mutane ne masu mummunar manufa wajen kwarewarsu.  A yau za mu leka duniyarsu ne don sanin hakikanin tsarin rayuwarsu : irin sunaye ko lakubbansu, gidajen yanar sadarwarsu, shahararrun littafai kan aikinsu, dabi’unsu da addininsu na dandatsanci da kuma shahararru cikin finafinan da aka yi kan sana’arsu. Ga fili ga mai doki.

Karin Bayani...

Bunkasa Harshe da Al’ummar Hausawa: Daga Adabi Zuwa Kimiyya da Fasahar Sadarwa ta Zamani (1)

A bayyane yake cewa abin da yafi yaduwa na littattafai cikin harshen Hausa labaru ne kirkirarru, wanda kuma galibi jigon soyayya yafi yawa a ciki. Ta la’akari da yadda duniya ke ci gaba ta hanyar kimiyyar sadarwa da kere-kere a yau, akwai bukatar sauya salon rubutu cikin harshen Hausa zuwa wadannan fannoni, don taimaka wa al’umma wajen wayar mata da kai kan halin da duniya ke ciki. Wannan yasa daga yau za mu fara nazarin rubuce-rubucen Hausa don tantance fannonin da suka dangance su, a karshe mu ga shin, ina muka dosa ne dangane da sauran fannonin ilimi da rayuwa!

Karin Bayani...