Baban Sadik

Idan baka samu kasida ko maudu’in da kake nema ba…

A LURA:  Dukkan kasidun dake wannan shafi suna da tsayi, domin kasidu ne da suka kunshi bincike na ilimi, ba wai labaru bane.  Don haka, idan tsayinsu ya gundureka,  kayi hakuri.  Dabi’ar mahallin ne.

Fasaha
Baban Sadik

Tsarin Sadarwa Tsakanin Kwamfutoci (Networking) (2)

A cikin kasidar da ta gabata makon jiya ne mai karatu ya samu bayanai kan tsarin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, abin daa Turance ake kira Computer Networking.  Bayan ‘yar gajeriyar gabatarwa, mun kawo bayani kan ma’ana da kuma nau’ukan tsarin sadarwan da ke tsakanin kwamfutoci, inda daga karshe muka nuna ma mai karatu cewa samun cikakkiyar fahimta kan irin tsarin da kwamfutoci ke sadar da bayanai a tsakaninsu ba abu bane mai sauki, musamman ma ganin cewa kashi sittin ko sama da haka na alakar da ke tsakanin ruhin kowace irin na’ura ta sadarwa da gangar-jikinta, ba alaka bace da za a iya gani a zahiri, sam.  Don haka sai dai kawai a kwatanta ma mai karatu don ya samu kiyastaccen tsarin a kwakwalwarsa.  Amma duk da haka, wannan alaka na nan, kuma tabbatacciya ce.

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Kwamfuta da Bangarorinta (1)

A yau kuma ga mu dauke da bayanai, a takaice, kan kwamfuta da manhajojinta.  Duk da yake wannan shi ne abin da ya kamata a ce mun fara dashi, amma dokin sanin Intanet da karikitanta ne suka shagaltar da mu.  Don haka tunda mun kawo wani matsayi ko mataki wajen sanin hakikanin Intanet da yadda ake tafiyar da rayuwa a kanta, dole mu koma tushe, ko mazaunin da wannan fasaha ke dogaro wajen aiwatar da dukkan abin da za mu ci gaba da kawo bayanai kansu.  Wanann ya sa za mu yi bayani kan Kwamfuta, ita kanta, da kuma ruhin da ke gudanar da ita.  Na tabbata daga lokacin da mai karatu ya karanta wadannan bayanai, insha’Allahu zai samu sauyin mataki, wajen fahimtar darussan da za su biyo baya.  Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau Kura.

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Dandatsanci: Wani Sabon Salon Yaki Tsakanin Kasashen Duniya (1)

Ga alama wani sabon salon yaki na kokarin bunkasa a tsakanin kasashe. A baya mun san galibin yaki tsakanin kasashe ko dai ya zama na makami ne, ko kuma na cacar baki da diflomasiyya. Amma a halin yanzu kasashe na yakar juna ta hanyar aikin kutse wato dandatsanci kenan ko “Hacking”, ga kwamfutocin wata kasa ‘yar uwarta. A yau za mu fara duba wannan sabon salon yaki a tsakanin kasashe. A sha karatu lafiya.

Sauran bayanai »