Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (15)

Bambancin Kamfani

Kashin farko na wayar salula da galibin kamfanonin ƙera wayar salula na duniya ke ƙerawa su ne wayoyi masu araha.  Waɗannan su ake kira: “Budget Phones”.  Wato wayoyin salular masu ƙaramin ƙarfi.  Galibinsu farashinsu ba ya wuce dala 100 zuwa 150. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 10 ga watan Nuwamba, 2023.

40

Bambancin Kamfani

Daga cikin manyan dalilan dake haddasa araha ko tsadar wayar salula na zamani akwai kamfanin da ke ƙera wayoyin salulan.  Kowane kamfani yana da nashi tsari, da nashi kintsi da irin nau’ukan abubuwan da yake ɗorawa ko ginawa a kan wayoyin da yake ƙerawa.  Waɗannan nau’ukan tsare-tsare ne ke bambanta shi da sauran kamfanonin da ke gasa dashi a fannin.  Amma kafin nan, zai dace mai karatu yasan manufofin ƙera wayar salula na zamani a duniyar yau, ta la’akari da tsada ko araha.  Akwai salo guda uku da kamfanonin wayar salula ke amfani dasu:

Masu Ƙaramin Ƙarfi – Budget Phones

Kashin farko na wayar salula da galibin kamfanonin ƙera wayar salula na duniya ke ƙerawa su ne wayoyi masu araha.  Waɗannan su ake kira: “Budget Phones”.  Wato wayoyin salular masu ƙaramin ƙarfi.  Galibinsu farashinsu ba ya wuce dala 100 zuwa 150.  Idan aka canza wannan adadi na kuɗi zuwa nairan Najeriya za ka ga kuɗi ne mai ɗimbin yawa.  Domin ya wuce dubu 100.  Wannan ya faru ne saboda ƙarancin darajar kuɗin ƙasarmu.  A taƙaice dai, kashi na farko cikin nau’ukan wayoyin da kamfanonin ƙera wayar salula ke ƙerawa su ne masu ƙarancin farashi, kamar yadda na sanar a sama.

Waɗannan wayoyi da ake ƙerawa na masu ƙaramin ƙarfi dai kamar sauran wayoyi suke wajen abubuwan amfani, sai dai suna da naƙasa ta wasu ɓangarorin, musamman abin da ya shafi ingancin sikirin, da ƙarancin ma’adanar waya (Storage), da ƙarancin mizanin masarrafar bayanai (Processor), da kuma ƙarancin mizanin batir, a wasu lokutan.  Kuma duk da cewa idan an ƙera su ana sayar dasu a kasuwar da ake sayar da waɗansa suka ɗara su inganci, sai dai an fi kawo su ƙasashe masu tosowa, waɗanda suke da ƙarancin samu.  Waɗannan ƙasashe kuwa galibinsu na nahiyar Asiya ne, da Kudancin Amurka (Latin America) da kuma nahiyar Afirka baki ɗaya.

Sai dai wani abin tambaya a nan shi ne, shin, dukkan kamfanonin ƙera wayoyin salula ne ke ƙera wayoyi a wannan tsarin?  Amsar ita ce a a.  Kamfanin Apple, misali, ba ya ƙera wayoyin masu ƙaramin ƙarfi, wato “Budget Phones”, in ka keɓance wayar iPhone SE da kamfanin ya ƙera a shekarar 2016, da 2020, sadda cutar korona ta killace duniya wuri ɗaya, harkokin kasuwanci suka tsaya cik, kamfanonin wayar salula suka fara hasara mara misaltuwa.  A halin yanzu ma akwai raɗe-raɗin kamfnain zai sake fitar wannan nau’in wayar salula da ake tsammanin zai sa wa suna: iPhone SE 8. Wannan waya dai, a iya tarihin kamfanin Apple, ita ce wayar da ake ƙididdigeta a sahun wayoyi masu ƙaramin ƙarfi.  A ɗaya ɓangaren kuma, akwai kamfanonin da su kuma wayoyin masu ƙaramin ƙarfi kaɗai suke ƙerawa.  Bayani kansu nan tafe.

- Adv -

Matsakaitan Farashi – Mid-Range Phones

Kashi na biyu na wayoyin da kamfanonin ƙera wayar salula ke ƙerawa ta la’akari da tsada ko araha, shi ne wayoyi matsakaita farashi.  Wannan su ake kira: “Mid-range Phones”.  Su farashinsu bai yi sama sosai ba, kuma bai ƙasa sosai ba.  Su ne wayoyin da farashinsu ke farawa daga dala 200 ($200) zuwa 450 ($450).  A Najeriya kuma kamar kace daga naira 200,000 (N200,000) kenan zuwa 500,000 (N500,000).  Bayan kashin farko, waɗannan su ne kashi mafi yawa daga adadin wayoyin da kamfanonin wayar salula ke ƙerawa.  Saboda galibin masu sayan wayar salula a ƙasashen duniya suna sayansu ne.  Wato adadin masu sayan wayoyi masu matsakaicin farashi sun ɗara na masu ƙarancin farasha yawa.  Amma a ƙasashe masu tasowa, adadin masu sayan masu ƙarancin farashi ya fi yawa.  Dalilin hakan kuwa a fili yake.

Wayoyin dake wannan ɗabaƙa dai suna ɗauke ne da galibin abubuwan morewa da wayoyin salula ke ɗauke dasu. Ina nufin wayoyin salula na alfarma.  Kusan dukkan kamfanonin ƙera wayar salula na ƙera wayoyin dake wannan ɗabaƙa, domin su ne aka fi saye. Galbinsu na ɗauke ne da ingantattun ɓangarorin waya, irin su sikirin, da mizanin batir mai girma, da mizani mai girma na ma’adanar waya, da kuma ingantaccen masarrafar sarrafa bayanai na waya, wato: “Processor” kenan.  Wayoyin dake wannan ɗabaƙa sun haɗa da wayoyin Samsung Galaxy A24, da Samsung Galaxy A34 da dai sauran ire-irensu.

Wayoyin Alfarma – Flagship Phones

Wannan shi ne ɗabaƙa na ƙarshe na sahun wayoyin da kamfanonin waya ke ƙerawa.  Su ne wayoyin da suka fi kowace waya tsada a duniya.  Ana ƙera su ne don masu alfarma, da masu sha’awan wayoyi masu tsada, da kuma shugabannin ƙasashe.  Ire-iren waɗannan wayoyi sun kasu kashi biyu. Kashin farko su ne waɗanda kamfanonin ke ƙerawa da kansu, don sayarwa ga masu buƙata. Kashi na biyu kuma su ne waɗanda wasu masu hannu da shuni – hamshaƙan ‘yan kasuwa, da shubabannin siyasa na ƙasashen duniya, irin shugabannin ƙasa da sauransu – ke sa a ƙera musu.  Su wannan kaso idan an ƙera su, ba a sake ƙera wa wani irinsu a duniya.  Misali, wayar da za a ƙera wa shugaban ƙasar Amurka, ba wanda za ta taɓa ganinsa da irin ta.  Sai dai kawai suna ya haɗa su, amma ba abin da wayar ta ƙunsa ba.

Wayoyin masu alfarma dai sun fi ƙaranci wajen ƙerawa, tunda an san ba kowa ke iya sayensu ba.  kuma za ka samu suna ɗauke ne da kowace irin siffa mai ƙayatarwa – na zahiri ne ko na manhaja.  Ko a hannu ka riƙe wayar, ka san ta sha bamban da sauran wayoyin salula, ta wajen nauyinta, da santsin taɓawa, da kuma kauri ko sirantaka, ya danganta salon da ake yayi.  Sannan kana ganin zanen dake jikinta ka san ba na talaka bane.  A ɗaya ɓangaren kuma, komai na ɓangarorinta jikinta za ka samu mai inganci ne.  Farashin wannan kaso na wayoyin salula na farawa ne daga dala 700 zuwa abin da ya sawwaƙa.  Farashinta ba shi da iyaka a sama.  Tirƙashi!  Babban goro sai magogin ƙarfe.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.