![Mahimman Abubuwan Ci Gaba a Fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa a Shekarar 2021 (1)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2022/02/exoplanet.jpg)
Mahimman Abubuwan Ci Gaba a Fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa a Shekarar 2021 (1)
An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 11 ga watan Fabrairu, 2022.
Makaloli a fannin kimiyya da fasaha!
An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 11 ga watan Fabrairu, 2022.
Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.
Kamar yadda aka saba lokaci zuwa lokaci, ga wasu daga cikin sakonninku nan. Wannan kashin farko ne, a mako mai zuwa in Allah yaso zan turo kasha na biyu. Don Allah a rika turo sakonni masu ma’ana, kuma a rika rubuto wuri da sunan mai aikowa. Allah sa mu dace, amin.
A cikin kasidar da ta gabata makon jiya ne mai karatu ya samu bayanai kan tsarin sadarwa a tsakanin kwamfutoci, abin daa Turance ake kira Computer Networking. Bayan ‘yar gajeriyar gabatarwa, mun kawo bayani kan ma’ana da kuma nau’ukan tsarin sadarwan da ke tsakanin kwamfutoci, inda daga karshe muka nuna ma mai karatu cewa samun cikakkiyar fahimta kan irin tsarin da kwamfutoci ke sadar da bayanai a tsakaninsu ba abu bane mai sauki, musamman ma ganin cewa kashi sittin ko sama da haka na alakar da ke tsakanin ruhin kowace irin na’ura ta sadarwa da gangar-jikinta, ba alaka bace da za a iya gani a zahiri, sam. Don haka sai dai kawai a kwatanta ma mai karatu don ya samu kiyastaccen tsarin a kwakwalwarsa. Amma duk da haka, wannan alaka na nan, kuma tabbatacciya ce.
Fasahar Intanet ta samo asali ne sanadiyyar musayar bayanai da kwamfutoci ke yi a tsakaninsu. Yau za mu dubi yadda kwamfutoci ke aiwatar da irin wannan sadarwa, wanda ya sauya duniya ta bangaren sadarwa.
Kashi na biyu cikin nazarin da muka faro kan kwamfuta da dukkan bangarorinta mahimmai. A sha karatu lafiya.
A yau kuma ga mu dauke da bayanai, a takaice, kan kwamfuta da manhajojinta. Duk da yake wannan shi ne abin da ya kamata a ce mun fara dashi, amma dokin sanin Intanet da karikitanta ne suka shagaltar da mu. Don haka tunda mun kawo wani matsayi ko mataki wajen sanin hakikanin Intanet da yadda ake tafiyar da rayuwa a kanta, dole mu koma tushe, ko mazaunin da wannan fasaha ke dogaro wajen aiwatar da dukkan abin da za mu ci gaba da kawo bayanai kansu. Wanann ya sa za mu yi bayani kan Kwamfuta, ita kanta, da kuma ruhin da ke gudanar da ita. Na tabbata daga lokacin da mai karatu ya karanta wadannan bayanai, insha’Allahu zai samu sauyin mataki, wajen fahimtar darussan da za su biyo baya. Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau Kura.
Manhajar WhatsApp na cikin sababbin manhajojin wayar salula (Mobile Application) da suke tashe a yanzu, kuma ana hasashen nan gaba sai ta kere sauran manhajoji. A yau za mu dubi yadda tsari da kintsin wannan manhaja yake ne. A sha karatu lafiya.