Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (14)

Siffofin Kyamarar Wayar Salula

A zamunnan baya, idan kana son ɗaukan hoto akwai maɓalli da za ka matsa a jikin kyamarar.  Kyamarorin zamani ma, wato DSLR, duk suna zuwa da wannan maɓalli su ma.  Daga baya ne aka samar da hanyoyin amfani da fasahar blutud (Bluetooth) don ɗaukan hoto kai tsaye.  – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 3 ga watan Nuwamba, 2023.

76

Siffofin Kyamarar Wayar Salula

Kyamarar wayar salula na da siffofi daban-daban da suka bambanta ta da kyamarar ɗaukan hoto da bidiyo na zamani.  Waɗannan siffofin ne za mu yi bayani a kansu a wannan mako. Kuma a ƙarshe mai karatu zai fahimci lallai nau’i da yanayin kyamarar wayar salula na cikin abin da ke bambanta farashin wayoyi a tsakaninsu.

Siffar farko da galibin kyamarar zamani ke ɗauka da ita, shi ne tsarin jawo abu mai nesa zuwa kusa.  Wannan tsari shi ake kira Zooming.  A kyamarorin zamani da ake kira DSLR, wannan siffa na goye ne a kan tabaran kyamarar, wato Lens kenan. Idan ka kalli tabaran kyamara za ka ga wata roba baƙa naɗaɗɗiya da ake iya juya ta gaba ko baya.  Tana ɗauke da lambobi a jikinta.  Idan ana son jawo abu mai nisa zuwa kusa don samun haƙiƙanin surarsa, sai a murɗa ta.  Wannan nau’i shi ake kira: Optical Zoom. 

A ɗaya ɓangaren kuma, kyamarar wayoyin salular zamani su ma suna zuwa da wannan siffa ta janyo abu mai nisa zuwa kusa, amma nasu a ɗamfare yake da manhajar kyamarar.  Idan kana son amfani da ita sai ka fincini fuskar manhajar da yatsunka sau ɗaya ko sau biyu; iya gwargwadon yadda aka tsara kyamarar.  Wannan shi kuma ake kira Digital Zoom.  Amfanin dukkansu dai shi ne samun damar janyo abu mai nisa zuwa kusa.

Daga cikin siffofin kyamarar zamani akwai yanayi ko salon da kyamara ke ɗaukan hoto ko bidiyo dashi.  Wannan salo shi ake kira Camera Mode.  Salon ɗauka na farko shi ake kira Auto Mode.  Wannan shi ne tsarin ɗaukan hoto da kowace kyamara ke zuwa dashi kai tsaye, don baiwa mai waya ko kyamarar damar ɗaukan hoto cikin sauƙi ba sai yasha wahala ba.  Wannan salo na ɗauke ne da tsare-tsare na gama-gari da ake kira Default Settings.  Kuma ga makoyi wajen ɗaukan hoto, yana taimakawa matuƙa kafin ka fara ƙwarewa wajen iya ɗaukan hoto.

Sai salo na biyu da ake kira Manual Mode, ko kuma Pro Mode, a wasu wayoyin – musamman wayoyin Huawei da Samsung.  Wannan salo shi kuma an samar dashi ne ga ƙwararru, waɗanda suka san yadda ake ɗaukan hoto.  Su za su saita yawan hasken da suke buƙata, da nisa ko kusancin kyamarar da wanda za a ɗauka, da saurin cafko haske da tabaran kyamaran ke yi; dukkan wannan da hannu ake saita su.  Shi yasa ma ake kira tsarin da suna Manual Mode.  Waton ɗaukan hoto da ake saita tsare-tsarensa da hannu.

- Adv -

Sai wasu nau’ukan salon ɗaukan hoto da suka zo a tsare, masu la’akari da wani yanayi na musamman.  Daga cikinsu akwai Program Mode, da Sport Mode wanda ke amfani da tsarin cafko haske cikin gaggawa don riskar gujegujen masu wasannin ƙwallon ƙafa ko ƙwallon kwando, misali.  Sannan akwai salon da ya ƙunshi tsare-tsaren ɗaukan hoto a waje, wanda ake kira Outdoor Mode.  Akwai kuma Portrait Mode dake ɗaukan hoton mutum ko wani abu a killace, da bashi mahimmanci, tare da tauwaye surar sauran abubuwan dake bayanshi ko gefensa.

Daga cikin shahararrun salon ɗaukan hoto akwai Night Mode, wanda ake amfani dashi wajen ɗaukan hoto cikin dare ko mahallin dake ɗauke da duhu ko ƙarancin haske, ko da kuwa da rana ne.  Daga cikin raunin kyamarar wayar salula akwai rashin iya ɗaukan hoto a wuri mai duhu ko ƙarancin haske.  Shi yasa aka samar da wannan tsari na musamman, don bai wa mutane damar ɗaukan hoton cikin sauƙi.  Bayan wannan, daga cikin siffofinsu akwai ɗabi’ar daidaita tabaran kyamarar kai tsaye, wato Stablization.  Wannan ɗabi’a dai ta ƙunshi gyatta kyamarar ne yayin ɗaukan hoton, don kauce wa girgiɗi da raurawan hannu.  Domin hakan na iya sa hoton ya fito bishi-bishi; a kasa gane wanda ke cikin hoton ba.  Wannan tsari na Stablization na samuwa ne ta hanyoyi guda biyu.  Na farko ta amfani da dirkar kyamara, wato Camera Tripod.  Ɗora kyamara ko wayar salula akan dirka na taimaka mata ainun wajen ɗaukan hoto cikin sauƙi da salama.  Sai hanya ta biyu da ta ƙunshi tsarin daidaito da wasu wayoyin ke zuwa dashi tun sadda aka ƙera su.  Wannan shi ake kira In-Built Stablization.

A ƙarshe kuma akwai tsari ko salon ɗaukan hoto cikin saiɓi, ko da kuwa wanda aka ɗauka yana gudu ne.  Wannan salo shi ake kira Slow Motion Mode.  Sai dai ba kowace wayar salula ke zuwa da kyamara mai ɗauke da wannan salon ɗaukan hoto ba.

Waɗannan, a taƙaice, su ne shahararrun siffofin kyamarorin wayar salula na zamani.  Abu na gaba shi ne bayani kan hanyoyin ɗaukan hoto da kymarori ke zuwa dashi.

A zamunnan baya, idan kana son ɗaukan hoto akwai maɓalli da za ka matsa a jikin kyamarar.  Kyamarorin zamani ma, wato DSLR, duk suna zuwa da wannan maɓalli su ma.  Daga baya ne aka samar da hanyoyin amfani da fasahar blutud (Bluetooth) don ɗaukan hoto kai tsaye.  Wasu kuma kan zo da na’urar rimot.

Sai dai su kuma kyamarorin wayar salula yanayinsu ya sha bamban da na’urorin kyamara masu zaman kansu.  Hanyoyin ɗaukan hoto a kyamarar wayar salula sun ƙunshi latsa alamar ɗauka dake fuskar wayar kai tsaye.  Hanya ta biyu kuma ta ƙunshi amfani da maɓallin ƙara amo ko sautin waya.  Hanya ta uku ta ƙunshi da murmushi.  Wannan ta fi samuwa a galibin manyan wayoyin salula. Da zarar ka gama gyattawa, kana yin murmushi wayar za ta ɗauke ka kai tsaye.  Sannan akwai waɗanda ke amfani da tafin hannu.  Da zarar ka ɗaga tafin hannunka ka wulƙita shi, nan take sai ta ɗauki hoto.

Waɗannan su ne hanyoyin ɗaukan hoto shahararru a kyamarorin wayar salula na zamani.  A makon gobe in Allah ya kaimu, za mu yi bayani a karo na ƙarshe kan dalilan dake sa tsada ko arahar wayar salula a wannan zamani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.