![Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (7)](https://babansadik.com/wp-content/uploads/2023/10/Wayar-Salula-7.jpeg)
Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (7)
Daga cikin ƙananan ayyukan wayar salula akwai jirkita bayanan da wayarka ta ɗauko na bidiyo, zuwa asalin hoton bidiyon kai tsaye. Kamar yadda na’urar Image Processing Unit ko IPU ke yi wajen sarrafa bayanan da waya ke ɗaukawa daga kyamara, zuwa asalin hotunan da wayar ta ɗauka. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 15 ga watan Satumba, 2023.