Rayuwata a Takaice

Suna na Abdullahi Salihu Abubakar, amma galibin jama’a sun fi sanina da “Baban Sadik”.  An kuma haife ni ne a Unguwar Hausawa ta Garki Village da ke Karamar Hukumar Municipal, a babban birnin tarayya ta Abuja, cikin shekarar 1976.   Mahaifi na shi ne Malam Abubakar Salihu, shi kuma Salihu kakana ne.  Asalin kakannina (da ma sauran mazauna Unguwar Hausawa a Garki Village) daga arewacin Najeriya suke.  Zama ne ya kawo su wannan wuri, wacce a wancan lokaci ta zama kamar zango, kusan shekaru dari biyu da suka gabata. Kuma ma saboda tsawon zamani da halin zamantakewa, a halin yanzu duk mun rikide mun zama Hausawan Abuja.   Na yi makarantar Firamare, da Sakandare da kuma Jami’a duk a Abuja.  A halin yanzu ina da digiri a fannin Tattalin Arzkirin Kasa (Economics), wanda na samu daga Jami’ar Abuja.  Ina  kuma kan neman ilmin Kur’ani da sauran fannonin Ilmin musulunci har yanzu.

Ni mutum ne mai sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance.  Ina kuma son binciken ilmi kan fannonin ilmi irin su Tattalin Arzikin Kasa (Economics), da Fasahar Sadarwar Zamani (Information Technology), da Fasahar Intanet, da Tsarin Harsuna (Linguistics), da Fassara (Translation), da Aikin Jarida (Journalism) da Kimiyya (Science) da dai sauran fannoni masu nasaba da wadannan.  Allah Ya hore min juriyar karatu da rubutu iya gwargwado. A halin yanzu na rubuta littafi kan fasahar Intanet, mai suna “Fasahar Intanet a Sawwake”, wanda ake gab da bugawa. Akwai kuma wadanda nake kan rubutawa a halin yanzu, kamar “Tsarin Mu’amala da Fasahar Intanet”, da kuma “Wayar Salula da Tsarin Amfani da Ita”.  Sai kuma kasidun da nake rubutawa a shafina dake jaridar AMINIYA a duk mako.

Ayyukan da nake gudanarwa sun hada da:

 • Bincike kan hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani da tasirinsu ga al’umma;
 • Rubuce-rubuce kan fannonin kimiyya da fasahar sadarwa;
 • Fassara (Turanci => Hausa, Hausa => Turanci, Larabci => Turanci, Turanci => Larabci, Hausa => Larabci, Larabci => Hausa);
 • Fassara Gidaje da Shafukan Yanar Sadarwa (Web Localization);
 • Gina Gidan Yanar Sadarwa (Web Design & Development);
 • Karantar da tsarin gina manhajar kwamfuta (Programming)

A halin yanzu ina zaune ne a Sabon Garin Garki (New Garki Town) da ke nan Abuja.  Ina da mata, kuma Allah Ya albarkaceni da zuri’a.


A cikin watan Nuwamba, 2016 ne na cika shekaru 10 da fara gabatar da kasidu a shafina dake jaridar AMINIYA mai take: “Kimiyya da Kere-kere.”   Abin ya faro ne cikin watan Nuwamba 2006.  Da yawa cikin masu karatu kan bukaci sanin tarihina da rayuwata da yadda a cewarsu na kai wannan matsayi.  Wannan yasa na tanadi wannan shafi don bai wa mai karatu da masu ziyara sanin wani abu daga cikin rayuwata a wannan fanni.

Wannan shafi ne mai dauke da kasidu da makaloli kan fannin ilimin KIMIYYA DA FASAHA (Science and Technology), musamman fasahar sadarwa da kere-kere da kuma sararin samaniya.  A wannan shafi za ka samu kasidu kan bangarorin ilimi kamar haka:

 • Kwamfuta (Computer)
 • Fasahar Intanet (Internet)
 • Fasahar Imel (Email)
 • Kariyar Bayanai (Information Security)
 • Fasahar Rediyo (Radio Technology)
 • Kimiyyar Sararin Samaniya (Astronomy)
 • Kimiyyar Haske (Laser Technology)
 • Fannin Kwakwalwa da Zuciya (Neurotechnology)
 • Fannin Dabi’u da Halayya a Fagen Sadarwa (Cyberpsychology)
 • Dandalin Abota (Social Media)
 • Kimiyyar Kur’ani da ta Zamani (Qur’anic and Conventional Sciences)
 • Fannin Sadarwa (Communication Sciences)

- Adv -

Asalin wadannan kasidu dai rubuce-rubuce ne da na faro tun shekarar 2006 a jaridar AMINIYA, karkashin shafi mai take: “Fasahar Sadarwa,” wanda daga baya na sauya wa take zuwa: “Kimiyya da Kere-kere.”

Na hallata daukawa, da kwafa, da sauya duk wani abin da ya shafi rubutuna don dalilai na BINCIKEN ILIMI, KO NISHADI, KO KARUWAR ILIMI, KO KARANTAR DA WASU (MUSAMMAN MATA DA KANANAN YARA), kyauta; bai sai an nemi izinina ba.

Amma duk mai bukatar amfani da wani bangare na rubutuna dake wannan shafi ko duk inda yaci karo dashi a Intanet ne ko jarida, don DALILAI NA KASUWANCI, DOLE NE YA TUNTUBE NI KAFIN YIN HAKAN.

Hakkin mallakar duk rubuce-rubucena nawa ne!


Dangane da tarihin rayuwata a wannan fanni, akwai kasidu guda 4 da na taba rubutawa kan hakan, cikin shekarar 2014.  Za a iya samunsu a wadannan shafuka dake tafe:

 1.  Rayuwata a Duniyar Sadarwa – Kashi Na Daya:  Bayani kan asalina a wannan fanni, da yadda na koyi kwamfuta, da abin da ya jefa ni cikin duniyar giza-gizan sadarwa ta Intanet.
 2. Rayuwata  a Duniyar Sadarwa – Kashi Na Biyu:  Bayani kan yadda nayi sabo da fasahar Intanet, da yadda na kware wajen sarrafa kwamfua da dalilan da suka haifar da hakan.
 3. Rayuwata a Duniyar Sadarwa – Kashi Na Uku:  Bayani kan masu bani shawara a fannin, da yadda na taimaka wajen shirin “Google Localization,” tsari na musamman da kamfanin Google ya tanada don kwararru su taimaka masa wajen fassara manhajoji da masarrafansa zuwa harsunan gida a kasashe daban-daban a duniya, ciki har da harshen Hausa.
 4. Rayuwata a Duniyar Sadarwa – Kashi Na Hudu:  Dalilan da suka sa na fara rubuce-rubuce a wannan fanni, da yadda aka yi na fara rubutu a jaridar AMINIYA, da fa’idojin da hakan ya samar, da kalubale da na ta cin karo dasu daga jama’a, da kuma wani bangare na rayuwata a Dandalin Facebook.

Da fatan za a amfana da dan abin da ya samu.


Wasu Shafuka Masu Fa’ida:

- Adv -