![Tasirin Hadarin Nukiliyar Kasar Japan Ga Duniya](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2017/03/japan.jpg)
Tasirin Hadarin Nukiliyar Kasar Japan Ga Duniya
Cikin watan da ya gabata ne kasar Jafan ta fuskanci wata girgizar kasa mai girma da karfin gaske, wanda kuma sanadiyyar haka nan take tekun kasar ya kama ambaliya (Tsunami). Wannan ambaliya ya kwashe gidaje da garuruwa da jama’a sama da dubu talatin – tsakanin wadanda suka mutu da wadanda aka rasa inda suke – sannan ya yi mummunar tasiri a kan cibiyoyin nukiliyar kasar, wadanda suke cikin tsibiri, daidai inda wannan lamari ya auku. A yanzu wadannan cibiyoyi na fuskantar barazanar fashewa a kowane lokaci, kuma tuni har an fara samun yaduwar mummunar tururin guba (radiation) da ke fitowa daga cikinsu. Wannan tasa muka kawo wa masu karatu bayanai kan mummunar tasirin wannan abu dake kokarin bayyana muddin ba a dauki wani mataki mai tasiri ba. Domin wannan matsala muddin ta fara yaduwa, ba kasar Jafan kadai za ta shafa ba, kusan duk duniya baki daya na cikin hadari. Saboda abu ne mai gamewa ba wai a jiki ko ruwa ko gidaje ko kasa kadai ba, har da iskar da ake shaka.