![Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2023/10/Wayar-Salula-1.png)
Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (1)
Manyan babbar manhajar wayar salula dake cin kasuwansu yanzu su ne: “Android”, wanda kamfanin Alphabet (ko Google) yake mallaka tare da bayar da lasisinsa ga sauran kamfanonin ƙera wayar salula dake duniya. Sai kuma babbar manhajar wayar salula mai suna “iOS” na kamfanin Apple, wanda ke ɗauke kan manyan wayoyin salula da kusan suka fi kowace irin wayar salula tsada a duniya. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 4 ga watan Agusta, 2023.