Hira da BBC Hausa: Siffofin “Windows 10” da Alakarta da “Windows 8” da “7” (2)

Ga kashi na biyu na hirar da BBC Hausa suka yi dani kan babbar manhajar Windows 10. A sha karatu lafiya.

298

BBC:  Mene ne bambanci tsakanin “Windows 7” da wannan da ake fitarwa a yanzu, kuma wasu abubuwa ne sababbi da suka fito a cikin “Windows 10” da ake kaddamarwa a yau?

Baban Sadik:  Wannan babbar manhaja da ake kaddamarwa a yau tana da dabi’u wadanda suka sha bamban ko suka sa ta sha bamban da sauran manhajoji da kamfanin ya fitar a baya, kusan 13 ko sama da haka.  Amma shahararru daga cikinsu sun hada da: kayatar da tsarin mu’amala da manhajoji mai suna “Start Button” wanda tun daga nau’in Windows na zamunnan baya har zuwa kan “Windows 7” yana nan.  Idan ka shiga fuskar kwamfutarka wato “Desktop” daga bangaren hagu a kasa, akwai wata alama da idan ka matsa, za ka ga dukkan manhajojin dake kwamfutar, a bangare daya kuma ga shafin fuskar kwamfutar kana gani.  Amma a “Windows 8” sun canza wannan tsari; da zarar ka matsa wannan alama sai ta mamaye dukkan shafin fuskar kwamfutar, ba ka iya ganin komai sai manhajojin dake gabanka.  A halin yanzu kamfanin ya sake kayatar da wannan tsari na “Start Button” ya mayar dashi a bangaren hagu, inda yake a baya.  Ka ga wannan siffar “Windows 7” ce.

Akwai kuma abin da ake kira: “Windows Tiles”, wanda tsari ne dake jera abubuwan mu’amala tsibi-tsibi a fuskar kwamfuta, ka gansu rau-rau-rau (gwanin ban sha’awa), wannan kuma siffar “Windows 8” ce.  Shi ma wannan tsari sun dada kayatar da shi a “Windows 10.”

Abu na uku, akwai masarrafar lilo (Browser) na kamfanin Microsoft mai suna: “Internet Explorer,” wacce an dade ana korafi a kanta.  Saboda da dadewa an gano cewa galibin kwayoyin cutar kwamfuta (Computer Virus) dake addabar kwamfutocin mutane masu amfani da manhajar Windows, suna samun kafar shigowa ne ta hanyar wannan manhaja ta “Internet Explorer.”  A halin yanzu ya bayyana cewa kamfanin Microsoft ya daina amfani da wannan manhaja ta “Internet Explorer,” domin ya cire ta daga “Windows 10.”  Ya gina wata sabuwar manhaja mai suna: “Windows Edge” da a halin yanzu, iya gwajin da aka yi tsakanin sauran manhajojin lilo a Intanet dake kasuwa – irin su “Mozilla Firefox” da “Google Chrome” – ya bayyana cewa manhajar “Windows Edge” da kamfanin Microsoft ke fitarwa a “Windows 10” ta fi sauran sauri da kayatarwa.  Ka ga wannan ci gaba ne ga kamfanin Microsoft ta wannan bangare.

Abu na hudu, kamfanin Microsoft ya samar da tsarin neman bayanai a kwamfuta da Intanet ta amfani da murya, a “Windows 10,” wato: “Voice Search.”  A al’adance kamar yadda yake a zamanin baya, babu yadda za ayi ka baiwa kwamfuta umarni ta murya kawai har ta nemo maka bayanai.  Amma a halin yanzu akwai wata masarrafa mai suna: “Cortana,” wacce Microsoft ya fara samarwa a wata wayarsa ta salula mai suna: “Lumia 930.”  “Cortana” masarrafa ce da kamfanin ya samar a wayar salula (wacce idan ka farkar da ita, duk abin da kake yi ko duk wuraren da ka saba zuwa, ko da kasuwanni ne, za ta rika lura dasu, kuma tana taskance bayanai kan abin da ka saba yi a wajen ko taswirar wurin ma gaba daya.  Kuma a duk sadda lokacin zuwanka wannan wuri yayi, sai ta tunantar da kai ta hanyar murya.  Sanan kana iya ba ta umarni ta tunatar dakai yin wasu abubuwa ko ta nemo maka bayanai kai tsaye daga Intanet ko cikin wayar).  A halin yanzu kamfanin Microsoft ya samar da wannan manhaja mai suna: “Cortana” don sawwake neman bayanai ta hanyar murya a cikin “Windows 10.”

Bayan wannan, akwai abin da ake kira: “Facial Recognition” (wanda tsari ne dake iya sheda mutum ta hanyar fuskarsa nan take).  Ma’ana, za ka iya zama a gaban kwamfutarka bayan ka gama kunna ta, kayi amfani da na’urar daukan hoto (Webcam) dake kwamfutar a karon farko don sheda fuskarka.  Daga nan, a duk sadda kwamfutar ke kulle, da zarar ka kalli wannan na’urar daukan hoto na kwamfutar, sai babbar manhajar ta bude maka kwamfutar nan take.  Wanda a baya babu irin wannan tsari.

- Adv -

Ba wannan kadai ba har wa yau, akwai wani tsari da kamfanin ya kira da suna: “Windows Continuum.”  Kafin bayani kan wannan tsari, daga cikin abubuwan da suka kashe wa kamfanin Microsoft kasuwa musamman bayan bayyanar  “Windows 8,” bayan dalilan da na bayyana a baya, (shi ne raja’a da mutane suka yi wajen mu’amala da wayoyin salula da na’ururoin sarrafa bayanai).  Idan ka lura yanzu za ka ga adadin masu amfani da kwamfutoci a duniya ya ragu.  Me yasa?  Hakan ya faru ne saboda samuwar wayoyin salula masu kayatarwa, da na’urorin mu’amala da bayanai – irin su “iPad” da “Samsung Galaxy Tab” misali – wadanda duk abin da za ka iya yi da kwamfuta kana iya yinsa dasu.  Kuma karin amfani da suke dashi shi ne, za ka iya daukansu a jakarka ko ka sanya su a aljihu kayi yawonka dasu.  Wannan na cikin dalilan da suka sa da dama cikin mutane suka daina sayan kwamfutoci.  Da kamfanin Microsoft ya gane wannan, sai ya tsara babbar manhajar “Windows 10” a halin yanzu, ta yadda idan kana da wayar salula ko na’urar mu’amala da bayanai irin su: iPad ko Tab da sauransu, idan ka saukar da babbar manhajar a ciki, to, yadda za ka iya amfani da “Windows 10” a kan kwamfuta haka za ka iya amfani da “Windows 10” a cikin wayar salula.  (An samar da dukkan tsare-tsaren biyu cikin babbar manhajar)…

BBC:  Kenan, dabara ce da kamfanin yayi amfani da ita don a ci gaba da tafiya dashi…

Baban Sadik: …dabara ce don a ci gaba da tafiya dashi, saboda ya kwato kwastomominsa da kamfanin Apple da Samsung da sauran kamfanonin kera wayar salula suka kwace masa.  Domin shugaban kamfanin Microsoft, wato Satya Nadella, ya tabbatar da cewa babbar manufar bullo da “Windows 10” ita ce, game dukkan masu mu’amala da na’urorin sadarwa gaba daya.  Yace ana sa ran mutum biliyan daya za su yi amfani da wannan babbar manhaja ta “Windows 10” a duniya.  To idan muka duba ko muka yi la’akari da dabi’u ko siffofin “Windows 10” sai mu ga cewa lallai akwai alamar haka na iya faruwa.  Domin akwai da yawa cikin wadanda suka saba sukan tsarin kasuwanci na kamfanin Microsoft cikin sharhinsu na hanyoyi da na’urorin sadarwar zamani, a halin yanzu da bayyanar babbar manhajar “Windows 10” duk sharhinsu ya rajja’a ne wajen yabon wannan sabuwar babbar manhaja.  Abin da kuma ke nuna lallai kamfanin Microsoft ya kama hanya kenan.

BBC:  Bayan duk wadannan abubuwa masu kayatarwa da ka bayyana na wannan sabuwar manhaja ta “Windows 10,” sai ga shi kuma kamfanin ya bayyana cewa zai bayar da wannan babbar manhaja ne kyauta.  Me hakan yake nufi?

Baban Sadik:  Daya daga cikin abubuwan dake baiwa mutane mamaki kenan.  Na nuna mana cewa, da dama cikin kamfanonin (da Microsoft ya saba mu’amalar kasuwanci dasu) sun juya masa baya.  Kuma idan bamu mance ba, lokacin da kamfanin ya fitar da babbar manhajar “Windows Vista,” kamfanin HP bai nuna sha’awarsa wajen amfani da wannan babbar manhaja ba.  Wanda kuma kowa ya san kamfanin HP babban kamfani ne.  A lokacin an kiyasta yana da kwamfutoci a kalla sun kai 800 dake ofishinsa na Amurka kadai, amma ya ki amfani da babbar manhajar “Windows Vista,” saboda rashin nagartarta.  Sai yaci gaba da amfani da tsohuwar manhajar “Windows XP” kawai.  Hakan kuwa ke nuna lallai kamfanin Microsoft ya rasa hatta mafi kusancin kamfanonin da ke kawancen kasuwanci dashi kenan.

Da Microsoft ya gano haka, sai ya mayar da wannan babbar manhja ta “Windows 10” ta zama kyauta.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, idan kana da kwamfuta wacce ke dauke da “Windows 7,” ko ince “Windows 7.1,” – wadda ita ce ta gaba-gaba a nau’in “Windows 7.”  Da kuma (masu amfani da) “Windows 8” ko “Windows 8.1,” nan take kyauta za ka iya samun wannan babbar manhaja ta hanyar “Windows Update” (da ke cikin Windows da kake amfani da ita).  Tsarin “Windows Update” cibiya ce da babbar manhajar Windows ke amfani da ita wajen samar wa kwamfuta bayanan karin tagomashi da nagarta, (kai tsaye daga cibiyar manhajoji na kamfanin Microsoft)…

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.